Sabon Farashin Jigilar Mahajjata A 2026, Ƴan Arewa N8.2m, Ƴan Kudu N8.5m
Published: 27th, September 2025 GMT
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da farashin aikin Hajjin 2026, inda aka samu ragin kaso 9.7% cikin ɗari idan aka kwatanta da farashin Hajjin bara 2025.
A cewar sanarwar da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya fitar ranar Juma’a da daddare, alhazai daga gundumar Maiduguri–Yola (Borno, Yobe, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.
67, yayin da sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67. A gefe guda kuma, alhazai daga jihohin Kudu za su biya N8,561,013.67. Wannan na nufin cewa kowanne mai niyyar tafiya Hajji a bana zai samu ragin kimanin N200,000 ƙasa da farashin 2025.
Farfesa Usman ya ce farashin ya biyo bayan doguwar tattaunawa da shugabannin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki tare da amincewar gwamnatin tarayya. Ya kuma bayyana cewa tawagar NAHCON da ke Saudiyya ta riga ta rattaba hannu da kamfanin Mashareeq Al-Zahabiyya a matsayin mai kula da walwalar ƴan Nijeriya na Hajjin 2026 da kuma kamfanin sufuri na Daleel Al-Ma’aleem.
Shugaban NAHCON ya buƙaci duk masu niyyar tafiya aikin Hajjin 2026 da su kammala biyan kuɗinsu kafin ranar 31 ga Disamba, 2025. Ya ce wannan tsari zai ba da damar shiryawa cikin lokaci, tare da tabbatar da ingantaccen sufuri da wuraren masauki ga dukkan mahajjata daga Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan.
A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton.
Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba.
Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa a ayyukan tsaro da ake gudanarwa a fadin jihar.
A wani labari mai nasaba da haka, Kungiyar Matan Sojoji da ‘Yansanda (DEPOWA) ta yaba da jajircewa da sadaukarwar dakarun rundunonin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro, wadanda ke ci gaba da sadaukar da rayuwarsu domin kare kasar.
Kungiyar ta kuma yi addu’a ga Allah domin kare mazajensu, wadanda ke kwana suna tashi a kan bakin aiki domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya.
Shugabar kungiyar DEPOWA, kuma matar Babban Hafsan Tsaro na Kasa (CDS), Mrs. Oghogho Musa, ta bayyana wannan godiya tare da yin addu’o’i a birnin Abuja yayin gudanar da wasan motsa jiki na rawa (Dance Aerobics Edercise) da aka gudanar a makarantar DEPOWA da ke sansanin Mogadishu.
Shugabar DEPOWA ta kuma jaddada kudirin kungiyar na gudanar da yakin addu’a da godiya na tsawon shekara guda ga dakarun da ke bakin daga, domin nuna yabo da godiya ga jajircewarsu wajen kare kasar Nijeriya, duk da hadarin da ke tattare da aikin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA