Aminiya:
2025-08-16@23:14:10 GMT

APC ta nemi INEC ta soke zaɓen cike gurbin Kano

Published: 17th, August 2025 GMT

Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano.

Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana.

An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC

A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu rahotannin da suka tabbatar an samu rikici a Shanono, Bagwai da Ghari.

Ta ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe sakamakon tashin hankali, yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan lamarin.

“APC na kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta soke zaɓukan cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma zaɓen mazaɓar Ghari a Jihar Kano saboda tashin hankali da kuma tada hargitsin ’yan daba da aka samu.

“’Yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa rumfunan zaɓe da dama,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa barin zaɓukan su ci gaba da gudana ya saɓa wa tsarin gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, kuma hakan zai iya zama barazana ga zaɓuka a gaba.

Wasiƙar da Jam’iyyar APC ta aike wa INEC kan buƙatar soke zaɓen cike gurbi a Jihar Kano

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bagwai Ghari Zaɓen Cike Gurbi zaɓen cike gurbi soke zaɓen

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13

Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomin ci gaban Ƙananan Hukumomi 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar.

Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu cikin rana guda.

Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano

Kakakin majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya bayyana hakan ne yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kan ƙudirin, wanda aka gabatar wa majalisar kwanaki uku da suka gabata.

Ya ce majalisar ta yi gaggawar karanta ƙudirin saboda muhimmancinsa, domin zai taimaka wajen kusantar da gwamnati ga jama’a.

Hakazalika ya ce zai kawo ci gaba a ƙauyuka, da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar ta hanyar da ta dace.

Kakakin ya ƙara da cewa an shirya sauraron ra’ayin jama’a domin samun shawarwari daga al’umma, shugabanni da ƙungiyoyi domin ƙara wa ƙudirin armashi.

Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13
  • Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya
  • APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano
  • An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano
  • Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC
  • HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya
  • An Taƙaita Zirga-Zirga A Ƙananan Hukumomi 4 Kafin Zaben Cike Gurbi A Kano
  • Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
  • Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC