Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025
Published: 12th, February 2025 GMT
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa.
Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa.
Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon HadimiCikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba.
Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da zarar an shawo kan matsalar.
Rahotanni, sun nuna cewa yawan wutar lantarki a kan babbar tashar wutar lantarki ta ƙasa (TCN), ya ragu daga megawat 4,064.70 da misalin ƙarfe 11 na safe zuwa megawat 1,222.78 da ƙarfe 12 na rana.
“Muna mai baƙin ciki da sanar da ku cewa wata matsala ta auku a babban layin wuta na ƙasa da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar yau, wanda ya haddasa ɗaukewar wuta a yankunanmu.
“Duk da cewa an fara dawo da wuta a hankali, muna tabbatar muku cewa muna aiki tare da hukumomin da suka dace domin maido da wutar gaba ɗaya da zarar an daidaita layin.
“Muna godiya da fahimtarku da haƙurin da kuke yi yayin da muke ƙoƙarin inganta ayyukanmu a gare ku.”
Babban layin lantarki na Najeriya na fuskantar matsalolin faɗuwa akai-akai, musamman a shekarar da ta gabata, inda hakan ke haddasa matsalolin ɗaukewar wuta a faɗin ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da Najeriya ta fuskanci faɗuwar layin wutar lantarki sau 12 a shekarar 2024.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Layi damuwa Ɗaukewa Najeriya Wutar Lantarki wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.