2025-09-24@17:20:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3862
«Katsina Ba Ƙorafi»:
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa....
Kasashen Pakistan da Iran suna shirin fadada dangantakar tattalin arzikin da ke tsakanin daga dalar Amurka biliyon $3 a ko wace shekara zuwa dalar Amurka billion $10. plan to expand bilateral trade from its current level of just over $3 billion to an ambitious $10 billion. Tashar talabijan ta Presstv a nan ta nakalto bangarorin...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kasar Agfanistan ta mayarwa kasar Amurka san sanin sojojin sama na kasar wanda ke Bagram ko kuma zata ga ba dadi. Kafanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka da farko a shafinsa na zumunta na ‘ Truth Social’. Shugaban ya gargadi Taliban...
Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin bayan karewar man fetur ne, inda fasahohi da ilmi da kirkire-kirkire da kuma darussan da za’a dauko daga kasashe kawayen kasar a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ne zasu zama abin dogaru. Tashar talabijan ta Presstv...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na...
Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba,...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
A cewar Atiku, wannan kalmomi (ƙabilanci da yanki) an tanade su ne don raba kan jama’a da nufin cimma burinsu na siyasa ta hanyar roƙon ’yan ƙabilarsu da kada su zaɓi wani ɗan takara wanda ya fito daga wata ƙabila’ maimakon tantance shi da kyawawan halayensa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan...
Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su...
Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa. A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Asabar wacce ta kunshi wannan bayanin ta kuma ce; Sojojin mamaya suna ci gaba da rusa sauran cibiyoyin kiwon...
A wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar a jiya Asabar ya ce; Abinda ya faru a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki na farko da na biyu, mayar da martanin Iran ya haifar da sakamako mai karfi wanda aiki ne na tsawon lokaci. Haka nan kuma sanarwar ta...
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar...
Gwamnatin yahudwan sahuniya ta kaddamar da hari da makami mai linzami kan wata motar hawa a layin Nabatiya- marjiyun dake khardali a kudancin labanon a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da buda wuta da aka cimma tun 27 ga watan nuwamba na shekara ta 2024. Wannan hari wani bangare ne na kata yarjejeniyar da...
Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya...
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce matsayin Sin dangane da batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma tana jaddada aniyar gwamnatin kasar na martaba hakkokin kamfanoni yadda ya makata. Ma’aikatar ta ce Sin na maraba da matakin gudanar da shawarwari da kamfanoni bisa doron dokokin kasuwa, ta yadda za a iya kaiwa ga shawo...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai...
A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran,...
Iran ta yi gargadin cewa za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyarta da hukuar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, muddin ake sake dawo mata takunkuman MDD. Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya ce Tehran za ta dakatar da hadin gwiwar da take yi da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bayan da...

Spain za ta hada kai da kotun ICC domin gudanar da bincike kan laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza
Tsarin shari’a na kasar Spain zai hada kai da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da kotun duniya domin binciken laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.” Wannan yunkurin “ya mayar da martani ga shawarar rahoton kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya mai zaman kansa (IOC) kan yankin Falasɗinawa da aka...
Bayanai daga Falasdinu na nuni da cewa akalla Falasdinawa 47 ne sukayi shahada a ranar Asabar din nan a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da jiragen yaki a Gaza yayin da sojojin suka sabunta bukata ga mazauna birnin da su fice daga birnin su koma kudu. A wani labarin kuma harin da Isra’ila...
Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar...
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata,...
Kididdigar da aka fitar akan adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da kuma jikkata sun haura 230,000,wanda ya faro tun daga watan oktoba 2023. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Juma’a, sannan kuma ta bayyana cewa an kara samin wani adadi mai yawa na shahidai a cikin...
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine...
An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci. Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara. Ya ce...
Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da...
Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo. “Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta yarda da duk wani aiki na siyasa ko matsin lamba na rashin adalci ba Rafael Grossi, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Iran tana da ‘yancin mayar da martani ga duk wani mataki da ya sabawa doka Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dangane da haramtaccen matakin da kungiyar Tarayyar Turai Troika ta dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya mayar da martani kan zargin shugaban Faransa Emmanuel Macron Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya musanta zargin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a...
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli...
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona...
A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan...
Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi...
Rahotanni sun bayyana cewa tankunan yakin HKI na ci gaba da kutsa kai a tsakiyar gaza a yau juma’a, lamarin da ya jawo tsananta kai hare-hare ta kasa da tilastawa dubban mutane barin muhallinsu sakamakon yankewar hanyoyin sadarwa, A gefe daya kuma Amurka a karo na 6 ta hau kujerar naki kan kudurin kwamitin sulhu...
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin...
Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa, ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila. Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa kan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato ya ce akasarin masu kai hare-hare suna fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da Filato. Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya bayyana cewa sun gana da kabilu daban-daban da kungiyoyin...
Sojojin HKI 12 ne suka halaka ko suka ji rauni wani harin da dakarun hamas suka kai masu a zirin gaza. A dai-dai lokacinda suke kai mummunan hare- hare kan Falasdinawa don nufin mamayar birnin Gaza. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar labarain na yahudawan na fadar haka takumakara da cewa sojojinsu...