Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto
Published: 11th, April 2025 GMT
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu.
Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.
A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari.
Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025, kamar yadda rahoton cinikayyar kayayyaki ta Amurka ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa Amurka ta yi gibin dala miliyan 143 a watan Janairu amma ta samu rarar dala miliyan 187 a watan Fabrairu. Wannan ingantaccen canji ya haifar da rarar dala miliyan 44 a kowace shekara.
Bayanai sun nuna cewa kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa Amurka sun habaka sosai a watan Fabrairu, wanda ya kai dala miliyan 474 idan aka kwatanta da dala miliyan 214 da aka fitar a watan Janairu.
A wani labarin kuma, Ministan Kudi na Nijeriya da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce harajin kashi 14 cikin 100 na baya-bayan nan da Amurka ta kakaba kan kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje zai yi wa tattalin arzikin Nijeriya illa.
Edun ya bayyana haka ne a taron kaddamar da harkokin mulki na kamfanoni da ma’aikatar kudi ta kasa ta shirya a Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kayayyaki Nijeriya dala miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.