Yau ake sake gurfanar da majinyaci ya lakaɗa wa likita duka a asibiti
Published: 19th, August 2025 GMT
A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe.
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai ƙara gaban ’yan sanda kuma tana jiran hukuncin da kotu za ta yanke.
“A yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma ƙungiyar ba za ta ce komai ba har sai ta ji sakamakon hukuncin kotun,” Aji ya jaddada.
Wanda ake zargin, Ahmed Usman mazaunin rukunin gidajen Abba Ibrahim da ke Damaturu an tsare shi a gidan yari na Potiskum har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce, “Mun rigaya mun miƙa ƙarar ga kotu domin ta tantance ranar da za a saurari ƙarar.”
Babbar kotun majistare ta 1 ta tabbatar da cewa an ɗage sauraren ƙarar domin ci gaba da sauraren ta, tare da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari.
Wasu ma’aikatan hukumar kula da asibitocin jihar Yobe da suka buƙaci a sakaya sunansu saboda rashin ikon yin magana a kan lamarin, sun yi qarin haske kan lamarin.
A cewar ma’aikatan, “Majinyacin, Ahmed Usman, ya je asibitin ne tun farko domin duba lafiyarsa tare da likitan da ke bakin aiki. “Lokacin da likitan ya kira sunansa, baya nan, shi ne aka ajiye babban fayil ɗinsa a gefe yayin da majiyyaci na gaba ya je wurin ya bayyana.
”Bayan hakan majiyyacin ya fusata, yana jin an yi watsi da shi. A cikin wani yanayi, marar lafiyan ya fita waje, ya yanko bulala daga bishiya, ya yi amfani da ita don cin zarafin likitan.”
Sun ƙara da cewa, jami’an tsaron asibitin sun shiga tsakani don shawo kan lamarin, kuma an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Kokarin tattaunawa da Dr. Fatima Umar Gamsa ya ci tura, domin tana kwance don jinya daga lamarin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, yana mai cewa: Dukkanin kasashe na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya da kuma hakkin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.
A cikin sakon da ya aike ta dandalin X a yau Talata, Ismail Baqa’i ya yi ishara da shirin Iran a babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ake yi yanzu a Vienna, don ba da shawarar daftarin kudurin da ya haramta kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya. Ya ce: “Iran, tare da China, Nicaragua, Rasha, Venezuela, da Belarus, sun gabatar da wani daftarin kuduri ga babban taron hukumar IAEA kan haramta kai hare-hare da kuma barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliya da ke karkashin hukumar sa-idon ta IAEA bisa tsarin kare martabar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.”
Ya kara da cewa: “Kamar yadda aka bayyana a cikin daftarin kudurin, dukkan kasashe na da ‘yancin yin amfani da makamashin nukiliya domin zaman lafiya da kuma ‘yancin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci