Mali: An kama wasu Manyan Janar-Janar dan kasar Faransa bisa zargin yunkurin juyin mulki
Published: 16th, August 2025 GMT
Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi.
Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana hakan ta gidan talabijin na kasar a yammacin jiya Alhamis, inda ya ce an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an fara gudanar da bincike.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ‘yan kwanakin nan kan tsare jami’an soji. Hukumomi sun bayyana dan kasar Faransa Yann Vezilier, inda suka zarge shi da yin aiki “a madadin hukumar leken asiri ta Faransa,” tare da hadin gwiwar shugabannin siyasa, jiga-jigan kungiyoyin farar hula, da kuma sojoji a Mali.
Gidan talabijin na kasar ya watsa hotunan mutane 11 da ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulkin, wanda hukumomi suka ce an fara shi ne a ranar 1 ga watan Agusta. Kungiyar ta hada da Janar Abass Dembélé, tsohon gwamnan yankin Mopti ta tsakiya, wanda aka kora a watan Mayu bayan ya bukaci a gudanar da bincike kan kisan fararen hula da sojojin Mali suka yi a Diafarabé. Haka kuma an tsare Janar Néma Sagara, wadda ta shahara da rawar da ta taka wajen yakar ‘yan bindiga a shekarar 2012.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wata Kotun kasar Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP.
IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya.
Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji“Wannan karon za mu aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi.
“Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina kuma da tabbacin cewa ba za su uzzura wa kwamashinonin ’yan sanda ba ma.”
Ya ƙara da cewa za su tura jami’an da aka janye zuwa “wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aika ’yan sanda ga manyan mutane domin ba su tsaro na musamman, yana mai mayar da su zuwa aikin tsaro da ya shafi al’umma baki ɗaya.
Kazalila, a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba ne Tinubun ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban ya ce a ɗauki sababbin ’yan sanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauk, wanda za a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ’yan sandan da za a ɗauka.