Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 145
Published: 4th, October 2025 GMT
145-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda ya ke kawo maku kissoshin da suka zo cikin Alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan, wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahida muttahari, kuma kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddin Rumi.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirarar ImamAl-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatimah (a) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun yimaganar yakin Nahrawan, inda Imam Amirulmumina(a) ya yaki khawarijawa, wadanda su ne suka bata masa nasaran da yake kusan samu kan rundunar sham,rundunar Mu’awiya dan Abu Sufyan bayanda da suka daga mushafin Alkur’ani wai suna bukatar a alkur’ani ya shiga tsakaninsu. Sun yi haka ne a lokacinda sun ga cewa an kusan samun nasara a kansu.
Imam Ali (a) ya fada masu cewa makircine aka yi maku, ko koma ko karasa nasarar da muka samu, sai suka ki, banda haka suka bayyana tawaye suka yi barazanar kashe shi kamar yadda suka kashe Uthman.
Sannan sun ki amincewa da wadanda ya gabatar masu, a matsayin wakilinsa a alkalancin da za’a yi a Daumata jandal, wato Abdullahi dan Abbas da kuma Malikul Ashtar.
Sannan suka tilasta masa amincewa da Abu Musa Al-ashari a matsayin wakilinsa a alkalancin da aka yi daga baya. Sun san cewa Abu musa makiyinsa ne, shi gwamnansa ne a kufa wanda ya yi masa, tawaye ya kuma tube shi.
Bayan haka alkalan suke bi son zuciyarsu a alkalanci, suka tube Imam Ali (a) kamar yadda yake tsammanin zai faru. Sannan basu bai ishesu ba sai da saka samar da wata akida suna kafirata musulmi daga cikin har da shi amirulmuminina (a), da farko sun ki shiga kufa tare da amirul muminina (a), sai da ya je da kansa ya yi jayayya da su a cikin yan mintoci ya kure su, sannan suka amince suka shiga kufa.
Amma tunda basa da gaskiya, sun kuma tara jahilai suna yaudararsu, suna ingiza mabiyansu kin amirulmuminina, da sauran muminai.
Sannan daga karshe suka tara mutane 12 a Nehrawan suka kashe mutane ba tare da wani dalili ba.
Kuma da alamun suna da wasu wadanda suke aikiwa mu’awiya a cikinsu. Don duk abinda suke yi a cikin musulmi wanda yake karfafa Mu’awiya ne ya kuma, mai sauran musulmi baya. Sun kashe Abdullahi dan Habbabul Art sahabin manzon All..(s) da kuma matansa dauke da tsohuwar ciki ba tare da dalili ba.
Sun kashe wasu matan uku su ma ba tare dawani dalili ba. Anan ne Amirul muminina(a) ya ga cewa sun fi mu’awiya hatsari, sai ya karkatar da rundunarsa ta yakar mu’awiya zuwa Nahrawan ya yi magana mai kyau da su, ya tunatar da su kurakuransu tun siffin har zuwa Nehran.
Amma don da al-amarinsu babu hankali acikinsa, sai yaki da mutuwa kawai suke magana, babu magana ta masu hankali daimani . Sai suka farwa rundunar Imam Ali (a) a Nahrawan suka kashe su gaba daya indabanda mutane 9.
Asali su dubu 12,000 a lokacinda Imam Ali (a) ya yi masu magana mutum 8000 daga cikinsu suka tuba suka dawo cikin rundunar Imam Ali(a). Amma 4000 suka dake kan bata, da kuma jahilci. Sune aka kashe gaba daya sai mutum 9.
Sannan mun bayyanacewa manzon All..(s) yayi maganar bayyanar Khawarijawa kafin bayyanarsu, da kuma wasu daga cikin sahabbansa da zasu kasance cikinsu.
Bayan yakin Nahrawan sun ya raba makamansu a cikin mayakansa da kuma dawakansu. Sannan sauran dukiyoyinsu wadanda suka hada da bayinsu ya barwa magadansu.
Daga nan sai tawayen da sojojin Imam (a) suka yi, don kafin yakin Nehrawan anniyarsa ita ce komawa sham don yakar Mu’awiya dan Abu sufyan .
Amma bayan yakin Nahrawan, sai gajiya ta bayyana a fili ga sojojin, saboda yake-yaken da suka yi a siffin yasa na kashe da dama daga cikinsu. Sojojin sun zama basa son yaki kuma.
To amma yaya Imam(a) zai yi ga Mu’awiya yana kara karfi, idan kuma ya dakatar da yaki to kuma mu’awiya zai zo ya mamaye ko ina har da kufa idan sun ki fita.
Daga karshe ya samu labarin wasu sojojin nasa sun gudu daga inda suke a Nahrawan zuwa kauyuka na kusa don kada a tafi da su Siffin.
Daga karshe Ash’as dan Kai Alkindi ya fito fili ya fadawa Amirul muminina(a) , yana cewa:
(Ya shugaban mumuminai, korimmu sun kare, takubbammu sun rasa kaifinsu, haka ma kawukan masummu dun lalace, ka koma da mu zuwa mazaunimmu, don mu sake tanadi mai kyau, mai yuwa kuma shugaban muminai ya kara yawammu, ya maye gurbin wadanda suka mutu daga cikimmu wannan zai fi dacewa da mu, ….) bayan maganar wannan mutum makiri, sai wasu daga cikin sojojin Imam suka sulale suka fice daga rundunar a cikin dare suka je suka boye a cikin kauyukan da suke kewaye da inda suka.
Daga nan Imam (a) ya tabbatar da cewa sun fice daga ikonsa ba kuma abinda zai iya yi, don haka ya ga ba makawa sai ya koma Kufa, sai kawai ya jagoranci sauran suka koma Kufa.
Kuma tun daga lokacin Imam Ali (a) ya kasa samun kan sojojinsa don yakar Mu’awiya dan Abu Sufyan. Yayi kiransu a khudubobinsa a masallacin kufa, yayi kiransu a bayyana a kebe a boye a bayyana ba wanda ya amsa masa sai wadanda ba za’a rasa ba, wadanda ba zai iya fita yaki da su kadai ba.
Sannan babban dalilin da ya sa Imam(a) bai da wadanda zasu amsa kiransa na fitan yaki , shi ne ya rasa mafi yawan sahabbansa masu Ikhlasi, wadanda suka san matsayinsa, kuma basa saba masa a cikin umurninsa a yake-yaken Jamal da Siffin da kuma Nahrawan.
Manyan-manyan sahabban manzon All..(s) wadanda da su ne Musulunci ya kafu a zamanin manzon All..(s), cikin muhajiru da Ansar, wadanda suka yi shahada a wadan nan yake-yake guda uku, da suna nan da sojojinsa ba zasu saba masa ba.
Imam(a) yayi bakin cikin rabuwa da su, ya yi kukan rashin a wurare da dama, yakan bayyana haka.
Daga ciki wata rana ya haw kan mimbari yana khuduba sai ya ambacesu yana cewa:
{Me ya cutar da yan’uwammu wadanda aka zubar dajininsu a Siffin, duk da cewa basa raye a yanzu, ? sun yi hakuri ne da ci da shan gurbatacce, Hakika sun riski All..ya cika masu ladansu, ya kuma sanyasu a gidan aminci, bayan tsoro a duniya, ina yan uwana wadanda suka kama hanya, kuma suka wuce a kan gaskiya,? Ina Ammar? Ina dan Attayyihan? Ina Zuzshahadatain, ? ina masu kama da su daga cikin yan’uwansu, wadanda suka kulla alkawali kan kan mutuwa kan tafarkin All..aka yanka kawukansu aka bawa fajirai!}.
Sannan yasanya hannayensa a kan goshinsa yana kuka.
Imam Ali (a) ya yi bakin ciki sosai a kan rashin wadan nan sahabbansa, sahabban manzon All..(s) wadanda suka kasance masan Al-kur’ani mai girma wadanda kuma suka aikata abinda ke cikinsa.
Suna biyayya gareshi ba sa saba masa kamar yadda suna sani a addinin musulunci. Wadannan sahabbansa da ya ambata, suna daga cikin wadanda suka gabatar da rayukansu a wadannan yake-yake don daukaka gaskiya a kan karya. Kamar yadda kuka sani an kashe dukkan mutane a yakin jamal da yakin siffin amma a Nahrawan mutun 9 kacal aka kashe. A jamal da siffin an kashe dubban musulmi a bangarorin biyu. Malaman tarihi sun yi ta sabani kan adadin mayakan Imam Ali (a) a yake-yaken Jamal da Siffin da kuma Nahrawan. Amma an kashe dubban musulmi a yakokin biyu. Da wuya ka sami gidan da bai rasa kowa nasa ba.
Daga cikin wadanda Imam ya amtaba a cikin wadanda suka yi shahada akwai Ammar dan yasir wanda yake dan shekara kimani 90 a duniya a lokacinda ya je yakin Siffin. Ya musulta tun farkon bayyanar addinin musulunci a Makka. Ya halarci dukkan yakoki tare da manzon All..(s). Sannan manzon All..(s) ya ce: Azzalumar runduna ce zata kashe Ammar zai gashi an kashe shi a hannun sojojin Mu’awiya, wanda ya tabbatar da gaskiyar Imam Ali (a).
Ga Zuzshahadataini, sunansa Khuzaima dan Thabit Al-ansari, shi ma yahalarci dukkan yake-yaken farkon musulunci tare damanzon All..(s) shi ma ankashe shi a siffin. An ce da ya ga ankashe Ammar dan yasir A yakin Siffin, sai ya ce na ji manzon All..(s) yana cewa, azzaluman rundunace zata kashe Ammar, sai ya zare takubinsa, ya shiga yaki bai fita ba har aka kashe shi.
Don haka Imam Ali (a) ya rasa masoya da dama a yake-yaken Jamal da Siffin, wadanda da suna nan daransu dabai fada cikin rashin biyayya da kuma rashin da’an da mutanen Kufa suna nusa masabayan yakin Nahrawan ba.
Masu sauraro a nan zamu dasaaya sai kumawata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wabarakatuhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar ImamHassan(a) 143 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 142 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 141 October 4, 2025 Araqchi Ya Ce: Bai Kamata Dokar Kasa Da Kasa Ta Zama Abin Wasa A Hannun Amurka Ba October 4, 2025 Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza October 4, 2025 Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza October 4, 2025 Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72 October 4, 2025 Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Iran ta bukaci duniya ta bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yakin Nahrawan a yake yaken masu sauraro wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.