HausaTv:
2025-10-13@15:44:30 GMT

Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba

Published: 28th, September 2025 GMT

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa gwagarmaya ba za ta  bari a kwance damarar ta ba, kuma za ta shiga fada irin na Karbala idan hakan ya kama, ya kara da cewa: “Za mu fuskanci duk wani aiki da zai yi wa Isra’ila hidima, ko da kuwa an mayar da shi tamkar wani aiki na kasa.

A jawabin da ya gabatar a yayin zagayowar cikar shekara guda da shahadar Sayyed Hassan Nasrallah da Hashem Safieddine, Sheikh Qassem ya mayar da martani ga kalaman manzon Amurka Tom Barrack, wanda ya ce Washington na son kwance damarar kungiyar Hizbullah, kuma ba za ta ba sojojin makamai domin tunkarar Isra’ila ba. Ya kara da cewa ” kwance damarar makamai na nufin kwance damarar dakarun gwagwarmaya bukata ce ta Isra’ila domin cimma manufofinta.

Sheikh Qassem ya yi kira ga gwamnatin Lebanon da ta cika aikinta na sake gina wuraren ‘ya kasar da Isra’ila ta rusa tare da ware kasafin kudi domin hakan, koda kuwa kadan ne. Ya nanata cewa Fifita maslahar kasa dole ne ya kasance kan gaba a cikin ajandar, kuma cimma hakan na bukatar hana Isra’ila ci gaba da zama a Lebanon.

Ya kara da cewa kiyaye hadin kai na cikin gida da kuma yin aiki don farfado da kasar Labanon ya zama wajibi,  kuma gwagwarmayar al’ummar kasar ita ce tushen karfinta.

Ya kuma yi kira da a aiwatar da yerjejeniyar Taif, wadda ta tanadi cimma nasarar ‘yantar da dukkanin yankunan kasar Lebanon da Isra’ila ta mamaye ta hanyar gwagwarmaya.

Ya ci gaba da cewa, “Muna goyon bayan gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kan lokaci,” yana mai cewa “gwamnati ta yi wani babban kure a lokacin da ta yanke shawara kan batutuwa da suka shafi makaman Hizbulah.”

Ya kara da cewa, suna son sojojin kasar Lebanon su yaki mutanensu, kuma muna goyon bayan sojoji  wajen tunkarar makiya na hakika, kuma a kodayaushe muna tare da su.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Shugaban Argentina ya nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar  Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran  Dr Ali Larijani  Ya Isa Birnin Berut . September 27, 2025 Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba September 27, 2025 MDD : Isra’ila na kai harin bam a Gaza kowane minti 8 ko 9 September 27, 2025 MSF ta dakatar da ayyukan birnin Gaza saboda hare-haren Isra’ila September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Ya kara da cewa ya kara da cewa kwance damarar

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini

Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun kungiyar Hamas kamar yadda aka tsara.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta bayyana cewa kungun fursinoni yahudawa masu rai 7 ne kungiyar ta Karba daga dakarun Hamas a yankin da ake kira Nitsarin a tsakiyar zirin gaza, da misalign karfe 8 na safe a yayinda gungu na biyu kuma wanda ya kunshi yahudawa 10 masu rai kungiyar Agajin ta karbesu a garin Khan Yunus dake areacin gaza da misalign karfe 10 na safe.

Labarin ya kara da cewa an ga motocin bas -bas suna isa kurkukun da ake tsare da falasdinawa. Sannan ana saran yahudawan zasu saki fursinoni 2000. Amma kada a manta bayan  fara yakin tufanul Aksa HKI ta kama falasdinawa fiye da 10,000 a tsakanin Gaza da yamma da kogin Jordan.

Gwamnatin HKI dai ta tabbatarwa yahudawan kasar kan cewa ba zai yu a gano ko da gawan wasu wadanda kungiyar Hamas ta kama a ranar 7 ga watan Octoba ba saboda sun lalace sun bace a cikin kasar

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal October 13, 2025 Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Bayyana October 13, 2025 Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice   October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
  • An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini
  • Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
  • Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara
  • Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta
  • Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta