Aminiya:
2025-08-15@22:50:51 GMT

Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Kano

Published: 15th, August 2025 GMT

Mutum 12 sun rasu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Samawa, da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:40 na daren ranar Juma’a a kan titin Zariya zuw Kano.

Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi

Tirela ƙirar DAF mai lambar KMC 931 ZE, wadda ke ɗauke da kaya da fasinjoji ta yi hatsarin.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta ce bincike ya nuna cewar matsala ce ta haddasa hatsarin.

Tirelar na ɗauke da mutum 19, wanda 12 daga cikinsu suka rasu, sai wasu biyar da suka jikkata.

Mutum biyu ne kacal suka tsallake rijiya da baya ba tare da sun ji rauni ba.

An kai waɗanda suka jikkata Babban Asibitin Garin Kura, sannan an kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Nasarawa.

Kwamandan FRSC na Kano, M.B. Bature, ya ziyarci wajen da hatsarin ya auku, inda ya zargi lodin kaya masu yawa da rashin bin dokokin hanya da haddasa hatsarin.

Ya gargaɗi direbobi kan haɗa kaya, dabbobi da fasinjoji a mota ɗaya.

A madadin Babban Kwamandan FRSC, Dauda Ali Biu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin mota waɗanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da kammala duk shirye-shiryen zaben ciki gurbi a kananan hukumomin Bagwai, Shanono da kuma Ghari (Kunchi) da ke Kano wanda za a gudanar a ranar Asabar.

Kwamishinan INEC a Kano, Zango Abdu, wanda ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai, ya ce an riga an raba kayan zabe masu muhimmanci da wadanda ba su da muhimmanci a kananan hukumomi da abin ya shafa.

Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi An kama Mai Unguwa kan yi wa yarinya fyaɗe a Gombe

Ya ce, “Tun kusan makonni uku da suka gabata aka riga da tura kayayyakin da ba su da muhimmanci wadanda aka tanadar wa mazabu da rumfunan zabe.

“Yanzu haka kayan zaben masu muhimmanci sun iso, kuma za a tura su kananan hukumomi yau da yamma tare da wakilan jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro.”

Ya kuma bayyana cewa an kammala horas da dukkan ma’aikatan wucin gadi kuma an tura su wuraren da za su yi aikin, yayin da jami’an tsaro karkashin kwamitin tsaro na haɗin gwiwa sun ba da tabbacin duk wasu tanade-tanade da suka kamata.

Da yake karin haske, Zango ya ce duk na’urorin BVAS wadanda za a yi amfani da su wajen tantance masu kada kuri’a su ma an tanade su tare da tabbatar da nagartarsu.

Ya jaddada kudirin INEC na gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci, inda ya ce hukumar za ta sanar da wanda ya yi nasara ne kawai bisa kuri’un da aka kada.

“Babbar damuwarmu a yanzu ita ce ’yan siyasa. Amma dai su ma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, sun kuma shaida mana za su yi zabe cikin lumana. Saboda kwanciyar hankali ne kawai zai ba ’yan kasa ’yancin zaben shugabanninsu,” in ji shi.

Dangane da yadda za a tattara sakamako, Zango ya ce za a bayyana sakamakon akwatuna a duk rumfunan zabe kafin a kai shi cibiyoyin tattarawa na mazabu.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Yunin da ya gabata ne INEC ta ayyana 16 ga watan Agustan bana, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomin na Kano.

Za a gudanar da zaben ne sakamakon rasuwar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bagwai da Shonono, Halilu Ibrahim Kundila na jam’iyyar APC, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar 6 ga watan Afrilun 2024.

Sai dai kuma za a gudanar da zaben cike gurbin ne a Karamar Hukumar Ghari — wadda a baya ake kira Kunc— a rumfunan zabe 10 da masu kada kuria 5200 bisa umarnin kotu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kafa dokar hana zance tsakanin saurayi da budurwa a Kano
  • Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani
  • An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi
  • Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi
  • An Taƙaita Zirga-Zirga A Ƙananan Hukumomi 4 Kafin Zaben Cike Gurbi A Kano
  • Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC
  • ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
  • ’Yan sanda sun kama matashi kan zargin aikata fashi a Gombe
  • ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai