HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno
Published: 15th, April 2025 GMT
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata.
Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin.
.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno Majalisar Sarakunan Arewa matsalar tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano Na Tsawon Watanni Uku
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba.
An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa.
Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda shi ne shugaban masu rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala, ya ce binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da kansiloli tara daga cikin goma na Rano suka sanya wa hannu.
A cewarsa, ƙorafin ya zargi shugaban da yin sakacin kuɗi, sayar da shaguna, da karkatar da takin zamani da aka ware wa ƙaramar hukumar, tare da wasu zarge-zarge daban.
Lawan ya bayyana cewa ko da yake shugaban ya ƙi amincewa da waɗannan zarge-zargen, ‘yan majalisar bisa ga Sashe na 128 na Kundin Tsarin Mulki da kuma Sashe na 55 (1–6) na Dokar Kananan Hukumomi ta Kano ta 2006, sun ba da shawarar a dakatar da shi na tsawon watanni uku domin gudanar da cikakken bincike.
Sauran shawarwarin sun haɗa da miƙa cikakken bayanin kuɗin shekarar 2025 na Karamar Hukumar Rano cikin gaggawa, da kuma naɗa mataimakin shugaban ya rike mukamin na wucin gadi yayin dakatarwar.
Bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin, wanda hakan ya jawo dakatar da shugaban tare da sanya ƙaramar hukumar ƙarƙashin kulawa ta wucin gadi.
Daga Khadijah Aliyu