HausaTv:
2025-12-12@04:19:50 GMT

Isra’ila ta katse wutar lantarki a zirin Gaza

Published: 10th, March 2025 GMT

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da katse wutar lantarki a Zirin Gaza.

Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ne ya sanar da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na katse wutar lantarki a zirin, a yayin da wasu rahotanni ke cewa mataki na gaba bayan katsewar wutar lantarkin, shi ne yanke ruwa a arewacin zirin Gaza.

Ya ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara kaimi ne domin kwato dukkan mutanen da ake garkuwa dasu tare da tabbatar da cewa Hamas ba za ta ci gaba da zama a Gaza ba bayan yakin.

A daya banagaren kuma Ministan kudi na Isra’ila ya yi ikirarin cewa gwamnatin kasar za ta hada kai da gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donald Trump domin sanin kasashen da za su karbi bakoncin bakin haure daga Gaza.

A baya-bayan nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da shirin tilastawa mazauna yankin Zirin Gaza zuwa kasashen Jordan da Masar da ke makwabtaka da ita.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da Sarkin Jordan Abdallah na biyu sun yi kakkausar suka ga shirin mamayar tare da jaddada cewa ba za su iya karbar sabbin ‘yan gudun hijira ba.

Jami’an kasashen Jordan da Masar da kuma wasu kasashen Larabawa sun jaddada cewa dole ne a kafa kasar Falasdinu, kuma a bar al’ummarta su zabi makomarsu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.

Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.

Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.

Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.

A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.

Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu
  • Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran
  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine
  •  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba