Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD
Published: 28th, September 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sake jadda yin Allah-wadai da kisan tsohon shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, inda ta bayyana cewa, matakin ya kasance karara a matsayin keta dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
An fitar da sanarwar ne a wannan Asabar, a daidai lokacin da ake bukin cika shekara guda da kisan gillar da aka yi wa Shahid Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine, wadanda aka kashe a shekarar da ta gabata a wasu hare-hare da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Beirut.
A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta kira kisan gillar a matsayin wani babban ta’addanci da nufin yi wa kasa mai cin gashin kanta mamba a MDD zagon kasa.
Ma’aikatar ta ce, ko shakka babu, hukunta masu laifi yahudawan sahyoniya kan wannan ta’assa zai kasance wani muhimmin mataki daga kasashen yankin.
Bugu da kari, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta jaddada rawar da Nasrallah ya taka a cikin shekaru 30 da suka gabata wajen jagorantar gwagwarmaya da kasar Lebanon ke yi kan wuce gona da iri da na Ira’ila.
Tehran ta jaddada goyon bayanta ga Beirut, inda ta yi kira ga kasashen yankin da su amince da karuwar barazanar da gwamnatin Sahayoniya ta ke yi a kansui, da kuma karfafa zaman lafiyar kasar Labanon, da tsaro da kuma ‘yancin kai.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta bayyana cewa, an yi amfani da na’urori na zamani na Amurka wajen aiwatar da ta’addancin da ya kai ga shahadar Nasrallah a yankunan da ke birnin Beirut.
Ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika, inda ta kira masu laifin a matsayin matsorata kuma masu jinni a hannunsu.
Yayin da take yin tsokaci kan abin sayyid Nasrallah ya gadar, sanarwar ta yi nuni da cewa: A yayin da ake gwabza fada a kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrullah ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ikon kasar ta Labanon da kuma tabbatar da kariyar da take da shi daga kasashen waje.
Ya soki manufofin gwamnatin Sahayoniya a matsayin wasa mai hatsarin gaske da ke shafar yanayin yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Argentina ya nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran Dr Ali Larijani Ya Isa Birnin Berut . September 27, 2025 Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba September 27, 2025 MDD : Isra’ila na kai harin bam a Gaza kowane minti 8 ko 9 September 27, 2025 MSF ta dakatar da ayyukan birnin Gaza saboda hare-haren Isra’ila September 27, 2025 Amurka ta soke bizar shugaban Colombia bayan shiga gangamin goyon bayan Falasdinu a New York September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: aikatar harkokin wajen kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan harkokin ƙasashen duniya ya bayyana kasancewar al’ummar Iraki da sanin da ba a taɓa gani ba a zaɓen da aka yi kwanan nan a matsayin babban nasara da ba a taɓa gani ba a tarihin Iraki.
Ali Akbar Velayati, Mai Ba da Shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Harkokin Ƙasa da Ƙasa, ya bayyana a ranar Asabar a wani taro da Seyed Mohsen Hakim – babban mai ba da shawara ga Seyed Ammar Hakim kuma mataimakin shugaban ƙungiyar Hikimar Ƙasa ta Iraki – cewa dangantakar da ke tsakanin Iran da Iraki tana da ƙarfi, tarihi, tana da tushe sosai, kuma ba za a iya karya ta ba. Ya ƙara da cewa tana ƙara ƙarfi kowace rana kuma za ta zama tushen bege ga duniyar Musulunci.
A nasa ɓangaren, Hakim ya bayyana yanayin da ake ciki a Iraki bayan zaɓen da aka yi kwanan nan, yana mai bayyana fitowar jama’a da kuma shiga cikin al’umma ba tare da wani yanayi ba – duk da makircin maƙiya – a matsayin babban nasara ga ƙasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci