An kafa dokar hana zance tsakanin saurayi da budurwa a Kano
Published: 16th, August 2025 GMT
Al’ummar unguwar Sharada da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun ƙirƙiro dokoki 29 domin gyara halayyar jama’a da kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu.
Daga cikin dokokin akwai hana saurayi da budurwa yin zancen dare, musamman a cikin mota, da kuma hana su wuce ƙarfe 10 na dare suna hira a waje.
Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno — INEC Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a KanoMahukuntan yankin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda damuwa kan lalacewar tarbiyya, ƙaruwa matsalolin tsaro, da kuma rashin bin al’adun da suka dace musamman a tsakanin matasa.
Wannan ba shi ne karon farko da aka taɓa kafa irin wannan doka ba a jihar.
A baya, unguwanni irin su Fagge, Tudun Yola, Kurna da sauransu sun taɓa kafa irin wannan doka, domin kula da tarbiyyar matasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: budurwa Saurayi Sharada Tarbiyya Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
A nasa tsokaci kuwa, sakataren gwamnatin Mozambique mai kula da ma’adinai Jorge Daudo, cewa ya yi lardin Shandong yana daya daga cikin larduna masu kwazo da ci gaban masana’antu a Sin, kuma yana da karfi a fannonin hakar ma’adinai, da sarrafa karafa da masana’antu. Sabo da haka, Mozambique na fatan kara yin hadin gwiwa da lardin na Shandong. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA