2025-08-01@01:16:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 129

«faɗan daba»:

    Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku. Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?” Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu. Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu. Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP. Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar...
    Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu. Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya. Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta. A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse. Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
    Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta. Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta. Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN David Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”. Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro,...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dole ne, ya taimaka wajen haɗa kan ƙasa, kyautata mulki, da bunƙasa tattalin arziƙi. Ya buƙaci a gudanar da wannan aiki cikin adalci, gaskiya da kuma bisa ra’ayoyin jama’a gaba ɗaya. HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Gwamna Abba, ya bayyana haka ne ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sulaiman Wali. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da saƙon maraba da baƙi a wajen Taron Sauraron Ra’ayoyin Jama’a na Yankin Arewa maso Yamma kan sake gyaran kundin tsarin mulki, da aka gudanar a Kano ranar Asabar....
    Kayan da aka gano a wajen samamen sun haɗa da wayoyin salula da dama, kwamfutoci, na’urorin haɗa Intanet da mota ƙirar Honda Accord. Sunayen waɗanda aka kama sun haɗa da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan da Abubakar Abusufyan. Sauran sun haɗa da Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid. EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    A cewar Ringim, idan ana so a sami cigaban da ya shafi kowa da kowa a Arewacin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, to ana buƙatar siyasa irin ta Kwankwaso wadda ke mayar da hankali kan talakawa da gaskiya a mulki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai: “Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“ A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya. Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal. WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere. Sai dai tsohon shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani. “Muna maraba da samar da haɗakar....
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a. An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025. Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis. Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a. An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025. Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis. Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata...
    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban Kasa Bola Tinubu kaɗi ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zabensa a shekarar 2015 ba. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin kaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa kan abubuwan da ya gani a zamanin mulkinsu. Buhari dai ya shugabanci Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023. ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II Daga cikin manyan bakin da suka halarci kaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Yakubu Gowon da tsohon Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar...
    Tashin hankali ya sake kunno kai a Masarautar Kano, inda aka zargi wasu magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da kutsawa cikin fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta Gidan Rumfa da ke Kofar Kudu. Shaidu sun bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne lokacin da tawagar Sarki Aminu ke dawowa daga gaisuwar rasuwar attajirin ɗan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Ɗantata. Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya A wata sanarwa da kakakin masarautar Kano, Sadam Yakasai, ya fitar ya bayyana cewa Sarki Sanusi ba ya cikin fadar lokacin da abin ya faru ba. “Sun fasa kofar shiga fadar, sun kai wa masu gadi hari,...
    ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba. Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zaɓaɓɓun shugabannin gwamnati sukan naɗa wasu muƙarrabai don su taya su sauke nauyin da aka ɗora musu. Wasu na zargin naɗin ba ya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga waɗanda aka naɗa saboda rawar da suka taka yayin yaƙin neman zabe. Shin irin waɗannan nade-naɗe na da wani tasiri ga rayuwar al’umma? NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naɗen masu taimaka wa shugabanni da irin tasirin da suke da shi. Domin sauke shirin, latsa nan
    Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba. Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko matarsa ta zama Babbar Alƙalin Alƙalai ta Ƙasa, hakan ba zai taimaka wa APC ba. Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano Ya ce gwamnatin APC ta gaza, kuma ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa ta hanyar manufofinta marasa kan gado. Dalung ya ce: “Ko duk gwamnonin jihohi 36...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu Yanzu adadin hadiman da ke aiki da Gwamna Abba sun zarce mutum 300. Hadiman sun haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman, Mataimaka na Musamman da kuma Masu Taimaka Masa. Gwamnan ya fara naɗa hadimansa ne a ranar 16...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars. Ya naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar. An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa” Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake gina ƙungiyar kafin tunkarar kakar wasa ta 2025-2026 a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL). A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon ƙafa. Gwamnatin ta rushe tawagar hukumar wasanni ta jihar tare...
    Kusoshin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun shiga haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC da nufin kayar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC. Tsofaffin mukarraban gwamnatin Buhari da suka koma haɗakar ADC sun haɗa da tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da masu muƙaman siyasa. Yawanci sun raba gari da APC ne saboda zargin an yi musu rashin adalci a jam’iyyar da kuma gazawar Gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin da ke ci wa ’yan Najeriya tuwo a ƙwarya. 1- Nasiru El-Rufai Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na gaba ne a tafiyar haɗakar inda tun farko ya lashi takobin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kafin sanar da sabuwar ƙawance da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yi wa wannan haɗaka zagon ƙasa da kawo cikas ga tafiyar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan zagon ƙasa da ake zargin wasu da yi wa wannan sabuwar haɗaka, ita ce na sanar da su rashin samun ɗakin taron da suka shirya gudanar da taron lokaci ƙalilan gabanin taron. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan...
    Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga sabuwar haɗaka da jam’iyyar ADC. Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam’iyyar, shugaban jam’iyyar na ƙasa Ambasada Iliya Damagum ya ce jam’iyyar tana gargaɗi ’yan’yanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC. Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam’iyyunsu. “Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam’iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai...
    Wasu manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun hallara a Cibiyar Yar’Adua da ke Abuja a yau Laraba da rana don taron ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a wani mataki na shiryawa zaɓen shekarar 2027. Taron ya samu halartar manyan fitattun ’yan takara da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasa. Cikin waɗanda suka halarta akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na LP; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Ministan Sufuri kuma gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Haka kuma, Solomon Dalung, Dino Melaye, Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe sun samu halarta. Emeka Ihedioha da Air Marshal Sadique Abubakar (rtd.) suma sun bayyana. David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP. A cikin wata wasiƙar da Aminiya ta gani, David Mark ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda rikice-rikicen shugabanci da aka gaza magancewa. Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos Ya ce waɗannan matsalolin sun kawo wa jam’iyyar naƙaso kuma sun jawo mata abun kunya a idon jama’a. A daren ranar Talata, an naɗa David Mark da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin riƙon kwarya (Shugaba da Sakatare) na wata sabuwar jam’iyyar ADC. Wannan jam’iyya wadda ta haɗa manyan ’yan adawa na da niyyar...
    Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya. An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP. Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar. “Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun...
    Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani? Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen. A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar...
    Na yi shi kamar ‘series’ amma ba ‘series’ bane, ‘part-part’ ne na yi shi haka ba wani me tsayi bane ba, baya wuce minti uku zuwa biyar ya ma yi tsayi kenan. Kai ka ke rubuta ‘comedy’ din ko kuwa bayar wa ka ke a rubuta maka? Ni nake rubuta ‘comedy’ na da kaina, sai dai idan ana hira da abokai ana abun dariya haka da sauransu, sai in dauke shi, shi ma din ko da ban rubuta ba in yi shi akai, mu je mu yi bidiyon shi a duk lokacin da muka samu dama to, gaskiya ba a rubuta mun ‘comedy’ sai dai irin a ba ni ‘idea’ haka. Ko akwai wani ‘comedy’ da ka taba yi wanda...
    A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu. Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.” Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar. Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta. Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana. Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya. Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba ne; ta wuce hakan.” An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina “Matsala ce daga cikin gida… Na ga matsalar tana da alaƙa da girman kai, ba a bar kowa a baya ba.” Da aka tambaye shi ko yana daga cikin masu haddasa matsala a cikin jam’iyyar, ya amsa cewa yana ciki. Gwamna...
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya shirya yin haɗaka da wasu ’yan siyasa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. A wata hira da ya yi da BBC, Amaechi ya ce matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar ne babban dalilin da ya sa ake buƙatar sabuwar haɗaka a siyasa. Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a Mangu Ko da yake bai tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba, sai dai ya ce komai zai bayyana nan da wani lokaci. “Lokaci ne kawai zai nuna,” in ji shi....
    “Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.” Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar. Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar. Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba. “Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba. “Dole ne a daina wannan.” Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai....
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin. Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar. “PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi. “Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna...
    Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin da ya sa ya naɗa Nyesom Wike a matsayin Shugaban Ma’aikata a lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas, maimakon Kwamishinan Kuɗi. Amaechi, ya ce ya zaɓi Wike ne a matsayin Shugaban Ma’aikata domin ya samu damar sanya ido a kansa. Tinubu ya gana da Fubara a Legas Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja “Na so ya zama shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sanha ido a kansa. “Ban ba shi kujerar kwamishinan kuɗi ba,” in ji Amaechi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise da yammacin ranar Talata. Wannan martanin ya biyo bayan kalaman Wike ne, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin...
    Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
    Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba. Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba. Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai “Ko da dukkanin gwamnonin jihohi 36 da Abuja sun koma APC, babu abin da zai canja. “Su da danginsu ba su fi ƙuri’u 1000 ba. Abin da muke so shi ne jama’a,” in ji Lawal a hirarsa da jaridar Nigerian Tribune. Ƙungiyar masu...
      Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa, musamman hanyoyi, karkashin shirin Renewed Hope Action Plan na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne ci gaba da aiwatar da shirin Highway Development and Management Initiative (HDMI), wanda ke amfani da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP). Wannan tsarin ya ba da damar janyo hannun jari...
    Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta soke lasisin gidajen wasannin gala guda takwas bisa karya wasu dokokinta. Idan za a tuna a kwanakin baya hukumar, ta soke lasisin wasu gidajen galar bisa samun su da laifin karya dokar hukumar. Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum Cikin sanarwar da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ya zayyano wuraren da hakan ta shafa da suka haɗa da Hamdala Entertainment, Lady J Entertainment, Ɗan Hausa Entertainment da Ni’ima. Sauran sun haɗa da Babangida Entertainment, Harsashi Entertainment, da kuma Wazobiya. Idan ba a manta ba hukumar a baya-bayan nan ta dakatar da haska wasu...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da naɗin sabbin sakatarorin ƙananan hukumomi guda 21 a faɗin jihar.   Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala ya sanya wa hannu, wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.   Ya bukaci sabbin sakatarorin da aka naɗa da su yi aiki tukuru don ganin nasarar wannan gwamnati da kuma ci gaban jihar gaba ɗaya.   Daga Abdullahi Tukur    
    Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da masu shirya fina-finai sun cimma matsaya bayan dakatar da wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Labarina da Dadin Kowa, Manyan Maga da Garwashi. An bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda daga Litinin 19 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu 2025 domin miƙa fina-finansu don tantancewa da sahalewa. Kwamishina ta nemi a hukunta wanda ake zargi da yi wa ’yar matarsa fyaɗe a Gombe Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma Wannan na zuwa ne bayan wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar da shugabannin masana’antar Kannywood a ranar Litinin. Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ce za a duba fina-finan cikin gaskiya da adalci. Shugaban...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa.  Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025. Dawakin Tofa ya ce Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya fitar da sanarwar dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take. Baya ga haka, gwamnatin...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002. Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin Abuja. Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Ƙungiya mai alaƙa da Alƙa’ida ta yi iƙirarin kashe sojoji 200 a Buarkina Faso Ya bayyana cewa lokacin da Boko Haram ta fara tayar da hankali a Jihar Yobe, Obasanjo ya kira shi domin neman shawararsa. Atiku, ya bayar da shawarar a kira shugabannin tsaro a ba su wa’adin daƙile lamarin, ko su...
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan.   “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya.   “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.”   Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
    Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai hari kan kasuwar ce mai tara ɗaruruwan mutane da ke zuwa daga gari-gari makwabtaka domin baza hajoji iri-iri musamman kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, fulawa, wake, lemuka da sauransu. Shafi’i Sambo, wani shugaban matasa...
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.   Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo.   Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi.   Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake...
    Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal.  Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya. An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Egbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa...
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi. “Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara,...
    Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas. Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar. ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe  An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu A cewar Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, an kame sojojin ne a wani samame da aka yi tsakanin ranakun 26 zuwa 29 ga watan Afrilu a cikin ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali. Ya ce, suna daga cikin waɗanda suke taimakawa ’yan ta’adda huɗu da sojojin suka kama. Kangye ya...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu. Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin Turakin Kano; Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano; da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano. Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarki Sanusi ya buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman da su kasance masu koyi da shugabanni da kuma ci gaba da...
    Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa  matsayin sabon Galadiman Kano. Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano. Wannan sabon...
    Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya. A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa. Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi...
    Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi. A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ke ta ƙaddamar kan sarautar Kano da Aminu Ado Bayero a gaba kotu, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano. Wannan lamari na nuni da cewa rikicin Sarautar Kano ya ɗauki sabon salo, inda kowanne daga cikin ɓangarori biyun ya naɗa nasa Galadiman Kano, inda masu riƙe da sarautun biyu za su gudanar da ayyukansu daban-daban. A cikin wasiƙar da ke ɗauke da wannan sanarwar, wadda Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, babban jami’in gudanarwa na Majalisar Masarautar Kano ya sanya hannu, naɗin Sanusi...
    Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin lamarin ya kai matakin da akwai wuraren da mutane ba sa iya zuwa da daddare saboda tsoron mummunan abin da ke iya samun su. An kashe sojoji 12 a barikin Nijar An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba Wasu na ganin yadda ake gudanar da siyasar jihar da kuma yadda rashin aikin yi su ne ummulahaba’isin wannan matsalar musammam a tsakanin matasa....
    Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma. Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima. Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa. Daga kanmu, magana...
    A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...
    Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cika hannu da wani matashi da aka gani a wani yanayi mai kamanceceniya da baɗala da wata Akuya, lamarin da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta. Matashin, Shamsu Yakubu mai shekaru 24 da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Kano, ya shiga hannu ne bayan ɓullar wani bidiyonsa a dandalan sada zumunta musamman TikTok yana tsotsar farjin wata Akuya. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya A cikin bidiyon da wani yake ɗaukarsa wanda ya yaɗu sosai a soshiyal midiya, an hasko matashin a wannan yanayin mai kama da baɗala tare da Akuyar. Sai dai yayin da yake amsa...
    An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki. Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami. Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna. An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa. Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki. Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa...
    Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.   Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.   Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku.   Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa.   Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin.   Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa...
    Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya Sanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu. Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu. Sunayen kantomomin ƙananan hukumomin Ribas  
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati “A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi. “Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take. “Suna cikin guje...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa. Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Manjo janar Idris (mai ritaya) shi ne...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa. Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi...
    Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
    Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da haƙuri da fahimtar juna domin haɗa kai tare da tabbatar da goyon baya ga jam’iyyar. A nasa ɓangaren, Sakataren APC na Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu da Minista Matawalle bisa wannan tallafi. Ya ce shinkafar ta zo a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar wahalar rayuwa, kuma ya yi alƙawarin cewa ’yan jam’iyyar za su ci gaba da haɗa kai da kaunar juna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantad da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar  Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman Shugaban Kasa sun halarci wannan gajeren bikin rantsuwar da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba. Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers a ranar Talata, 18 ga Maris, domin magance rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar, duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke. A yayin ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa halin rashin tsaro da matsin lamba...
    Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.   WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga fitaccen marubuci kuma masanin adabi, Farfesa Wole Soyinka, cibiya ce mai zaman kanta da ke amfani da binciken ƙwaƙwaf a aikin jarida domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta tsarin shugabanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa. Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa. Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa Seyi ya faɗi hakan ne yayin yi wa wani dandazon matasa jawabi a Yola, babban birnin Jihad Adamawa. Seyi Tinubu wanda ke ci gaba da shawagi a wasu jihohin ƙasar yana buɗa-baki, ya ce a kwanakin wasu sun dage wajen sukar mahaifinsa, sai dai hakan ba zai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba...
    Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.  Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa. “Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za...
    An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar “Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu “Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi. Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale...
    Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar. Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu shida da ke ƙaramar hukumar, inda ya jagoranci ɗaukacin jami’an majalisar ƙaramar hukumar don gudanar da ziyarar. ’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo A dai cikin makon nan ne Shugaban ƙaramar hukumar tare da tawagarsa suka ziyarci fadar Sarkin Kagoma, Mista Paul Zakkah Wyom; Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar.   A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.   A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a ziyarar aiki a ƙasar Sin daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Fabrairun 2025, domin yin haɗin gwiwa a muhimman sassa.   Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd,...
    Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke. Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu. Ya...
    ’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar. Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong. Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi. Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan...
    Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC Aminiya ta ruwaito cewa, Ibrahim Yakubu Adamu wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA. Falgore ya ce nan gaba kaɗan za su aika masa goron gayyata domin tabbatar da buƙatar gwamnan. Kazalika, majalisar ta kuma tabbatar da dokar...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
    Ana sa ran shirin zai inganta samar da abinci, rage rikice-rikicen Makiyaya da Manoma, da kuma samar da damarmaki ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke dogaro da kiwo a matsayin sana’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna. An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar...
    Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram tara, ciki har da ƙwararren mai haɗa wa ƙungiyar bama-bamai, Amirul Bumma a wani samame da suka kai a dajin Sambisa da ke Jihar Borno. Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun kai farmakin ne a Ƙaramar Hukumar Bama, ƙarƙashin rundunar Operation Desert Sanity 4, bayan samun bayanan sirri. Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Boko Haram sun yi ƙoƙarin tsayawa da su fafata, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su. Bayan kammala artabun, mayaƙan sun dawo wajen da gadajen asibiti domin kwashe waɗanda suka jikkata, wanda hakan ke nuna girman asarar da suka yi. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai babban jagoran...
    Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa. Bayan artabun, Boko Haram sun yi yunƙurin kai farmakin ramuwar gayya ta hanyar birne bama-bamai a hanyoyin da sojojin za su bi. Sai dai dakarun sun gano sama da guda 10 daga cikin abubuwan fashewar kuma sun tarwatsa su, wanda hakan ya hana aukuwar asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin. Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi...