Ci Gaba Da Bukukuwan Cikan Shekaru 46 Da Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran
Published: 11th, February 2025 GMT
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya
Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.
Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin Musulunci a
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa.
Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe uku na turai wato Faransa da Jamus da kuma Burtaniya, saboda samun fahintar juna da kuma daukewa kasar takunkuman tattalin arzikinn da turawan suka dora mata.