2025-09-17@23:24:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6283

«majalisar kwamishinoni»:

    Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan cibiyar gudanarwa na kungiyar Hamas dake birnin Doha na kasar Qatar dazo da rana. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijan ta 13 ta HKI na bada labarin cewa jiragen yahudawan sun kai hare-haren ne a dai-dai lokacinda shuwagabannin kungiyar Hamas suke taro don...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi...
    A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya.  Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata yarinya ’yar kimanin shekaru 10 da ke Unguwar Bedi a ƙaramar hukumar Zuru, ta faɗa mummunan...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da...
    Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel, mai shekaru 45, sun ce suna zargin abokin aikinsa ne ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi a wani otel da ke Abuja. Matar marigayin ta ce alamu sun nuna an kashe mijinta ne, saboda an samu raunukan harbin bindiga a kafaɗunsa. Gini...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da wani harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno. Mohamed Malick Fall, Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan jinkai na Majalisar a Nijeriya, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar Jumma’a, 5...
    Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa Iran ba ta neman fada da wata kasa ta musulmi ba, kuma tana ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kuma wanzar da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi. Da yake jawabi a taron kasa da kasa na hadin kan musulmi karo na 39 a birnin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai gana da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi a wannan mako domin kammala sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa. Ganawar za ta iya kawo sauyi wajen tattaunawar diflomasiyya kan batun nukiliyar Iran, da kuma da sassauta matsin lambar da kasashen Turai ke yi...
    Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel mai shekaru 45, sun ce suna zargin wani abokin aikinsa ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi. Mai ɗakin margayin ta yi iƙirarin lamarin ya faru ne a wani Otel da ke Abuja, tana mai cewa alamu sun nuna kashe mijin nata aka...
    Ya ce: “A Zamfara an kashe ‘yan ta’adda 30 a hare-haren sama da kasa, yayin da masu tada kayar baya 76 da suka hada da mata da kananan yara suka mika wuya ga jami’an tsaro.   “Rundunar ‘yansanda ta bayar da rahoton kama mutane 1,950 da ke da alaka da munanan laifuka, garkuwa da mutane,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake adduna almakashi, tabar wiwi, shisha, da sauran haramtattun abubuwan maye.   “Ana kan binciken dukkan wadanda ake tuhuma kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin aikin dabanci,” in ji Abiodun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar IAEA zai sauya saboda hare-haren da HKI ta kaiwa cibiyoyin makamashi nukliya na kasar iran a cikin watan yunin da ya gabata. Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto Baghaei yana fadar haka a yau litinin ya kuma...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
    Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110. Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara...
      Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk...
    Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin. Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta...
    “Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.  ...
    Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ke cewa za ta iya dakatar da ayyukanta na sarrafa ɗanyen mai har nan da tsawon watanni biyu zuwa uku. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote, Anthony Chiejina ya fitar, inda ya bayyana rahoton a matsayin “tsantsar ƙarya”...
    Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi. Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya...
    Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana...
    Najeriya na iya shiga cikin matsalar ƙarancin man fetur daga yau Litinin, muddin Gwamnatin Tarayya ba ta warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) ta ƙarƙashin NUPENG da kamfanin Matatar Mai ta Dangote ba. Direbobin sun sanar da shiga yajin aiki saboda shirin kamfanin Ɗangote na fitar da motoci 4,000...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar...
    Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaro kasar ya bayyana cewa: Jami’an tsaron Iran suna cikin shirin ko ta kwana Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaron kasar Admiral Habibullah Sayyari ya jaddada cewa: Dakarun kasar da suka hada da sojoji da dakarun kare juyin juya halin...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye...
    Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli. Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori....
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna. Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal Tsadar Rayuwa:...
    Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar...
    Wani Jirgin Drone wanda ake sarrafashi daga nisa, ya fada kan zauren fisinjoji a tashar jiragen sama na Ramon dake yankin Araya na kudancin haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan harin ya nuna irin yadda sojojin Yemen suke fadada hare-harensu a kan HKI, da kuma tabbatar mata da...
    Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma...
    Bictor Boniface Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe. Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu. Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake...
    Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo...
    Alamomin Basir Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura? Alamomin Basir Cikin Dubura: 1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno. 2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa....
    Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin...
    Sojojin runduna ta 6 da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, sun gano wata mafakar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da dama a ƙauyen Ikyaior da ke ƙaramar hukumar Wukari, a kan iyakar Taraba da Benuwai. Bayanan sirri da sojojin suka samu ne suka taimaka musu wajen kai farmakin da ya kai ga gano...
    A jawabin da ya yi wa shugabannin sashen sintiri, jami’an ‘yansandan motoci, da sauran jami’an da ke aiki a hedikwatar rundunar, CP ya ce halayen jami’an sintiri a fili suke bayyana hoton da al’umma ke da shi game da rundunar ‘yansanda. Adeh ta bayyana cewa CP ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’ai ke...
    Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124. Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa...
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa yana ƙaryata Shugaba Bola Tinubu. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da Hukumar DSS ɗin ta aike wa kamfanin X Corp mallakin fitaccen attajirin nan...
    Hajiya Sa’ah ta kuma bayyana cewa ita wannan ƙidaya da yin rajistar haihuwa, aure da sauran su, abubuwa ne masu muhimmanci da za su taimaka wa gwamnati ta san yawan su, ta yadda za su sami nasarar ci gaba da lasar romon Dimokraɗiyya mai yawa, musamman a bangaren ilmi, lafiya da dai sauran abubuwan more...
    ’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin...
    A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara...
    Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya...
    Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa. A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai. Ta...
    Ƙungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta buƙaci kwamitin shirya bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan da ya soke ranar Juma’a, 26 ga Satumba, da aka shirya gudanar da bikin. Ƙungiyar ta ce wannan rana za ta iya hana ɗaruruwan Musulmi gudanar da Sallar Juma’a da suke yi a kowane...
    Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke...