Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
Published: 9th, March 2025 GMT
Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara.
“Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara.
“Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.”
Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da ke aiwatar da sauye-sauye na tattalin arziki da zamantakewa tana fuskantar ƙalubale, amma ya jaddada cewa tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Tinubu sun taimaka wajen rage wahalar da ke tattare da irin waɗannan sauye-sauye.
Ya ce: “Kowace ƙasa da ta aiwatar da wani sauyi na zamantakewa da tattalin arziki tana fuskantar matsaloli a farkon tafiya, amma ina ganin cewa a Nijeriya, an rage tsawon wannan lokaci saboda hangen nesa, jajircewa, da ƙarfin gwiwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke da shi cewa wannan gyara zai kai Nijeriya ga ci gaba mai ɗorewa.”
Idris ya bayyana Faransa a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗar Nijeriya kuma ya buƙaci gwamnatin Faransa da ta mara wa shirin gyaran tattalin arzikin Tinubu baya domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Har ila yau, ya jinjina wa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, bisa girmamawar da ya yi wa Shugaban Ƙasa Tinubu ta gayyata zuwa ziyarar gwamnati a watan Nuwamba 2024, yana mai cewa irin wannan girmamawa ba kasafai ake yi wa shugabanni ita ba.
Ministan ya tabbatar wa jakaden na Faransa cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiwatar da duk yarjejeniyoyin da ta ƙulla da gwamnatin Faransa a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu.
Haka kuma, Idris ya yaba wa Jakada Fonbaustier bisa ƙoƙarin sa na inganta hulɗar Nijeriya da Faransa tun daga lokacin da aka naɗa shi.
A nasa jawabin, Jakada Fonbaustier ya ce ziyarar sa ta ƙunshi ƙirƙirar hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da Shugabannin ƙasashen biyu suka cimma a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu a Faransa a bara.
Ya bayyana ƙudirin gwamnatin Faransa na tallafa wa Nijeriya wajen inganta hanyoyin sadarwa da fasahar yaɗa labarai.
Ya ce: “Dole ne mu tabbatar da cewa an yi aiki tuƙuru don bin diddigin ziyarar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a birnin Paris a watan Nuwamba.
“Shugabannin biyu sun tsara wata sabuwar hanya mai faɗi don haɓaka dangantaka, kuma a wannan fanni, sadarwa da watsa labarai suna da matuƙar muhimmanci.
‘A nan ne Faransa za ta iya bayar da gudunmawa ta fuskar ƙwarewa da fasaha.”
Jakaden ya bayyana Minista Idris a matsayin gwarzon sauyi a fannin sadarwa a Nijeriya, yana mai cewa matsayin sa a gwamnatin Tinubu ya dace da inganta matsayin Nijeriya a idon duniya da kuma janyo hannun jari daga ‘yan kasuwar Faransa da za su hallara a Paris a ranar 10 ga Afrilu, 2025, don Taron Kasuwanci na Faransa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa Tinubu da Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda wasu ’yan majalisa suka haɗa kai suka daƙile yunkurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Sanata Kalu ya tabbatar da cewa akwai yunkuri daga wasu ’yan majalisa na tsige Akpabio daga mukaminsa, wanda bai yi nasara ba.
Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a YobeKalu wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia ne ya ce, “Kodayake an yi yunkuri, amma ba mu bari hakan ta faru ba. Shi ya sa kullum nake cewa mu ’yan gida daya ne, kuma hakan ba zai faru ba,” in ji shi.
Ya jaddada cewa Majalisar Dattawa na da hadin kai kuma tana mayar da hankali kan aikinta na doka, musamman wajen tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin fuskantar kalubalen tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.
‘Soludo zai iya komawa APC’
Dangane da ci gaban siyasa a Kudu Maso Gabas, Kalu ya nuna yiwuwar Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A yayin da yake amsa tambaya kan makomar siyasar Soludo, Kalu ya ce: “Ina ganin bayan shari’o’in da ke gabansa, Soludo mutum ne mai ra’ayin cigaba kamar ni, Shugaba Tinubu, da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kuma gwamnonin APC na Imo, Ebonyi, Enugu da sauransu. Don haka Soludo mutum ne mai ra’ayin ci gaba.”
“Ba na ganin wani abu ne da ba daidai ba idan ya shigo APC. A gaskiya, an tabbatar da cewa zai shiga jam’iyyar. Babu wani zabi da ya fi dacewa da shi face ya zo mu hada kai.”
Kalu ya kuma bayar da tabbacin cewa Shugaba Tinubu zai samu wa’adi na biyu, yana mai cewa a halin yanzu babu wata gagarumar adawa da ke kalubalantar shi.
“Shin akwai wani da ke fafatawa da shi? Zaben nan Tinubu ne da Tinubu, kamar yadda Soludo ya fafata da kansa a zaben Abia.”
“Shugaban kasa ba shi da adawa. Jam’iyyarmu tana da karfi a kasa kuma muna tare da jama’a. Babu wanda zai ce ba mu da jama’a. Za mu ci gaba da yin iya kokarinmu domin ganin talakawan Najeriya sun samu ci gaba,” in ji shi.