Shugaban wanda ya samu wakilcin Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, Shugaban kasar ya ce tuni gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da al’ummar Ogoni domin magance duk wata matsala da za ta iya kawo cikas ga tashar domin fara samar da ɗanyen mai.

ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiKwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE

Daga Usman Muhammad Zaria 

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin.

Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.

Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.

 

A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.

Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina