Cire Tallafin Mai Ya Taimaka Mana Wajen Aiwatar da Ayyuka, In Ji Gwamna Mbah
Published: 15th, August 2025 GMT
Ya ce: “A Inugu, mun sami damar cika duk abin da muka yi wa mutanen mu alƙawari a lokacin kamfen, godiya ga jarumtar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wadda ta samar mana da albarkatun da ake buƙata don aiwatar da manyan ayyuka.”
Ya kuma bayyana ayyukan da ake yi a halin yanzu a jihar, waɗanda suka haɗa da gina ajujuwa 7,000, samar gadajen asibiti 3,300, da samar da gonakin gwamnati hekta 2,000 a cikin gundumomi 260 na jihar.
Gwamna Mbah ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa manufofin Gwamnatin Tarayya baya, yana mai cewa suna da amfani ga al’ummar jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar.
Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa.
Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum.
A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri.
Malam Umar Namadi ya ƙara da bayyana cewa an ware sama da naira biliyan 74 ga bangaren noma da kiwo, sai naira biliyan 50.74 don wutar lantarki da makamashi, yayin da naira biliyan 12.68 za su tafi ga shirin ƙarfafa matasa.
Ya nuna cewa an tanadi naira biliyan 25.4 don ruwa da tsafta, sannan naira biliyan 35.4 don muhalli da sauyin yanayi.
Gwamna Namadi ya kuma gabatar da sama da naira biliyan 288 don ayyukan kananan hukumomi 27 na jihar.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa kasafin shekarar 2026 ya fi na shekarar 2025 da kaso 19 cikin 100.