Leadership News Hausa:
2025-10-13@17:58:48 GMT

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

Published: 15th, August 2025 GMT

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu.

Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani.

“Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance.

“’Yan kasuwa da ke habaka kasuwancinsu a zamanance suna da wuri a Ikom da masu yin kayan daki a Kalabar da masu zanen kaya a Ogoja, Ugep, ko Odukpani.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa tsare-tsaren gwamnatina na sabuwar fata ke nufin samar da yanayi mai kyau ga kanana da matsakaitan karkokin domin su samu damar habaka.

“Kudurinmu ba shi ne, ba kawai bayar da rance ko tallafi ba, gina wani tsarin da zai samar da ababen more rayuwa da kuma karfafa basirar ‘yan kasuwa,” in ji shi.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kuros Ribas, Bassey Otu ya bayyana taron harkokin kasuwanci kanana da matsakaita karo na 8 a matsayin matsayin wata manufa mai matukar muhimmanci a tsakanin jihar da gwamnatin tarayya.

Otu ya ce manufar ita ce inganta ruhin harkokin kasuwanci na ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: harkokin kasuwanci

এছাড়াও পড়ুন:

Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor

Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.”

 

Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari October 11, 2025 Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor
  • Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida