Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci
Published: 14th, August 2025 GMT
Ƙasar Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman da kuɗinsu ya kai Dala miliyan 346, kwatankwacin Naira biliyan 530 don yaƙi da ta’addanci.
Makaman da za a siyar sun haɗa da bama-bamai da na’urorin kakkabo jiragen sama da jirage marasa matuka da sauran su.
NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa TuraiA cewar Kamfanin Sarrafa Makamai na Amurka (DSCA), za a sayar wa Najeriya makaman ne domin tallafa wa shirinta na yaki da ’yan ta’adda da masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Kamfanin ya sanar da cinikin ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Najeriya ta buƙaci sayen bama-bamai guda 1,002, na’urar kakkabo jirage guda 1,002, sai manyan bindigu guda guda 5,000 da sauran makamai.
Kazalika, Amurkar ta amince ta sayar wa Najeriya helikwaftocin kai hari guda 12 da sauran muggan makaman da darajarsu ta kai Dala miliyan 997 a 2022.
Kamfanin ya ce kamfanonin da aka amince wa su yi kwangilar dillancin makaman su ne Lockheed Martin da RTX.N da kuma BAE.
“Wannan cinikin zai taimaka wa bunƙasa hulɗar kasa da kasa da kuma manufofin Amurka a kan harkar tsaro da inganta alaƙa da Najeriya a matsayin babbar ƙawa a yanki Afirka yamma da hamadar Sahara,” in ji sanarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya a sayar wa Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba.
Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a.
Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno Lafiyar Tinubu kalau – SoludoAn yanke wannan hukunci ne bayan majalisar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓar koke-koke na jama’a, wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa, ya jagoranta a zaman ranar Laraba.
Majalisar ta kuma umarci ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar da ta bai wa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar damar riƙon muƙamin shugaban har sai an kammala bincike.
A cewar rahoton, an zargi Yau da haifar da rigima tsakanin shugabannin siyasa da kansiloli, bayar da kayayyakin gwamnati ga magoya bayansa, rabon takardun shiga makarantar Dangote da takin zamani ba tare da adalci ba.
Hakazalika, an zarge shi da sayar da takin gwamnati sama da farashin da aka amince da shi na Naira 20,000 ba tare da sanar da kansiloli ba.
Har ila yau akwai zarge-zarge da suka haɗa da rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen shiga daga kasuwanni da kuɗaɗen harajin dabbobi, sayar da rumfunan kasuwa ba tare da izini ba.
Sauran zarge-zargen sun haɗa da raina dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki, da kuma yin amfani da kuɗaɗen ƙaramar hukuma ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamitin ya zauna da ɓangarorin biyu a ranar 11 ga watan Agusta, inda shugaban ya musanta wasu daga cikin zarge-zargen amma ya amince cewa ya ƙara Naira Naira 2,000 a kan farashin takin zamani da gwamnati ta amince da shi.
Bisa ga sashe na 55 na dokar ƙananan hukumomi ta shekarar 2006, kwamitin ya tabbatar da dakatar da shi domin gudanar da cikakken bincike.
Sannan ta umarci a miƙa dukkanin takardun kuɗi da na gudanarwa na ƙaramar hukumar cikin kwanaki bakwai.
A zaman majalisar na ranar Laraba, wanda kakakin majalisar Ismail Falgore ya jagoranta, majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin.