Ambaliyar Ruwa Ta Haifar Da Koma-baya A Fannin Ilimi A Najeriya-UNICEF
Published: 26th, January 2025 GMT
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar.
Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa.
Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Jigawa a shekarar da ta gabata ta lalata gine-ginen makarantu 115, wanda hakan ya kawo cikas ga dalibai.
Ya bayyana alhininsa kan yadda lamarin ya haifar da tsawaita rufe makarantu, wanda ya shafi karatun yara sama da 92,518 a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
“A jihar Jigawa, ambaliyar ruwan da ta afku a shekarar da ta gabata ta lalata gine-gine da kayayyakin makarantu 115, wanda hakan ya sa ba za a iya amfani da su ba.
“Hakan ya haifar da tsawaita rufe makarantu da kuma rashin wadatar ilimi ga dalibai kimanin 92,518, wadanda 43,813 daga cikinsu mata ne, yayin da 48,705 kuma yara maza ne, a fadin kananan hukumomi 27 na jihar,” Mista Farah.
Ya yi nuni da cewa, UNICEF tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin kasashen waje da na kungiyar kasashen renon Ingila da ke Burtaniya, na tallafa wa gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa, don samar da yanayin koyo mai kyau domin rage tasirin sauyin yanayi da ya shafi koyon ilimia makarantu.
Ya bayyana cewa, a shekarar 2024, UNICEF ta dauki nauyin matasa dubu daya, wadanda 350 daga cikinsu sun fito ne daga jihar Jigawa, yayin da 650 kuma suka fito daga Katsina, don dasa bishiyu 300 a yankin hamada da kuma wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa a jihohin biyu, domin dakile tasirin sauyin yanayi.
“Tare da goyon bayan abokan hulda da suka hada da ofishin kula da harkokin kasashen waje, da na kungiyar kasashen renon Ingila da ke Birtaniya, UNICEF na tallafawa jihohin Kano da Jigawa don samar da yanayin koyo mai kyau, don rage tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa”.
Shugaban na UNICEF ya kuma bayyana cewa a shekarar da ta gabata asusun ya gina cibiyoyin kula da tsaftar ruwa da tsaftar muhalli (WASH) a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a wuraren da ake bukata a cikin jihohin uku.
Ya ce asusun ya kuma gina tare da gyara wuraren tsaftar muhalli a makarantu 33, inda aka gina 25 a jihar Kano, sauran 8 kuma a jihar Jigawa, wadanda yara 39,432 ke amfani da su a jihohin biyu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.