NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe
Published: 14th, August 2025 GMT
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe.
Hukumar ta kuma ce ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025.
’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin NajeriyaKwamandan Hukumar a jihar, Mallam Maijama’a Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na kafar yada labarai mallakar jihar Gombe (GMC), Ibrahim Isa.
Ya ce an kama mutum 69 maza da mata da suke kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a wasu lokuta.
Muhammad ya kuma ce hukumar na amfani da dabarun rage samarwa da rage bukatar miyagun kwayoyi, tare da kira ga karin hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
Daga nan sai ya gode wa gwamnatin Jihar bisa bayar da motocin aiki guda biyu da gyaran ofishin hukumar, da inganta cibiyar farfado da masu shan miyagun kwayoyi
A nasa jawabin, Daktan kafar yada labaran, Ibrahim Isa, ya tabbatar wa NDLEA da goyon bayan kafar ta GMC, ciki har da bayar da lokacin watsa shirye-shirye kyauta, tare da alkawarin ci gaba da yin aiki tare wajen yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwayoyi Tabar wiwi miyagun kwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.