Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Darakta-Janar Na NTA Da Wasu Daraktoci
Published: 15th, August 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauyen jagoranci a Hukumar Talabijin ta ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro a matsayin sabon Darakta-Janar. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Karimah Bello a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Tallace-Tallace, Stella Din a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Labarai, da Sophia Essahmed a matsayin Manajing Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited.
Pedro, ɗan asalin jihar Lagos, ƙwararren mai ba da shawara ne a harkar kafofin watsa labarai, mai gogewa sama da shekaru 30 a fannoni da suka haɗa da talabijin, haƙƙoƙin watsa wasanni, da dabarun tallace-tallace a Afrika, da Birtaniya da Gabas ta Tsakiya. Kwararre ne a fannin nishaɗi da mallakar fasaha, tare da digirin na biyu a Gudanar da Zuba Jari daga jami’ar City Business School, London.
2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – SoludoA 1995, ya kafa Optima Sports Management International (OSMI), wanda ya shahara wajen yaɗa manyan gasanni kamar Premier League na Ingila, da UEFA Champions League, da Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA, da wasannin CAF zuwa ƙasashe sama da 40. Haka kuma, ya yi aiki a manyan muƙamai a Bloomberg Television Africa, Rapid Blue Format, da kuma matsayin mai ba da shawara ga FIFA, da UEFA, da Fremantle Media, da Ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Afrika (AUB).
Masana sun bayyana Pedro a matsayin wanda ya yi fice wajen samar da kafafen yaɗa labarai masu ƙarfi a kasuwanci, da ƙara samun kuɗin tallafi, da kawo shirye-shirye masu inganci ga masu kallo a Afrika. Wannan naɗin na nuna manufar Gwamnatin Tarayya na sabuntawa da sake gina NTA domin ta yi gogayya a kasuwar watsa labarai ta zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025