An naɗa Benjamin Hundeyin sabon kakakin ’yan sandan Nijeriya
Published: 5th, September 2025 GMT
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya amince da naɗin CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon Kakakin ’Yan Sanda na Ƙasa (FPRO).
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.
Ɓarkewar cutar Ebola ta kashe mutum 15 a Congo Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar taraKafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasance kakakin rundunar ’yan sanda reshen Jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.
Hundeyin ya yi karatu a fannin Turanci da kuma nazari da halayyar masu laifi da tsaro wato Criminology da Security Psychology.
Haka kuma, memba ne na ƙungiyoyin ƙwararru kamar Nigerian Institute of Public Relations (NIPR) da International Public Relations Association (IPRA).
A shekarar 2020 kuma ya kasance cikin tawagar Najeriya a aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Darfur, Sudan.
Sufeto Janar ɗin ya buƙaci sabon kakakin da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen inganta ayyukan rundunar da kuma ƙarfafa hulɗa a tsakanin ‘yan sanda da al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kayode Egbetokun
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ya yammacin Afirka.
Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna.
Sai dai kuma a cikin sabon tsarin mulkin da za a kada kuri’ar raba gardama akansa babu wannan dokar a cikinsa.
Har ila yau, sabon kundin tsarin mulkin ya zo da sabon tsarin tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa shekaru bakwai,wacce za a iya sabuntawa sau daya. Haka nan kuma a karkashin sabon tsarin mulkin za a kafa majalsiar dattijai,wacce shugaban kasa ne yake da ikon nada kaso 1/3 na mamabobin wannan majalisar.
Da akwai mutane fiye da miliyan 6.7 da za su kada kuri’ar raba gardamar, za kuma a amince da shi, idan rabin wadanda su ka yi zaben su ka amince da shi.
Tun a 2024 ne dai aka tsayar da cewa za a mika wa fararen hula Mulki sai dai kuma sojojin sun saba alkawali. A watan Disamba na wannan shekarar ne aka tsayar za a yi zaben shugaban kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci