Leadership News Hausa:
2025-11-02@00:51:27 GMT

2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC

Published: 31st, July 2025 GMT

2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC

Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku.

Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?”

Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu.

Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP.

Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar tana ƙoƙarin jawo ‘yan siyasa domin dawo da ƙarfinta.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya za su yadda da jam’iyyarsu, Abdullahi ya ce jam’iyyar APC da ke mulki ta yi alƙawarin kawo sauyi amma ta gaza.

Don haka, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su gwada wata sabuwar tafiyar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Haɗaka

এছাড়াও পড়ুন:

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

“Ba za mu ci gaba da ɓata kuɗi a kan abubuwan banza ba, kamar yawan ministoci, sayen motocin gwamnati, da ma’aikatan da ke yi wa shugabanni hidima.

“Idan muna samun ƙarin kuɗi amma muna kashe su ba daidai ba, to duk ci gaban da muka samu ba zai yi tasiri ba,” in ji shi.

Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce matsalolin tattalin arziƙin Nijeriya sun samo asali ne shekaru da dama.

Ya shawarci shugabanni su riƙa sauraron masu faɗa musu gaskiya maimakon waɗanda ke yabonsu kawai.

Ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa da an cire tallafin man fetur tun wuri da ha rage wahalar da ake ciki yanzu, amma gwamnatocin baya sun kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025 Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II
  • Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II
  • Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa