Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
Published: 15th, August 2025 GMT
Bugu da kari kuma, gudummawar da Nijeriya ke bayarwa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya ba za su misalta tu ba, wanda hakan ke jaddada aniyarta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manufofinta na kasashen waje a al’adance suna nufin ingantawa da kuma kare muradun Nijeriya tare da tallafa wa hadin kan Afirka.
Gabatar da ajandar “4D”, a sakamakon haka, yana wakiltar sauyin da aka samu a lokacin da ya dace, wanda hakan zai bude damar karfafa hadin gwiwar da kasashen duniya, tabbatar da zaman lafiya na duniya, da kuma bunkasa matsayin Nijeriya a idon duniya. Sai dai, nasarar wadannan manufofin ya ta’allaka ne a kan aiwatarwar su mai inganci.
Ya kamata a lura da cewa Nijeriya ta tsunduma cikin harkokin diflomasiyya da dama a bara, ciki har da kulla wasu muhimman yarjejeniyoyi da Jamhuriyar kasar Sin. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci Abuja, domin jaddada alkawuran da aka dauka a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2024, inda aka rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi guda 10. Hakazalika, firaministan Indiya Narendra Modi ya ziyarci Nijeriya, inda ya bayyana aniyar kasarsa na zuba hannun jari a wasu muhimman sassa kamar a bangaren noma, samar da abinci, sadarwa, fasaha da bayanai, da kuma tsaro.
Shugaba Tinubu ya kuma gudanar da rangadin diflomasiyya, inda ya halarci taron G20 a Brazil da kuma kai ziyara a Faransa da Afirka ta Kudu da dai sauransu. Wadannan alkawurra an yi su ne da nufin karfafa martabar Nijeriya a idon duniya da kuma samar da fa’idodi na gaske ga kasar.
Duk da yake wadannan tafiye-tafiye na diflomasiyya abin yabawa ne, amma kuma dole ne su kasance su samar wa da kasar jari mai ma’ana da fa’ida ga ‘yan Nijeriya.
Sai dai a halin yanzu, hakan ya yi nisa daga zahirin abin da yake faruwa. Dole ne gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu muhimmanci domin tabbatar da cewa manufofin kasashen waje na Nijeriya sun fifita muradun kasa tare da kare ‘yan kasarta a kasashen waje. Wannan shi ne ainihin manufar “4D”.
Za a iya danganta raguwar tasirin Nijeriya a fagen duniya da tabarbarewar tattalin arzikin da aka shafe tsawon shekaru ana yi, wanda ya tilastawa ‘yan kasar da dama neman ingantacciyar damammaki a kasashen waje, galibi a cikin yanayi mai wahala da wulakanci. Idan ana son a sauya wannan hali, dole ne gwamnatin Tinubu ta gaggauta farfado da tattalin arzikin kasar domin fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci.
Ana iya cimma wannan ta hanyar jawo hankalin masu zuba hannun jari daga kasashe irin su Indiya, Sin, Afirka ta Kudu, da Faransa, musamman a fannoni kamar hakar ma’adinai, aikin gona, da ICT, wadanda ke da fa’ida masu yawan gaske. Har ila yau, dole ne Nijeriya ta mayar da hankali wajen bunkasa harkokin kasuwanci na yanki, kamar samar da kasuwar samun kayayyakin amfanin gona da za su hada masu samarwa da masu shigo da kayayyaki, ta yadda za a rage dogaro da kuma fadada kasuwancin kayayyakin Nijeriya.
Domin manufofin Nijeriya na kasashen waje su yi tasiri, dole ne ta fara magance bukatun ‘yan kasarta. Gwamnatocin da suka gada sun yi ta fafutika wajen yin amfani da damar hadin gwiwar kasa da kasa domin samar da ayyukan yi, da jawo jari, da kawar da talauci. Alkaluman sun yi muni: a tsakanin 2023 zuwa 2024, kashi 63% na ‘yan Nijeriya – kimanin mutane miliyan 133.3 – suna rayuwa cikin kangin talauci, a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS). Rashin aikin yi na matasa ya kasance wani muhimmin batu, a yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 34.6% a karshen shekarar 2024, inda hauhawar farashin kayayyakin abinci ma ya fi kamari.
Rahoton Tattalin Arziki na Afirka (ERA 2023) ya jaddada gaggawar magance kalubalen tattalin arzikin Nijeriya. Ya gano manyan gibi guda uku – kwarewa, abubuwan more rayuwa, da kuma ingancin cibiyoyin (gudanarwa) – wadanda dole ne a gyara su domin gina tubuli mai karfi domin ci gaba.
Mun yi imani wannan ita ce hanya madaidaiciya. Dole ne gwamnatin Tinubu ta fito da tsare-tsare masu kyau na ci gaban kasa, samar da shugabanci nagari, da aiwatar da gyare-gyaren tsari a dukkan bangarori masu muhimmanci.
A yayin da Nijeriya ke fuskantar tabarbarewar tattalin arziki da kuma yanayi na cire fata a tsakanin ‘yan kasar, dole ne gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye tare da rungumar tsarin hulda da kasashen waje na Ambasada Yusuf Tuggar. Manufofin kasashen waje da zai jawo zuba hannun jari, samar da ayyukan yi, da magance tushen talauci, tabbas wadannan a karshe za su samar da nasara. Da duk wani abu da ka iya rage barazana ga barin Nijeriya ta makale a tsaka mai wuya a tsakanin yiwuwarsa da tabarbarewar ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya dole ne gwamnatin Tinubu ta a kasashen waje Nijeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu.
Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu.
A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro.
Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar hankali.
A taron G20 da aka yi a Afirka Ta Kudu, Tinubu ya bukaci shugabannin duniya su samar da tsarin kudi na kasa da kasa, tare da magance matsalolin bashi.
Ya ce tsarin da ake amfani da shi a yanzu ya zama tsohon yayi, kuma bai dace da kalubalen wannan zamani ba. ya kuma nemi a samar da ka’idojin duniya da za su tabbatar da cewa kasashen da ke samar da muhimman ma’adanai ciki har da Nijeriya, suna amfana da su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci