Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
Published: 15th, August 2025 GMT
Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci.
Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne.
Abin takaici shugabannin wadannan kungiyoyi na dattawan Arewa, babu damar da ba su samu ba. Amma Fisabilillahi in da sun yi amfani da damar da suka samu, da yanzu za ai magana akwai marabarata a Arewa ko matasa masu bangar siyasa? Wasu gwamnoni cikin su. Yanzu misali, in banda me tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekaru zai yi a kungiya? Wanda yai gwamna shekara 8, yai minista, yai sanata, kuma maida kan shi baya ya dawo kungiya? Kuma kungiya ba irin ta su tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ba. Ai a duniya, wadanda suka taba rike mukaman siyasa na kafa gidauniya amma ba kungiyar siyasa ba. Ba kungiyar neman abinci ba da tattaunawa kan mukaman siyasa. Gidauniya aka sani mai yaki da cututuuka,ko mai bunkasa ilmin mata da yara da sauran matsaloli ba kungiyar assasa kabilanci ba da siyasar ci da ceto
Wadannan mutanen ta kare masu ne kawai. Ba su da abin fada shi ne suka dawo suka dauki kahon tsana suka kafa ma gwamnatin Shugaba Tinubu. Babu wani kishin Arewa a tare da su.
Wadanne Ayyuka Tinubu Ya Gudanar A Arewa?
Tunda aka kirkiri Nijeriya,ba ai shugaban da ya dauko hanyar ‘yantar da Arewacin Nijeriya ba, kamar shugaba Tinubu. Misali, su wa za su fi cin gajiyar hukumar kiwo? Arewa an santa da noma da kiwo. Tinubu ya kirkiri hukumar kiwo ya dauko minista daga Arewa Mukhtar Idi Maiha ya damka amanar wurin. Ya dauko mutane masu daraja kamar Farfesa Attahiru Jega ya sanya a wurin domin a zamanantar da kiwo, a kawo karshen fadace fadace tsakanin manoma da makiyaya, sannan Nijeriya ta samu karuwar kudaden kasashen waje. A gabanka, lokacin babbar Sallah, shugaban mulkin sojar janhoriyar Nijar ya hana a shigo da dabbobi a Nijeriya. Wannan babban sako ne cewa mu tashi mu farka. Kuma Arewacin Nijeriya za mu dogaro da kanmu harma mu ciyar da Nijeriya da nama da madara idan muka ci gaba da ba gwamnatin Tinubu goyan baya.
Shugaba Tinubu ya bude iyakokin da Buhari ya kulle, abinci ya karu a kasa. Shugaba Tinubu ya ba da ayyukan hanyoyin da gwamnatin Buhari ta watsar kamar layin dogo daga Kano zuwa Maradi, hanyar Sokoto zuwa Badagary, Akwanga zuwa Gombe, Kafur Marabar Kankara zuwa Gidan Mutum Daya, Kano zuwa Kongolom da sauran su. Ana ci gaba da aikin bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa Kano, ana ci gaba da aikin hako mai a Kolmani. Shugaba Tinubu ya ba Arewa mukaman da sune gwamnati. Ministan tsaro guda biyu duk Arewa ne. Mai ba shugaban kasa akan tsaro dan Arewa ne. Kuma ba wanda aka hana yai aikin shi. Misali, ko Hasidin Iza Hassada ba zai ce kashe ‘yan ta’adda dubu goma sha uku ba komi bane. Ko ‘yanto mutanen da akai garkuwa da su sama dubu sha daya ba daidai ba ne.
An ba mu mukamin ministan kiwon lafiya da walwala, Muhammad Ali Pante da duniya ke alfahari da shi saboda an tabbatar da kwarewarsa. Misali, cikin shekaru 2 kawai, an gyara kananan asibitocin guda 500 a jihohin Arewa. An sakar fannin kiwon lafiya matakin farko kudi Naira Biliyan 20 a Arewa domin rage mutuwar mata masu haihuwa da yara kanana. An yi ma mata dubu 4 fidar haihuwa (CS) kyauta. An yi miliyoyin yara allurar rigafin kyanda,zazzabin cizon sauro da farar masassara. Mutane miliyan daya da dubu dari tara masu dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki na ci gaba da samun magani duk da datse tallafi da gwamnatin Amurka ta yi. da sauran su.
Tinubu ya ba mu karamar ministan Ilmi, Suwaiba. A shekarar 2024, gwamnatin shugaba Tinubu ta ba kowace jihar Naira Miliyan 598 ta horas da malamai, ta gina makarantu na zamanin na firamare 37 da sauran su. Hukumar TETFUND baki daya hannun ‘yan Arewa take. Babban Sakataren hukumar Sonny Echono da shugaban Board din Aminu Bello Masari duk ‘yan Arewa ne,kuma dubi irin aikin da ake a wurin?
Batun ba dalibai lamani,abi ne mai kyau da zai amfani ‘ya’yan talakawa su sami ilmi mai inganci domin fita daga kangin talauci. Tsaffin Arewa masu ci da gumin Arewa ba su damu da ilmin ‘yan uwansu ba. Sun fi kyautata ma kawalai, karuwai da ‘yan bangar siyasa.
Idan ka koma bangaren aikon gona, Abubakar Kyari da ayyukan da ake. Takin kawai a shekarar 2024 karkashin tsarin AgriPocket sun ba manoma miliyan 2 a kan rangwamen farashin kashi hamsin. Babban Bankin Nijeriya, ya rama manoma da ba na boge ba buhun taki miliyan biyu da dubu dari biyu.
Saboda haka farfaganda ce ta siyasa masu fadar ba a yi da Arewa. Kamata yai su fito fili su ce ba a yi da su kawai.
Kiranka ga al’ummar Arewa?
To ni kirana ga matasan Arewa, shi ne, kada su bari masu ci da ceto su maida su makaman siyasa. Tinubu ya ce kowa zai iya zama mai ilmi. Ko farfesa kake so, ga kofa an bude. Saboda zabi ya gare ka ka bi hanyoyin da aka tanada domin amfana da tsare-tsaren gwamnati, kamar NELFUND da sauran su.
Mutanen Arewa mu sani zaman lafiya da hadin kan Nijeriya ya fi burin wani dan siyasa. Maganar kabilanci da bangaranci mu barta, saboda kasashe da yawa sun tarwatse,an yi yake yake a kasashen Afirika da dama saboda wasu ‘yan siyasa sun fito da batun kabilanci.
Rwanda, Saliyo, Liberia, Ibory Coast da sauran su duk sun danin sakamakon siyasar banza ta kabilanci. Mulki zai dawo a 2031 ba 2027 ba, kuma shugaba Tinubu ne yakamata a sake zabe saboda shi ya gano matsalar Najeriya,kuma ya dauki hanyar magance ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da sauran su a gwamnatin
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi
Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi.
Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja.
Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu har lahira a Bayelsa Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar“Shugaban ƙasa [Tinubu] da muƙarrabansa sun yi ƙoƙari sosai wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya.
“Wannan namijin ƙoƙarin na Tinubu abu ne da ya zama dole a yaba masa da ba kowa zai iya yi ba.
Tsohuwar Ministar Kuɗin ta Nijeriyar ta ƙara da cewa, yanzu aikin da ke gaban shugaban shi ne ya haɓaka tattalin arzikin ta yadda kowane ɗan ƙasa zai samu na kansa cikin sauƙi.
Ngozi ta yi kira ga gwamnatin Nijeriyar ta tanadi hanyoyi da dabarun sauƙaƙa wa talakawan ƙasar da ke fama da raɗaɗin tsare-tsaren tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Duk da ta yaba wa shugaban ƙasar kan tsare-tsarensa na tattalin arziki da suka haɗa da cire tallafin man fetur, tsohuwar Ministar Kuɗin ta ce dole ne gwamnatin ta tallafa wa ’yan ƙasar.
Iweala ta ce “muna ganin shugaban ƙasar da gwamnatinsa sun daidaita tattalin arzikin Najeriya, amma duk da haka sai sun tabbatar da ɗorewar sauyin mai kyau da aka samu zuwa yanzu.”