Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC
Published: 10th, March 2025 GMT
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi.
Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal.
An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-RufaiOkocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi.
“Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha.
Tun da farko, bayan hukuncin kotun ƙolin, majalisar jihar ta ba gwamnan jihar wa’adin kwana biyu ya sake gabatar da kasafin kuɗi, gayyatar da ya ƙi amsawa.
Daga baya shi kuma gwamnan ya gayyace su gidan gwamnati domin su tattauna, inda su ma suka ce ba za su je ba, domin a kafofin sadarwa suka ga gayyatar.
Ana iya tuna cewa, majalisar ta kuma bai wa Gwamna Fubara wa’adin sallamar da sau naɗe-naɗen da ya yi wanda ba ita ta tantance su ba.
Za a sake zaɓen ƙananan hukumomin Ribas
A makon jiya ne Hukumar zaɓen Rivers ta saka 9 ga watan Agusta a matsayin ranar sake zaɓen ƙananan hukumomi.
Rahotonni sun ambato shugaban hukumar Adolphus Enebeli na sanar da hakan yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a birnin Fatakwal.
Wannan na zuwa ne bayan Kotun Ƙolin Nijeriya ta soke zaɓen da hukumar ta gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024.
A gefe guda kuma, majalisar dokokin jihar ta gayyaci shugaban hukumar ya bayyana a gabanta domin yin bayani game da zaɓen.
Wannan dambarwar na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa tsakanin gwamnan da tsohon gwamna kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke ƙara kamari.
Tun bayan ɗarewar Fubara kan mulki, dangantakar da ke tsakaninsa da magabacinsa ta yi tsami, lamarin da ya haddasa rabuwar kawuna a Majalisar Dokokin jihar.
Wasu ‘yan majalisa sun tsaya tsayin daka domin kare gwamnan, yayin da wasu ke goyon bayan APC da Wike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Siminalayi Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi
An kori direban Kamfanin Simintin Mangal bayan jami’an tsaro sun kama shi da motar kamfanin dauke da yara 21 da ake zargin an yi safarar su ne daga jihohin Arewa.
Gwamnatin jihar ta ce yaran da ke tsakanin shekaru 6 zuwa 17 an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri.
Sanawar da Kwamishinan Yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar bayan kama yaran a cikin motar ta yi zargin za a yi amfani da su wajen horar da ’yan ta’adda.
Kamfanin ya nesanta kansa daga lamarin, ya ce direban ya karya dokokin aiki, kuma ya jefa al’umma cikin haɗari.
Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashentaBabban Manajan sashin kula da mulki na kamfanin, Musa Umar, ya ce ba da izininsa direban da aka kama ya fita da motar ba, domin iya jigilar siminta kaɗai suke yi ba ɗaukar fasinja ko yara ba.
Gwamnatin Kogi ta ce za a mika yaran ga gwamnatocin jihohinsu bayan tantancewa, yayin da duk wanda aka samu da hannu a safarar zai fuskanci shari’a bisa dokokin hana safarar yara da kare haƙƙin yara.