2025-09-17@21:52:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2547

«karamar hukumar»:

      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
    Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
    Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD. Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana. Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a...
    Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025. Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci. Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696. Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar. Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba. Sai dai an...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai. Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu. Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina...
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje. Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma. Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
    Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS. DSS wadda ta kafa hujja da sashe na...
    “Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.   “Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar. Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya...
    Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce. Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025. Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa. ’Yan bindiga sun kai wa sojoji...
    JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa  wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar. An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin...
    An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na  69TH  a jiya Litinin, inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da ya shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yakejagorantar tawagar Iran a taron. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa a irin wannan taron na shekara-shekara inda kuma aka tattauna abubuwa masu muhimmanci dangane da makamashin Nukliya. Kafin ya bar nan Tehran Eslami ya ce zai gabatar da al-amura wadanda suka shafi sabawa dokokin hukumar da IAEA ta kasa. Ya kuma kara da cewa JMI ba zata saba barin hakkinta tashe makamashin Uranium wanda ya zo cikin yarjeniyar NPT. Eslami ya kammala da...
    Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin. Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe. Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Wannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina. A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar. Yarjejeniyar sulhu da aka cimma...
    Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka. NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar. A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun. Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.   Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.   Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.   Sai dai kasa...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.   Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.   Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.   Sai dai kasa...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai. A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su...
    A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara. A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar. Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye...
    Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje. Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli. Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja. Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba. Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II “Za mu...
    Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.” Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce harin, ha’inci ne da wauta.” Sakatare-Janar na Kungiyar ya bayyana “cikakken goyon baya” ga Qatar bayan abin da ya kira “cin zarafin Isra’ila”, yana mai jaddada cewa dole ne kasashen duniya su dauki kwakkwaran mataki kan Tel Aviv. Shi ma da yake jawabi a taron share fagen kasashen musulmin da na Larabawa, firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar. Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi suka halarci taron gaggawa na Doha, domin tattauna harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a kasar Qatar. Babban jami’in na Hamas ya yi kira ga shugabannin yankin da ke halartar taron da su mayar da Isra’ila saniyar ware a siyasance da ta fuskar tattalin arziki...
    Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin. Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin. Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani...
    A yau Lahadi ne wakilan kasashen Sin da na Amurka, sun isa birnin Madrid na kasar Sifaniya, domin gudanar da tattaunawa game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya. Cikin kwanaki masu zuwa, sassan biyu za su zanta game da batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba haraji, da karya ka’idar kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar cinikayyar Sin ya tabbatar a ranar Jumma’a. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa Ibom Shirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa. Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka? Ni haifaffen ɗan Zaria ne, wani gari da ake cewa, Samaru ana yi masa laƙabi da Samarun Zaria. Kuma nan nake a Hayin Dogo layin Ɗahiru Baban Naira. A nan na tashi tare da iyayena, mahaifina ana ce masa Malam Hassan mai maganin gargajiya, gida mai almajirai. Bayan na taso iyayena suka kai ni makarantar Allo, bayan nayi shekaru biyu aka dawo da ni aka saka ni a firamare. Na samu na yi ‘primary three’ dan ko gamawa ban yi ba, daga nan aka ƙara kai ni...
    Rahotanni sun bayyana cewa an fara taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da na musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, domin share fage na taron shuwagabannin kasashen da zaa yi gobe litinin in mai duka ya kaimu , domin tattaunawa kan harin baya bayan nan da Isra’ila ta kai Qatar, Taron zai tantance matakin diplomasiya da zaa dauka kan hari da Isra’ila takai kasar  Qatar a yankunan fararen hula da zimmar kasashe jamai’an kungiyar Hamas, harin yayi sanadiyar shahadar mutane 5 har da jami’an tsaron kasar  Qatar, kuma harin ya fuskancin yin tir daga kasashen duniya. Taron gaggawar da kungiyar kasashen musulmi  oic ta kira yana nuna yadda ake goyon bayan kasar Qatar a yankin, da kuma nuna damuwarsu...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan  Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A karkashin Sashe na II, bangare na 4 na dokar, dukkan mutane da kungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card). Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin wadanda suka gaza yin rajista, ko su ki karbar bukata idan...
    Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
    An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
    A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin cire kayayyakin lantarki. “Rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno an kwashe gawar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken likitanci yadda ya kamata.” Ya jaddada cewa rundunar ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin gargaɗi ga mazauna jihar da su guji aikata lalata kayayyakin gwamnati. Daso ya ƙara da...
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal. Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa. Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a...
    Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.   Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benuwe.   Haka kuma a jihar Filato a wannan rana, dakarun Sashe ta 8 ta ‘Operation Enduring Peace (OPEP)’ sun kama wasu da ake zargin barayin ne a karamar hukumar Mangu tare da kwato makamai da alburusai da kudade.   A wani samame kuma sojojin na Shiyya ta 1 OPWS sun kwato bindiga kirar AK-47 daya da harsashi 29 a wani sintiri a...
    Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin Hukumar ta kafar sadarwar zamani duk waɗanda suke amfana da tsari da su tabbatar da bayanan Banki da suka bada da na makaranta daidai suke domin hakan ne zai bada dama ta ci gaba da samun kuɗin duk lokacin da aka tashi biya ba ater da ɓata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Mohammad Eslami ya bayyana dangane da cikakkun bayanai na halartar taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA inda ya ce: A gobe ne za a fara taron shekara- shekara na hukumar IAEA karo na 69 a birnin Vienna. Ya kara da cewa: “Iran zata tsara tare da gabatar da wani kuduri na yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
      “An biya wasu bukatunmu, gwamnati ta yi alkawarin duba sauran bukatun, don haka, an dakatar da yajin aikin, za mu dawo wuraren ayyukanmu don ci gaba da aiki a ranar Lahadi, mun yi hakan ne domin nuna fatan alheri da kuma taimaka wa ‘yan Nijeriya da ke neman lafiya a cibiyoyinmu daban-daban,” in ji Osundara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
    Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa. Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta  da ke Jega a Jihar Kebbi. Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse...
    Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari a watan Agusta, amma aka ba da belinsa. Sai dai an sake kama shi a ranar Asabar bayan rasuwar Gbadamosi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Litinin. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Andre Wright-Walters, mai shekaru 37 (05.02.1988) na Aɓery Hill, Greenwich, an gurfanar da shi a ranar Lahadi, 7 ga Satumba. Ya bayyana a gaban kotun majistare ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta. Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar. Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Sarkin ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari. “Ƙasar nan tana tashi da faɗuwa bisa ingancin shugabanni. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta. “Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna abubuwa kamar...
    A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta kara lalubo albarkatun dake bangarorin al’adu da yawon bude ido na Sichuan, da gabatar da kyawun al’adun Bashu da karfafa aikin sadarwa cikin ci gaba mai inganci na lardin Sichuan. Har ila yau, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohin bidiyo na ultra HD da na daukar murya da dakin gwaje gwajen ayyukan watsa labarai na kasa a birnin na Chengdu. (Mai fassara: Fa’iza...
    Yau Asabar, an gudanar da taron dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025 a birnin Chengdu. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, ya halarta tare da sanar da bude taron. Mahalarta na kasar Sin da na kasashen waje da suka halarci bikin bude taron sun bayyana cewa, ba za a iya raba tinkarar kalubale da samun kyakkyawar makoma, da karfin al’adu da wayewar kai ba. Sun jaddada muhimmancin zurfafa hadin giwwar al’adu na kasa da kasa a fannonin raya ilimi, kimiyya da fasaha, al’adu, da kafofin watsa labarai don kara inganta hadin kan al’adu da mu’ammalar jama’a. Dandalin...
    Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna neman saurayin tare da sauran mazauna gidan da suka tsere. “Lokacin da jami’anmu suka isa wajen, ba kowa a cikin gidan. Saurayin da sauran mazauna gidan sun riga sun gudu,” in ji shi. Ya ƙara da cewa ’yansanda za su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da Comfort. Lamarin ya haifar da firgici da damuwa ga ɗalibai da mazauna yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Mariya Sanusi Dantata, mahaifiyar attajirin Afirka Aliko Dangote, tare da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, sun halarci gasar karatun Alƙur’ani da Maryam Shettima ta shirya a Jihar Kano. An yi gasar laƙabi da #ReciteWithShetty, inda taken shi ne “Alƙur’ani: Jagora Wajen Tsaftace Kafofin Sada Zumunta”. ’Yan bindiga sun buɗe wa ’yan zaman makoki wuta a Anambra An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Manufar gasar ita ce bunƙasa tarbiyya da inganta amfani da kafafen sada zumunta. A yayin karrama waɗanda suka shiga gasar, Shetty, ta bayyana cewa dubban yara daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka shiga gasar ta hanyar kafafen sada zumunta. “Na yi mamakin yawan mahalarta. Hakan ya nuna akwai haziƙan matasa...
    A nasa jawabin, Air Marshal, AVM JA Usman, ya yaba wa hafsan hafsoshin sojin saman bisa jajircewarsa da kuma sadaukarwa wajen ciyar da harkokin sojin sama da sauran ma’aikata gaba. ya yi nuni da cewa, taron ya sabunta ƙudirin hukumar na yin amfani da fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ya kuma isa wurin tare da gano gawar mamacin a cikin wata mota ƙirar ‘Peugeot 406’, ɗauke da lamba kamar haka; BWR-577 BF. “Ba tare da ɓata wani lokaci ba, aka kai gawar zuwa babban asibitin Asokoro, inda likitoci sukatabbatardacewa; hargawar ta fara ruɓewa. “Kwamishinan ƴansanda na babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan wannan al’amari da ya faru tare da bayar umarnin ƙara ƙaimi wajen gano ko wane ne mamacin.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci. A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai haɗa da wakilai daga Ma’aikatan Kuɗi, Tsare-Tsaren Ƙasa, Shari’a, Man Fetur, Babban Bankin Nijeriya, Haraji da Kwastam, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni, da sauran muhimman hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
    Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a yankuna daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila Dakarun Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai farmaki kan wasu wurare masu muhimmanci a yankin Jaffa da aka mamaye. Wannan farmakin na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta ne, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan ‘yan uwa a zirin Gaza, da kuma wani mataki na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kasar Yemen. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta kuma jaddada cewa; Rundunar sojin kasar ta kuma kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu...
    Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci babban taron kasashen musulmi da na  Larabawa da za a yi a Doha a ranakun Lahadi da Litinin, taron da Qatar ta kira domin samar da tallafi ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar a ranar 9 ga watan nan kan kasar ta Qatar. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce zasu halarci taron yana mai cewa shi da shugaban kasar za su gabatar da jawabai. “Lokaci ya yi da za a yi aiki, kuma kalmomi kadai ba su isa ba,” in ji shi yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na IRIB a yammacin ranar Alhamis, yana...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa  fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke yankin Ilasa-Oshodi, inda aka gano katan 277 na jabun magungunan maleriya nau’in Malamal Forte. Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja NAFDAC ta ƙara da cewa, “Ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro na Malamal Forte...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta. Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta...
    Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare. A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.” ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas. Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin...
    Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin.   Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin ayyukan da suka kamata a yi a tekun tsibirin Huangyan, kana ya bullo da shiri mai ma’ana domin rigakafin barkewar rikice-rikice. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin.   An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
    Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka ga Majalisar Dokokin Jihar domin haramta auran jinsi da kuma wasu aiyukan batsa a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a ofishin gwamnati na birnin Kwankwasiyya. A wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tauye darajar addinin Musulunci da al’adun Kano ba. ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano Ya bayyana cewa ƙudirin ya fi karkata kan hana auran jinsi ɗaya,...
    Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Adelabu, ya ce gwamnati ta samu nasarar samar da wutar lantarki da rarraba ta a matakin da ba a taɓa samu ba a tarihin ƙasar. Ya bayyana cewa bunƙasa wutar lantarki shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin tana tallafa wa makarantu, asibitoci, masana’antu da kasuwanci. Ya...
      Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da mika kudirin dokar haramta auren jinsi daya, luwadi da madugo ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi a matsayin doka. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Juma’a, ya ce gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar karo na 31 da aka gudanar a reshen gidan gwamnati da ke Kwankwasiyya City a Kano. Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta kan koyarwar addinin Musulunci ba, yana mai jaddada cewa dole ne Kano ta ci gaba...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku suka dauka na yin biris da batun harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a baya-bayan nan, da kuma barazanar da suke yi na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, lamarin da yake ganin zai kara ta’azzara halin da ake ciki. Araghchi ya bayyana hakan ne a daren Alhamis a wata tattaunawa ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres. Ya jaddada aniyar kasar Iran na kare hakki da muradun al’ummarta bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kasashe mambobinta da su yin da Allawadai da hare-haren da Amurka...
    Kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya a yawan hakkokin mallakar fasaha, a masana’antun dake karkashin bangaren tattalin arziki na fasahohin zamani ko dijital a shekarar 2024, inda karuwar da ta samu ya zarce na matsakaicin adadin na duniya A cewar hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta Sin, adadin hakkokin mallakar fasahar kirkire kirkire a wadannan masana’antu ya kai 500,000 a bara, adadin da ya karu da kaso 23.1 kan na mizanin shekara-shekara. An fitar da wadannan alkaluma ne yayin taron shekara shekara kan hakkin mallakar fasaha na kasar Sin da aka yi wa taken “Hakkin Mallakar Fasaha a Zamanin Fasahohi da Na’urori.” (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Har ila yau, karkashin wadannan shawarwari, kasashe membobin BRICS za su ci babbar gajiya daga fifikonsu, da ma alfanun dake tattare da hadakarsu wuri guda.   Zage damtse da kasashe membobin BRICS ke yi wajen karfafa cudanya, da hadin gwiwa na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da duniya ke fuskantar karin rashin tabbas, ake kuma kara fuskantar koma baya ta fuskar jituwa tsakanin wasu sassan kasashen duniya. Don haka, dandalin BRICS karin dama ce ga duniya ta rungumar juna, don kare cudanyar mabanbantan sassa, da tsarin cinikayya mai game dukkanin bangarori, har a kai ga cimma nasarar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa da kowa.   Tarihi ya sha nuna yadda cudanyar sassa daban daban ke...
    Zanga-zangar ta biyo bayan kashe jami’an ‘yansanda uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a wani shingen bincike a cikin garin Egbe.   Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya shaidawa manema labarai a Lokoja cewa, harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.   Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansanda, Miller Dantawaye, nan take ya tura rundunar ‘yansanda zuwa yankin domin fatattakar maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Don tunkarar zaɓen 2027, wata Ƙungiya a ƙarƙashin inuwar Tinubu/Barau/Atah Movement a ranar Alhamis a Kano ta shirya taron addu’o’i na musamman domin samun nasara ga shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin. Taron addu’ar wanda ya samu halartar Malaman addinin Musulunci da magoya bayan jam’iyyar APC daga Ƙananan hukumomin Jihar 44, an gudanar da shi ne a Gidan Baballiya Kurna da ke Ƙaramar hukumar Fagge. Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus A yayin taron addu’o’in  malaman sun kammala karatun Alkur’ani mai girma tare da gabatar da addu’o’i na musamman kan takarar Tinubu a wa’adi na biyu da kuma burin Barau ya zama Gwamna a 2027. Malaman sun kuma yi...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema. Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba. An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko. Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a...
    Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa idan kasashen Larabawa ba su goyi bayan ‘yan gwagwarmaya ba, to su ma za su fuskantar hare-haren Isra’ila” A jawabinsa babban sakataren kungiyar ta Lebanon ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila da Amurka suna aikata munanan laifuka a zirin Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da ke mamaye, yayin da al’ummar Falastinu suka yi tsayin daka duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta. Bugu da kari, Sheikh Naim Qassem ya yaba da sadaukarwar Iran da al’ummarta da kuma al’ummar kasar Yemen, kan yadda suka tsaya tare da al’ummar Falastinu. A cewarsa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan Falastinu da al’ummarta da kuma tsayin daka domin...
    Kungiyar kwadago ta CGT a faransa ta ce mutane 250,000 ne suka shiga zanga zangar da ake wa lakabi da ‘’A toshe komai’’ a fadin kasar, ko yake hukumomin kasar sun ce mutum 175,000 ne suka halarci zanga zangar ta jiya Laraba. Rahotannin sun ce a babban birnin kasar an yi arangama a kusa da wasu muhimman wurare. ‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar yayin da aka kona kwandon shara da dama. Babban Daraktan Kula da Sufurin Jiragen Saman ya kuma sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tashoshin jiragen sama na Marseille, Nice, Bastia, Ajaccio, Figari da Calvi, tare da haifar da jinkiri da sokewa a ranar. Bayanai sun ce...
    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya. Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba. “Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada...
    Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSQAA), ta gargadi masu makarantu masu zaman kansu kan kara kudin makaranta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar a hukumance ba. A wata takarda mai kwanan ranar 7 ga Satumba, 2023, wacce Mercy Bainta Kude, Daraktar Sashen Makarantu masu zaman kansu ta sanya wa hannu a madadin Darakta-Janar, Hukumar ta jaddada cewa “babu wani ko wata mai makaranta da zai ko za ta kara kudin makaranta ko inganta makarantar ​​ba tare da amincewar KSSQAA ba.” Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna Umurnin ya zo ne a daidai...
    Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi  hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a fara aiwatar da harajin man fetur a watan Janairun 2026 ba lokacin da za a fara aiwatar da wasu harajin da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a bana. Har yau, babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da shirin fara cire harajin kashi 5 na man fetur  da ‘yan kasa suke sha,” in ji Ministan a martanin da ya mayar dangane da cece-ku-ce...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba.   “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kasashen musulmi da na Larabawa su yi Allah wadai da yin tir da harin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga ‘yan uwanta na kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne kasashen musulmi su dauki mataki da gaske wajen tofin Allah tsina kan gwamnatin mamayar Isra’ila da yin tir da laifukan da take aikatawa kan al’ummomi. A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani a yammacin jiya Talata, shugaba Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kakkausar murya ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Qatar, tana mai jaddada cewa, harin da aka kai kan tawagar kungiyar Hamas da ke tattaunawa da kuma janyo shahadan Falasdinawa da ‘yan Qatar, babban laifi ne da kuma keta dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta jaddada cikakken goyon bayanta ga Doha wajen tunkarar wannan ta’addanci. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, wannan harin ta’addanci na nuni da cewa, cin zarafi...
    Sabanin yadda wasu kasashe ke tayar da takaddamar cinikayya da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin duniya ta samu ci gaba, musammam kasashe masu tasowa, ta hanyar bude kofa da yin komai cikin adalci.   A duk inda aka ambaci “Babba”, to a ko da yaushe, shi ne mai nuna sanin ya kamata da tallafawa da jagorantar na kasa, domin su zamo masu dogaro da kan su da bin daidaitacciyar hanya. Wannan kuma ya yi daidai da dabaru da manufofin kasar Sin, inda take mayar da hankali kan yadda za a gudu tare a tsira tare tsakaninta da kasashe masu tasowa.   A sakonsa...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki.   “Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka....
    Cikin shekarar 2024, an kafa sabbin kamfanonin 59,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari kan na 2023. Wani rahoto da ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta fitar a wajen bikin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 dake gudana a birnin Xiamen ya ce, ainihin jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar a bara ya kai dala biliyan 116.24, lamarin da ya sa kasar ta ci gaba da rike matsayinta na mafi samun jarin waje a tsakanin kasashe masu tasowa. Haka kuma, ana ci gaba da samun ingantuwar bangarorin da ake zubawa jarin waje a kasar, inda masana’antar fasahohin zamani ta dauki kaso 34.6 na...
    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar warware tankiyar da ke tsakanin Matatar Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG). Wannan na zuwa ne bayan wani zama da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, inda rahotanni ke cewa shugabannin NUPENG sun umurci mambobinsu da su dakatar da yajin aikin da aka fara a faɗin ƙasar. ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Kwadago da Ayyuka, Mohammed Maigari Dingyadi; da Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, duk sun halarci zaman. Haka zalika, tawagar Kamfanin Dangote ƙarƙashin jagorancin...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar. An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da...
    Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai birnin Doha na kasar Qatar ya kuma bayyana cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Gaith ya yi tir da hare-haren da HKI ta kai gine-gine a Doka. Sannan kasashen Iran Saudia da Hadaddiyar daular Larabawa duk sun yi allawadai da hare-here. Gwamnatin kasar Turkiyya ta yi allawadai da...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi watsi da abinda yazo cikin bayanin bayan taro na kungiyar kasashen Larabawa na cewa tsiran Abu Musa da Tumb babba da karami mallakin UAE ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran na fada a cikin bayanin da ta fitar a safiyar yau Talata kan cewa, da wadannan kasashen sun fidda bayanai kan al-ummar gaza wadanda HKI take kissa dare da rana da yafi masu. Bayanin ya bukaci kasashen Larabawa su maida hankalinsu kan kasar Falasdinu da aka mamaye su kum yi aiki don hada kan a-ummar musulmi su tunkari HKI a kan ta’asan da take aikatawa a gaza, da sun yi abinda...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi a fadin kasar. A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 20 da fara aiwatar da shirin “malamai na musamman”, da yawa daga cikin malamai na musamman sun dukufa wajen ba da ilmi a yankunan karkara, tare da nuna kishi da jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa za su ci gaba da tabbatar da aniyarsu kan koyarwa tare da bayar da sabbin gudumawa...
    Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur. A yayin da ƙungiyar ta yi watsi da matakin, ta kuma kwatanta aiwatar da hakan a matsayin ganganci da mugunta ga tattalin arzikin ƙasar. Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayyar ta sanar da ɗaukar wannan mataki da zai fara aiki a farkon watan Janairun 2026, domin samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen gina...
    Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel, mai shekaru 45, sun ce suna zargin abokin aikinsa ne ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi a wani otel da ke Abuja. Matar marigayin ta ce alamu sun nuna an kashe mijinta ne, saboda an samu raunukan harbin bindiga a kafaɗunsa. Gini Ya Rushe A Jigawa, Mutum 1 Ya Rasu, 7 Sun Jikkata Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya Ta kuma bayyana cewa an ba su labarai daban-daban uku kan yadda aka ce mijinta ya mutu, lamarin da ya sa suke zargin ana ƙoƙarin rufe gaskiyar abin da ya faru. Kakakin rundunar ’yansandan birnin tarayya,...