Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Hassan (a) 141
Published: 4th, October 2025 GMT
141- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
/////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata , a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatima (s) da muke kawo maku a cikin shirin da ya gabata, munyi maganar yadda Aka ayyana Abu Musa Al-Ashari a matsayin wanda zai wakilci Imam Ali (a) a wajen hukunci duk da cewa ya fada masu kuma sun san cewa zasu, shi ba amintacce ne a wajenshi ba.
Daga nan kun san akwai wani abu a kasa kuma kusan juyin mulki suka yi masa. Sai ya barsu suka yi aminda suka ga dama. Daga karshe sun rubuta wata takarda inda suka tabbatar da sulhu da kuma hukuncin da bangarorin biyu, amma abin mamaki shi ne dukkansu makiyan Aliyu dan Abitalib (a) ne suke hukunci. .
Sannan munyi maganar Harauriyya da kuma sabon akida da sunan addinin musulunci da suka kirkiro a cikinsa. Khawarijawa, wadanda suke. Yi barazana ga Imam Alim (a) a Siffin suka hana shi nasarar da ya samu a yakin, su ne , wadanda yawansu ya kai 12000 su suka kirkiro wannan akidar, a Harauriyya kamar yadda muka bayyana sannsan suka sanya shi’arinsu (Hukunci ta All..Ce). Kalmar gaskiya amma suna nufin bata da ita, kamar yadda Amirulmuminina (a) yake fada.
Don haka alokacinda Imam Ali (a) ya shiga Kufa wadannan yan tawayen kuma khawarijawa sun ki su sha gari, sun tsaya a harauriya inda suke yada akidarsu, ta kin Aliyu dan Abu talib (a), da kuma karkata karkata daga addinin musulunci.
Sannan mun bayyana cewa manzon All..(s) ya fadi hadisai da dama dangane da bullowarsu, da kuma sifofinsu. Daga ciki mun kawo hadisi guda inda yake fada (s) kan cewa zasu karanta alkur’ani amma ba zai wuce makokoronsu ba. .
A wani hadisin wanda Abu sa’id Alkhuduri ya ruwaito, y ace, wata rana an kawowa manzon All..(s) dukiya , sannan ya fara rarraba ta ta dama da hagu, tsakanin sahabbansa (s), sai daga cikin wadanda yake basu, akwai wani mutum sanye da kayan da aka yayyake kasrsa. Yana da wata alama ta yawan sujuda a tsakanin idanunsa, sai dukiyar ta kare, bai samu ba. ! sai ya juya yana tafiya yana cewa, ‘wallahi baka yi adalci ba a yau. Sai manzon All..(s) ya fara jujjuya hannunsa yana cewa.
{Idan ban yi adalci ba wa zai yi,? Amma da sannu wasu masu ficewa daga addini zasu fice kamar yadda kore yake ficewa daga bakaa, kuma ba zasu koma cikinsa ba sai idan bakin zai koma inda ya fito, zasu karanta Alkur’ani amma ba zai wuce makokoronsu ba, suna kyautata zance, amma suna munana aiki, to wanda ya riskesu ya yakesu, wanda ya kashesu yana da lada mafi kyau, wanda suka kasheshi yana da shahada mafi daukaka, All.. ya barranta daga garesu, bangaren da ya fi gaskiya daga rundunoni biyu ne zasu kashe su }
Kamar yadda ya zo cikin mustadrak Hakim JZ 2 SH 154.
Bangarorin biyu sun fidda hadisai da dama daga manzon All…(s) dangane da su. Dangane da fitarsu daga addinin musulunci, amma suna kiran kansu musulmi, kuma wannan yana daga cikin mujizozjin manzon All..(s) saboda fadar gaibun da yayi kuma ya tabbata a bayansa.
Sai wani mai shela daga cikinsu ya bayyana cewa, shugaban yaki shi ne, Shibs dan Rib’ii Attamimi, mai bata sallah Abdullahi dan al-kawwaamAl-Yashkari, kuma al’amura shoorah idan sun sami fatahi. Kuma bai’a ga All..ne mai girma da daukaka..
A lokacinda al-amarinsu ya bayyana, sai Imam Ali (a) ya aiki Ibn Abba zuwa wajensu, amma tare da umurnin kada ya shiga jayayya da su sai ya karaso. A lokacinda Abdullahi dan Abas ya hadu da su, sai ya ga cewa ba makawa sai ya shiga bincike da jayayya da su. Sai ya ce masu: Me kuke suka a cikin mahukunta biyu? Ga shi All..mai girma da daukaka yana cewa, : {Idan suna sun sulhu All..zai yi masu muwafaka kan hakan}(Annisa .Aya 35) macce da mijinta, kenan, ! me zai hana al-ummar Muhammad (s) yin sulhu?.
Sai wani daga cikinsu ya bashi amsa da cewa: Amma abinda All..ya sanya hukuncin a fili ga mutane, sanna ya umurcesu da su yi ijtihadi a cikinsa da gyara. Sai su yi hakan mkamar yadda yace, amma abinda ya sanya hukuncinsa kuma ya zartar da shi, ba zai yu bayi su yi ijtihadi a cikinsa ba, hukuncin zina bulala 100, hukuncin sata yanke hannu. Bayi basa da hakkin kawo ijtihadinsu a cikinsa.
Sai Ibn Abbas yace: All..na cewa: {Masu adalci biyu daga cikinku su yi hukunci} Ma’ida 95. … ya ci gaba da jayayya da su har zuwa lokacinda Amirulmumina (a) ya shigo wurin tare da tawagarsa zuwa wurin, a lokacinda ya iso sai ya shiga heman Yazid Dan Kais, sai ya shiga wurin ya yi alwala ya yi raka’o’I biyu sai ya fita zuwa wajensu.
Sai ya sami dan Abbas yana jayayya da su, sai ya ce masa: ka yi hankali ban ce maka kada kayi jayayya da su ba, All…ya jikanka?
Sai ya juya kan khawarijawan ya ce masau, waye shugabanku? Sai suka ce Ibanul Kawwaa.
Sai ya juya wajensa ya ce masa: Me ya fitar da ku cikimmu kuna aibatamu? Sai suka ce: Hukuncinku a ranar Siffin.
Sai yace:
{Ina hada ku da All.. shin a lokacinda suka daga alkur’anai sai kuka ce: Mu amsa kiransu zuwa ga littafin Alll..sai na ce maku, ni na san mutanen nan fiye da ku, su ba ma’abuta addini ba, kuma ba ma’abuta Alkur’ani ba, ni na kasance tare da su,, kuma na sansu suna yara da kuma bayan sun girma ba? Sun kasashen mafi sharrin yara mafi sharrin mazaje ba?, don haka ku ci gaba da hakkinku, da kuma gaskiyansu, abin sani kawai sun daga alkur’ani ne don yaudararku, da kuma raunanaku da kuma kaidi gareku, ammam sai kuma ki karban ra’a yin a, kuka ce: aa’a sai dai zaku karba daga wajensu: Sai nace maku, ku tuna da wannan zance na da kuma sabamani da kuka yi, a lokacinda kuka ki, sai littafin da suka daga, sai na shardanta maku kan cewa, su raya abinda Al-kur’ani ya raya su kuma kashe abinda Alkur’ani ya kashe, idan sun yi hukunci da abinda ya zo cikin ALkur’ani, ba zai yu mu sabawa hukuncin wanda ya yi hukunci da Al-kur’ani ba, Idan sun ki, mun barranta daga hukuncinsu}.
Sai suka yi shiru, don amsa dukkan abinda yake riya cewa ya rikice maku. Duk tare da cewa basu bayyana masa hakikanin akidunsu ba. Sai wani daga cikinsu ya tambaye shi kan ncewa: Shin kana ganin Adalci ne mutane su yi hukunci kan abinda ya shafi zubar da jini? .
Sai ya Amsa da cewa {Bamu sanya mutane matane a matsayin masu hukunci ba, sai dai Alkur’ani muka sanya mai hukunci, wannan Alkur’ani rubutu ne, a cikin littafi, baya magana, sai dai mazaje ne suke maganar abinda yake cikinsa.}
Sai wani yace: Bamu labarin Ajali, me ya s aka sanya ajali tsakaninka da su?
{Don jahili ya sani, wanda ya sani kuma ya tabbatar, mai yuwa All..mai girma da daukaka ya kyautata al-amarin wannan al-ummar a cikin wannan tsagaita wutan da muka yi}
A nan sai Imam (a) ya ga cewa sun gamsu da maganganunsa, sai yace masu {Ku shiga gari, All.. ya yi maku rahama}.
Suka amsa kiransa, sai ya suka shiga gari gaba dayansu tare da shi. Amma sun kasance kan akidunsu, suna kuma yada su cikin mutanen Basra, suna kuma tada hankali daga lokaci zuwa lokaci. Al-amari ya kai ga wata rana, Imam (a) yana khuduba a cikin masallaci sai wani daga cikinsu, ya kaste masa maganarsa, tare da karanta inda All..yake fada a cikin Alkur’ani
{Idan ka yi shirka, lalle ayyukanka zasu baci, kuma lalle zaka kasance daga cikin masu asara} Zumur 65.
Sai Imam (a) ya amsa masa da wata ayar Alkur’ani inda All..yake cewa,
{Ka yi hakuri, Lalle alkawalin All..gaskiya ce, kuma kaga wadanda basu da yakini su kauda hankalinka} Al-Rum aya ta 60.
Amma a hankali a hankali al-amarin khawarijawa yana kara tabarbarewa, don sun fara jawo rashin zaman lafiya a cikin al-umma musamman a Kufa, har ya kai ga suna cutar da mutane, sun jefa tsoro da rashin amince a cikin mutane.
Ana cikin wannan halin ne sai Mu’awiya dan abu sufyan ya aikawa Imam sako inda a cikinsa yake neman ya cika al-kawali na aika tawagarsa zuwa wajen yankin hukunci tsakaninsa da Imam (a).
A lokacin Mu’awiya ya san cewa ya murmure daga kayen da ya so samun sojojinsa, in ba don kaidin da suka yiwa sojojin Imam (a) ba. Sannan ya san cewa fitana ta auku a cikin mutanen kufa na bayyanar khawarijawa, don haka idan za’a sake komawa yaki ma, wadanda zasu fito tare da Imam (a) kadan ne.
A na cikin wannan halin ne, sai lokacin zuwa taron hukunci tsakanin Imam Ali (a) da kuma Mu’awiya ya karato. Sai Imam (a) ya shirya tawaga ta mutane 400 zuwa.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi Ya Ce: Bai Kamata Dokar Kasa Da Kasa Ta Zama Abin Wasa A Hannun Amurka Ba October 4, 2025 Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza October 4, 2025 Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza October 4, 2025 Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72 October 4, 2025 Turkiyya Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaban Amurka Kan Daina Sayen Iskar Gas Daga Rasha October 4, 2025 Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump October 4, 2025 Iran ta bukaci duniya ta bijirewa haramtattun takunkuman Amurka October 4, 2025 Duniya na yabawa Hamas kan amincewa da daftarin Trump October 4, 2025 Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “ October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jayayya da su masu sauraro
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba.
Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar.
Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin moriyar tsoffi ga iyalai miliyan 2.24 dake da tsoffin da suke fuskantar matsaloli.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samar da tsare-tsaren hidimomin kula da tsoffi guda 500 a cikin unguwanni da wasu unguwanni masu dacewa da zaman tsoffi guda 2,990 da kuma dakunan cin abinci 86,000 ga tsoffin. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA