Hukuma ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da N4bn a Kano
Published: 5th, October 2025 GMT
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta fara binciken Tsohon Gwamnna Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu zuwa aikin Dala Inland Dry Port.
Ana zargin kuɗin an kashe su wajen bayar da kwangila don samar da wasu abubuwan more rayuwa a wajen aikin.
An gano yadda aka mayar da kashi 20 na kuɗin wanda mallakar jihar ne zuwa ga iyalan Ganduje a shekarar 2020.
Wannan ya janyo an cire Jihar Kano daga cikin masu mamallaka kamfanin, inda ’ya’yan Ganduje ke riƙe da muƙamakn daraktoci da wasu masu hannun jari.
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa binciken ya fara ne bayan hukumar ta samu koke-koke daga jama’a kan zargin karkatar da kuɗin.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban hukumar PCACC, Saidu Yahya, ya ce binciken zargin karkatar da kuɗin jihar ya kusa kammalawa.
“Eh, mun samu koke-koke daga jama’a kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu na kuɗin Jihar Kano zuwa Dala Inland Dry Port da tsohuwar gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi,” in ji Yahya.
“Zuwa yanzu mun gayyaci wasu da ake zargi da hannu a lamarin. An kama mutum ɗaya, an yi masa tambayoyi, daga baya kuma aka sallame bisa beli bayan ya bayar da muhimman bayanai.
“Bincike ya kuma gano cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi yanzu yana Yola, a Jihar Adamawa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za a kai lamarin zuwa kotu nan ba da jimawa ba, domin binciken ya tabbatar da cewa akwai isassun hujojji don ci gaba da shari’a.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dala Inland Dry Port Karkatar Da Kuɗi zargi kan zargin karkatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.
Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.
Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a BornoA wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.
Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.
Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.
Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.