Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 142
Published: 4th, October 2025 GMT
142-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
/////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata , a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatima (s) da muke kawo maku a cikin shirin da ya gabata, munyi maganar yadda Khawarijiwa suka ki shigan birnin Kufa tare da Amirul muminina (a), inda suka taro a wani wuri da ake kira harauria, suka kirkiro wata akida ta kafirta musulmi, musamman Imam Ali (a), suka fara zama matsalar tsaro a inda suke, a lokacinda labara ya zo masa sai ya aiki Abdulladi dan Abbas zuwa wajensi, tare da umrnin kada ya shiga jayayya da su a cikin alkur’ani mai girma.
Amma alokacinda Abdullahi dan Abbas ya isa wajensu sai ya cewa, dole sai ya shiga jayayya da su.
Suka kawo batun hukunta mutane , sai ya ce masu akwai inda All… ya umurci mata da mijinta su yi sulhu ba, ta yaya zasu hana al-ummar Muhammad (a) yin sulhu? Sun yi ta jayayya da shi kan akidunsu, kafin Imam Ali (a) ya karaso wurin ya kuma gana da su.
Da farko bayan isowarsa, ya yi alwala sannan yayi raka’o’ii 2, sannan ya je wajensu, ya sami dan Abbas yana jayeyya da su. Sai ya hana shi. Sannan ya juya wajen Khawarijawan, ya tambayesu waye shugabansu sai suka fada, sai ya ce, mene kuke aibawa a cikin al-amarimmu sai suka ce batun, hukuntar da mutane a Siffin, sai yace masa. Ina hadaku da All..shin ban fada maku ba a lokacinda suka daga Alkur’ani kan cewa wadan nan mutane ba matanen addinin bane, ba kuma mutanen Alkur’ani bane, na fiku saninsu tun suna yara har suka girma, sun kasance mafi sharrin yara sannan mafi sharrinin manyan mutane. Kuma sun daga alkur’ani don yaudara ne, don kaidi a gareku. Amma sai kuka ki ra’ayina kuka ce zaku karbi littafi daga garesu, sai na ce maku ku tuna da zancena da kuma kin ra’ayi da kuka yi. Sannan na ce mako na amince da sharaddan su yi hukunci da Al-kur’ani mai girma.
Sai wani daga cikinsu yace, dai dai ne hukuntar da mutane kan jinane? Sai Imam (a) yace: ai ba mutanene muka hukuntar ba, Alkur’ani ne muka hukuntar, tunda shi ai rubutu ne, wanda aka zana a cikin al-kur’ani baya magana, mazaje ne zasu karanta abinda yake cikinsa. ..
Daga karshe a lokacinda ya ga suna fahintar maganarsa, sai y ace to su shiga gari tare da mu.
Sai suka yi biyayya suka shiga birnin Kufa tare da amirulmuminina (a). tare da wadanda suke tare da shi.
Kamar magana ta mutu amma ashe suna yada akidunsu a cikin gari suna tada hankalin mutane, harma a kwai wani lokacinda wani daga cikinsu ya kaste maganarsa a cikin khuduba tare da karanta wata ayar alkur’ani.
Ana cikin wannan halin ne sai maganan hukunci ya tashi, sai Imam(S) ya aiki mutanen 400 zuwa Daumata jandal ko Azuraa, daga cikin har da shi AbuMusa Al-Ashari, ko kuma Abdullahi da Kais, da kuma dan Abbas a matayin mai bada sallah.
A lokacinda mahukuntan suka hadu a daumata jandal, wato amru dan Asi da kuma Abumusa Al-ashari, Mu’awiya ya tattauna da Amru ya kuma fada masa halayen Abu musa da rauninsa.
Don haka bayan haduwarsu, sai ya barshi kwanaki uku, ya kuma kebe masa wuri yana bashi abinci mai dadi, da abinsha mai zaki, bai fara wata magana da shi ba sai lokacinda ya kosar da shi.
Sannan ya fara magana da shi yana girmama shi, yana fada masa kan cewa Abu Musa kai babba ne daga cikin sahabban manzon All..(s), kai babban mutumne mai yuwa saboda albarkacinda All..ya hada kan wannnan al-ummar. Yana lallashinsa .
Har ya sami kansa sai ya fara fada masa yadda zai, yace masa da farko kai ka fara tube Aliyu dan Abilib daga khalifanaci, sai ni kuma na tube mu’awiya dan Abusufyan, sai mu zabawwa wannan al-ummar mutum wanda bait aba shigo cikin wannam fitinan ba. Babu jinin wani a kansa.
Sai Amru ya fahinci cewa Abu musa ya larkata zuwa Abdullahi dan Umar, sai yayi sauri ya gabatar da sunansa ga Abu Musa.
Ya ce masa ba wanda ya dace da hakan kamar kamar dan Umar. Sai Abu musa yayi farin ciki , yana tsamman Amru zai yarda ya gabatar da shi bayan sun tube Imam Ali da kuma Mu’awiya.
Sai yacewa Amr ta yay azan sami alkawali cewa zaka gabatar da shi bayan mun tube wadannan biyu.
Sai Amru dan Asi ya ce masa, zan yi maka rantsuwa sai ka yarda kan cewa, zan cika alwalin da na dauka sai ka yarda. Sai fara matsa rantsuwa da All.. da duk abinda ya san Abu musa zai yarda.
A lokacinda Abu Musa yaga cewa ya yi rantsuwa wand aba wata rantsuwar da ta rage kan cewa zai ciki al-kawari, sai ya yarda ya amince haka za’a yi.
Abu musa bait aba tunanin Amru dan Asi zai saba masa tare da yawan ransuwar da yayi ba. Har sai yana ganin kawai haka ya awku ne.
Daga nan sai labara ya yadu cikin wadanda suka halarci hukuncin kan cewa sun yi ittafaki kan abu guda nan gaba kadan zasu bayyana lokacin bayyana hukuncin.
A lokacinda aka taru sai Amru dan Asi ya cewa Abu Musa bismilla ka ci gaba ya bayyana abinda muka cimma a cikin tattaunawarmu. Abu Abu musa yaki, sai yayi ta tara masa, kasa, yana cewa babban sahabbai kuma , ai ba yadda za’a yi a gabace ka. A lokacinda tawagar Imam Ali (a) ta ga haka sai, Ibn Abbas ya zo ya fadawa Abu Musa zai yaudare k aka fadi wani Abu shi kuma ya saba maka.
Amma amru y adage, sai shi ya fara hawa mimbari. Daga karshe Abu musa yah au, ya fara da sunan All..
Sai ya ce ya mutane, lalle mu munga cewa abinda y dace ga al-umma, zai tabbatar da amince da zaman lafiya a cikinta, shi ne mu tube Aliyu da Mu’awiya, don haka ni na tube Ali kamar yadda na tube rawanina, sai ya kama rawaninsa ya tube a gaban jama’a , sannan mun sanya Ubdullahi dan Umar Khalifa, shi sahabi ne kuma babansa ma babban sahabin manzon All..(s).
Abu musa ya tube Imam Ali (a) ya san cewa shi nafsu mandon All…(s), sannan matattaran ilminsa ne, kuma wazirinsa ne kamar yadda Haruna ya kasance ga musa. Da wasu falaloli da dama, Abu musa ya san wadannan gaba daya amma ya amince ya tube shi.
Amma mu je gaba, daga nan sai Amru dan Asi ya haw kan mimbari ya bude maganarsa da sunan All..yayi salati ga manzon All.. (s).
Sai ya ce: Yak u mutane Lalle Abu Musa Abdullahi dan Kais ya tube Aliyu (a) kamar yadda kuka ji ya fitar da shi daga wannan al-amarin, kuma shi yafi saninsa, Don haka ku saurara nima na ciri Aliyu tare da shi, sannan na tabbatar da Mu’wiya a kaina a kuma kanku.
Kuma Abu musa ya rubuta a cikin sahifansa, lalle an kashe Uthman a matsayin wanda aka zalunta. Kuma shahiudi, Da kuma kan cewa waliyinsa yana iya neman jininsa a ko ina yake. Kuma mu’awiya sahabin manzon All..(a) ne hakama babansa.
Sai ya shiga yabon Mu’awiya yana cewa shi khalifa ne a kaina a kuma kanku. Dole ne mu yi da’a gareshi mu yi biyayya. Kan neman jinin Uthman.
Sai Abu musa ya tashi yana cewa, me ya sameka, All..ya la’neka. Kai ba kome ba sai kamar kare. Sai Amru y ace masa kai kuma kananan kamar jaki dauke da littafai.
Don haka da haka aka kammala taron Daumata Jandal, inda mahukuntan sun yi hukunci da ra’ayinsu. Basu yi hukunci da Alkur’ani ba, a gaba dayan tattaunawa da suka yi, ba wani daga cikinsu da ya kawo matsayin wadannan mutanen biyu, wato Imam Ali da kuma mu’awiya a cikin addinin musulunci ba. Ko kuma wanda ayoyin al-kur;ani suka sauka suna yabonsa.
Sannan a tattaunawarsu gaba daya basu kawo batun way a kashe uthman ba, tunda ai don kisansane aka yi yakin siffin. Don haka sun sabawa sharuddan da Imam Ali (a). ya shimfida masu.
Sannan daga karshe, kaga cewa, khawarijawa sun yiwa Imam Ali (a) da sauran musulmi asara, a yakin siffin sun yaudaru da daga mushafi, don da sun saurari Imam Ali (a) da an gama da mu’awiya ko kuma an kwace sham daga hannunsa. Amma wannan saba masa da suka yi, ya sa an bawa munafukai dama har ya kaiga sun shimfida iko a kan musulmi sun kama yada fasada da tsoro cikin mutane.
To barna kan, an rika an yi shi, kuma wannan ba kome ya jawo haka ba, sai sabawa umurnin Imam Ali (a), da kuma bin son zuciya.
Yaya Abu musa Alashari, ko abdullahi dan kai zaiyi da All..a ranar kiyama, All..a daga hujjansa a bayan kasa bayan manzon All..(s) amma ya zo ya cire shi. Me zai fadawa All..a ranar kiya ya ki bayyana matsayin Imam Ali a cikin sahabban manzon All..(s) a lokacinda shi kadai zai yi haka.
Ba abinda zamu ce sai inna lillah wa inna ilaihi raji’un.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 141 October 4, 2025 Araqchi Ya Ce: Bai Kamata Dokar Kasa Da Kasa Ta Zama Abin Wasa A Hannun Amurka Ba October 4, 2025 Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza October 4, 2025 Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza October 4, 2025 Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72 October 4, 2025 Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Iran ta bukaci duniya ta bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Duniya na yabawa Hamas kan amincewa da daftarin Trump October 4, 2025 Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: masu sauraro Abu Musa Ya Abu musa ya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA