Oficin Jakadan Iran A MDD Ya Ce Babu Wani Sako Da Suka Karba Daga Shugaban Kasar Amurka
Published: 8th, March 2025 GMT
Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran.
Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai ta sake tattauna da Iran sabowayar yarjeniya.
Kafin haka dai jagoran ya bayyana cewa, tattaunawa da Amurka a dai dai lokacinda take takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki, ba zai yu ba, saboda daukan kaskanci ne wanda bai dace da JMI.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya jaddada goyon bayansa ga ra’ayin Jagoran dangane da tattaunawar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato
Sojoji sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da suke ƙoƙarin yi garkuwa da ayarin ’yan kasuwa a kan hanyar Tarah–Karawa da ke Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
’Yan kasuwar na kan hanyarsu daga ƙauyen Tarah zuwa kasuwar mako a Sabon Birni ne lokacin da ’yan bindiga suka kai musu hari a Kwanan Akimbo da misalin karfe 8 na safe.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin da ke sansani a Kurawa sun ji karar harbe-harbe, suka garzaya wajen, inda aka yi musayar wuta na kusan sa’a guda.
“Sojoji sun yi musu luguden wuta, daga baya ’yan bindigar suka ja da baya suka tsere zuwa maɓoyarsu a can bayan rafin.
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47“Mun ƙirga gawarwakin ’yan bindiga tara a yankinmu, sannan aka gano wasu hudu a dajin kusa da rafin. Sojoji kuma sun kwashe makamai da babura da dama suka kai Kurawa,” in ji wani mazaunin.
Ya ƙara da cewa mutane biyu ne suka samu raunuka, suna karbar magani a asibiti, amma dukkan ’yan kasuwar sun tsira ba tare da wani rauni ba. “Babu asarar rayuka a ɓangaren sojoji,” in ji shi.
Al’ummomin Kurawa da maƙwabtansu sun yi murna da nasarar da sojojin suka samu.
Ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya ce an gano gawarwakin aƙalla tara daga cikin ’yan bindigar, kuma bincike na ci gaba.
“An kwato makamai da babura da dama daga hannunsu. Ina fatan sojojinmu za su ci gaba da irin wannan aiki,” in ji shi.
Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Gatawa da Shalla da ke Sabon Birni da Isa, inda suka kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da mata da dama.