‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’
Published: 4th, September 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14 daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.
Cibiyar Gargaɗi Kan Ambaliya (FEWS) ta ma’aikatar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin SambisaSanarwar, wacce Daraktan Kula da Zaizayar Ƙasa da Ambaliya na ma’aikatar ya fitar, ta gargadi dukkan masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye domin kare kansu.
A cewar sanarwar, garuruwan da jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Kuros Riba (Edor, Ikom, Itigidi, Akpap), Kano (Gwarzo, Karaye), Zamfara (Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukuyum), Taraba (Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gembu, Gun Gun Bodel, Kambari, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Bandawa, Ngaruwa), Abia (Eziama, Umuahia) da kuma jihar Yobe (Geidam, Kanama, Potiskum).
Sauran wuraren sun haɗa da jihar Filato (Langtang, Shendam, Wase), Borno (Ngala), Imo (Okigwe, Otoko) Neja (Sarkin Pawa), Sakkwato (Sakkwato, Wamakko, Isa, Shagari, Makira), Kaduna (Kafanchan) da kuma Akwa Ibom (Oron).
Daga nan sai ma’aikatar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati da su kasance cikin shiri.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA