Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
Published: 10th, March 2025 GMT
Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo.
Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar daular Larabawa, za su halarci atisayen wanda za’a fara a gobe talata daga tashar jiragen ruwa ta chabahar don kallon yadda atisayen zai kasance.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Iran: Gwagwarmaya Ce Kadai Hanyar Warware Matsalar Falasdinu
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya.
Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi ne ci gaba da gwgawarmaya, sannan kuma da samun goyon bayan al’ummar duniya.”
Bayanin ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin na jajiberin ranar Kudus,al’ummar Falasdinu suna cikin mawuyacin yanayi na cin zali da nuna karfi akansu da ‘yan sahayoniya suke yi ta hanya mafi muni, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar dubban Falasdinawa da kuma jikkatar wasu dubu dubatar, daga cikinsu da akwai kananan yara, mata da kuma fararen hula.”
Bayanin sojojin na Iran ya yi kira ga dukkanin ‘yantattun mutane a duniya da su fito domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da ake cin zalinsu, tare da kara da cewa, al’ummar Iran ma’abota juyin juya hali za su fito a ranar Kudus ta duniya domin nuna kin jinin zalinci irin na ‘yan sahayoniya.