2025-11-03@02:53:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 119

«Jihar Kwara»:

    Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya. Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.” A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa:  Nageria kasa ce ta Demokradiyya,...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u    Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi. A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati. A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi. Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025 Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  October 30, 2025 Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025
    Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
    An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu. Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka da Marco Rubio da Sergey Lavrov a shekaran jiya inda su ka cimma matsaya akan cewa, ganawar ba ta zama dole ba. A makon da ya shude ne dai shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin su ka yi ttataunawa ta wayar tarho, inda su ka cimma matsaya akan ganawa a birnin Budaphast na kasar Bulgaria. A cikin watan Ogusta na wannan shekarar an...
    Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa.   Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka gudanar a birnin Ilorin.   A cewarsa, Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kwara tana daga cikin ma’aikatun da ke ba da muhimmanci ga hidima ga jama’a, wadda ke da alhakin gurfanar da masu laifi a kotu, kare gwamnati, tsara da tantance takardun doka, da kuma ba da shawarar doka ga sauran ma’aikatun gwamnati.   Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki ta hannun sassa guda shida (directorates)...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya. Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori. A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi. Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan...
    Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Iraki a birnin Tehran Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya karbi bakwancin mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji. A yau litinin ne mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, ya iso birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda yake jagorantar wata babbar tawaga ta tsaro. Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji, inda suka tattauna batutuwa da dama musamman kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da muhimman mu’amalar da ke tsakaninsu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify...
    Ma’aikatar raya matasa ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar Masu Ruwa da Tsaki don horar da matasa kan amfani da fasahar AI don ganin sun kasance masu amfani da dogaro da kai, da kuma samun fasaha.   Da yake jawabi a lokacin da tawagar ta ziyarci ma’aikatar a Ilorin, kwamishinan ci gaban matasa na jihar, Ndanusa Shehu, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kuma ya kawo sauyi.   A cewarsa Artificial Intelligence wata hanya ce ta tsara makomar aiki a duniya tare da jaddada mahimmancin ganin matasa sun iya amfani da irin wannan kirkirarriyar fasaha.   Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da nuna kyakykyawan manufa na karfafa matasa, tun daga samar da damammaki a...
    Rundunar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da aikin ceto har sai duk waɗanda aka sace sun kuɓuta kuma an dawo da zaman lafiya a jihar. Mohammed Gana Alhaji, wanda ya yi magana a madadin al’ummar Patigi, ya gode wa sojojin bisa ƙoƙarinsu na yaƙi da rashin tsaro da kuma kare al’ummar yankin. A ranar 23 ga watan Satumba, 2025, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari wasu ƙauyuka na Patigi, inda suka kashe wata mata mai juna biyu a ƙauyen Matokun, suka yi wa wasu rauni, sannan suka sace mutum takwas. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima October 15, 2025 Manyan Labarai Kotu A Kano Ta Tsare Wani...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025
    Shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi ya yi kira ga takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame ya kawo karshen taimakon da kasarsa take bai wa kungiyar M23. Shuagab Tshisekedi ya bayyana hakan ne dai a wurin taron kasa da kasa dangane da zaman lafiya da aka bude a birnin Brussel na kasar Belgium, da shi ma takwaransa na na Rwanda Paul Kagame yana zaune a wurin. Tsheisekedi wanda yake tsaye yana Magana ya juya da kansa ya kalli Paul Kagame sannan ya ce: ” Ga shugaban Rwanda nan ina gani, kuma da shi nake yin Magana. Ina yin magiya da mu kawo karshen gaba. Ya kamata mu kawo karshen wannan rikicin.” Haka nan kuma ya  ci gaba da yin Magana kai...
    Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara.     Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da  cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin.   Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun.   Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
    Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar Kwara ta yi watsi da zargin cewa mambobinta na boye makamai a cikin shanunsu domin gujewa jami’an tsaro.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Shehu Garba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Ilorin.   Ya ce Hausa Fulani da Bororo a jihar su ne masu bin doka da oda kuma ba su da wani laifi a kan haka.   Shugaban na MACBAN ya yi zargin cewa mayar da tsohon Sarkin Fulanin Igangan da ke Oyo, Alhaji Saliu Abdulkadir zuwa jihar Kwara a shekarar 2021, da kuma sauran makiyayan da suka yi tashe-tashen hankula ne suka haddasa matsalar tsaro...
    Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara. Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa. A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba. Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji. Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman.   A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su.   “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sama da al’ummomi 100 a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu ayyukan raya kasa don kyautata rayuwa ga mazauna.   Shugaban zartarwa na karamar hukumar Ifelodun, Alhaji Abdulrasheed Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ayyukan gwamnatinsa a cikin shekara daya da ta gabata, yayin da ya ke gabatar da wani shirin Newskeg of the Correspondents’ Chapel na NUJ, majalisar jihar Kwara, wanda aka gudanar a Ilorin.   Ya lissafta ayyuka da dama da aka kammala, wadanda suka hada da gine-gine da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Oke-Ode, Labaka Oja, Adanla, Ofarese, Ijaya-Share, da Ajapa, da samar da kayan aikin likita da samar da muhimman magunguna a fadin cibiyoyin...
    Sanarwar ta ce, wadannan hare-haren sun sake tabbatar da aniyar NAF na kare jami’an tsaro da fararen hula, da kuma ci gaba da matsin lamba kan masu tada kayar baya.   Ya kara da cewa, duk hare-haren an kammala su cikin nasara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Kwara ta jaddada kudirinta na sake gyarawa da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a matakin farko.   Sakatariyar zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWPHCDA), Farfesa Nusirat Elelu, ta bayyana hakan a lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) da masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Oke-Ero da kuma shugaban ma’aikatar lafiya a Ilorin.   Ta lura cewa gwamnatin na ci gaba da nuna himma wajen samar da kiwon lafiya mafi dacewa ga kowane dan kasa, musamman a yankunan karkarar da ba a yi musu hidima ba.   Farfesa Elelu ya bayyana cewa, jihar ta bayar da makudan kudade wajen farfado da fannin kiwon...
      Ta kuma tabbatar da yin garkuwa da mutane shida a yankunan biyu, inda ta kara da cewa wasu shida sun samu raunuka a harbin bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama. Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025) Shaidu sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a babura, inda suka dinga harbi ba ƙaƙƙautawa wanda ya sa mazauna ƙauyukan suka gudu. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Motokun, Egboro da Fanagun. Wani mai suna James Ibrahim, ya ce: “Mun farka da safe muka ga mutane suna gudu daga Motokun bayan harin. An harbi wata mace wadda daga bisani ta rasu a asibitin Patigi....
    Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar. Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa duk da ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro. Rufe kasuwannin dabbobi Sanarwar farko ta fito daga Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi bakwai na Kwara ta Kudu, inda suka bayar da umarnin rufe duk kasuwannin Kara a yankin. Shugabannin —Abdulrasheed Yusuf (Ifelodun), Benjamin Jolayemi (Isin), Azeez Yakub (Irepodun), Awelewa Gabriel (Ekiti), James Fadipe (Oke-Ero), Sulyman Olatunji (Offa), da Akanbi Olarewaju (Oyun)— sun ce matakin ya zama dole don...
      Ya ce Morocco, ta sha alwashin zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da fadada musaya a fannoni irinsu yawon bude ido, da ilimi, da al’adu, da ci gaba da yayata kawance bisa matsayin koli tsakanin kasashen biyu. A daya bangaren kuma, Morocco na maraba, da kuma goyon bayan shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin.   Sanarwar ta ce shirin rufe kasuwannin Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi ba tare da sanin sarakunan gargajiya da shugabanni da masu gudanar da aiki ba, bai dace ba.   Ya bayyana cewa kafin daukar irin wadannan shawarwarin da shugaban karamar hukumar ya yi ya kamata a yi shawarwari da yawa don tafiyar da...
    A yau Juma’a shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF). A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa. Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu. A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar. Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
    Ministan harokokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Masar da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi a karon farko tun bayan yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka kaiwa Iran a cikin watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, Aragchi ya kai ziyarar aiki na kwana guda birnin Alkahira a yau Talata ce don tattauna batun shirin Nukliyar kasar Iran da shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi a birnin Al-Khahira. Labarin ya kara da cewa ministan ya ce Iran ta amince ta bude sabon shafi a huldarta da hukumar IAEA bisa wani sabon tsari wanda a cikin iran zata tabbatar da amincin shirinta...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaran aikinsa na kasar masar badar albadelatty ta wayar tarho inda suka tattauna game da batutuwan da suka shafi yankin da kuma irin ci gaban da aka samu, kuma sun mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi Gaza da kuma shirin nukiliyar Iran na zaman  lafiya. Iran dai na neman isar da sakon diflomasiyya ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakaninta da kasashen yammacin duniya dangane da shirinta na nukiliya. A halin da ake ciki, Masar ta dauki  kanta a matsayin babbar mai shiga tsakani a rikicin Gaza, inda ta daidaita alakar ta da kasashen Larabawa da ke makwabtaka da...
    Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran ya tattauna da takwaransa na Birtaniyya kan tattaunawar nukiliya da hanyoyin kawar da sabani tsakanin Iran da tawagar Turai Mai bai wa fira ministan kasar Birtaniya shawara kan harkokin tsaro, Jonathan Powell, ya tattauna kan farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma warware hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen rikicin a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da Ali Larijani, babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran. Bangarorin biyu sun tattauna batun sake farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma neman hanyoyin da za a bi don magance matsalar makamashin nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa. A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho da aka gudanar a yammacin yau Alhamis, bangarorin biyu...
    Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed mai ritaya, ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce; jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.   Haka zalika, mazauna Ndanaku da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, sun kauracewa wurin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga. Kazilika, harin na zuwa ne makwanni kadan bayan faruwar makamancin haka a garin Babanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun.   Kwamandan ‘yan banga, Gina Gana; wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa; an kai hare-hare guda biyu ne kwanaki uku da suka gabata, wanda ya tayar wa da kowa hankali a garin.   Har wa yau, a makon day a gabata ne Gwamna...
    Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar  a Ilori babban birnin Jihar Kwara. Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan. Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya....
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar bayanan sirri daga majiyoyin tsaron al’umma, sun dauki wami mataki kan wani harin fashi da makami da ya afku a wani dakin kwanan dalibai da ke unguwar Eleko, Ilorin. Sanarwar ta ce ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga, sun kai ga kama wasu maza biyu da ake zargi.   Ta ce wadanda ake zargin sun hada da Ishola Adeyemi,...
    Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi.   A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.   A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai daruruwa, a kan babura, sun mamaye al’ummar Babanla a karamar hukumar Ifelodun.   A cewarsa wadanda ake zargin sun kai hari ne a hedikwatar ‘yan sanda inda suka kai farmaki cikin kasuwar.   Ya bayyana cewa maharan sun yi ta harbe-harbe kai-tsaye, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda...
    Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas  Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
    Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa.   A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana.   A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci.   Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma,...
    Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara. An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin haɗin gwiwar karamar hukumar Ifelodun da shirin Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES). Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi wanda Honarabul Ganiyu Afolabi, dan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Omupo ya wakilta,  ya jaddada muhimmancin wannan shiri wajen magance matsalolin da manoman karkara ke fuskanta. Ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai rage rikici ba...
    Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar. ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore A yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta. Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari.   Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar Edu.   Ya kuma shawarce su da su yi taka tsantsan wajen gudanar da ayyuka daban-daban na kwas din.   Gwamna AbdulRazaq ya tabbatar wa ‘yan yiwa kasa hidimar cewa gwamnatin jihar za ta samar da yanayin da zai taimaka musu su ci gaba.   A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jihar, Mista Onifade Joshua, ya yabawa gwamna AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake baiwa...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kori mabarata 94 daga titunan Ilorin, domin tantancewa, gurfanar da su da kuma mayar da su gida.   Da take magana da ‘yan jarida yayin aikin, kwamishiniyar jin dadin jama’a da ci gaban jihar Dr Mariam Nnafatima Imam ta ce wadanda aka kama domin dawo da su sun hada da mata 43 da maza 51.   Ta ce ma’aikatar ta yi aikin dawo da mabaratan domin an haramta barace-barace a jihar Kwara.   Imam ya godewa gwamnan jihar bisa kokarin da yake yi na ganin jihar ta kawar da barace-barace a kan tituna da sauran matsalolin zamantakewa .   Kwamishinan ta ce a ko da yaushe gwamnatin jihar tana tuntubar gwamnatocin jihohin masu bara a tituna...
    An yi kira ga manoma a jihar Kwara da su yi taka tsan-tsan domin hasashen za a samu ruwan sama da kuma tsawa da ake hasashen nan da kwanaki masu zuwa.   A wata sanarwa da kwamishinan noma da raya karkara na jihar, Dr, Afees Abolore ya fitar, ya ce a cewar hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ana sa ran wasu sassa na jihar za su fuskanci ruwan sama da kuma yiwuwar tsawa.   Ya ce za a fuskanci ruwan sama ne da rana da yamma, tsakanin Litinin 28 ga Yuli da Laraba 30 ga Yuli, 2025.   Ya yi bayanin cewa duk da cewa ba a sami ruwan sama ba tukuna, yanayin da ke gaba zai iya...
    A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama. Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.   Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.   A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar.   AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin.   Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin.   Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu.   Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
    A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 65, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. A cikin sakonsa Wang Yi ya bayyana cewa, cikin shekaru 65, an raya dangantaka tsakanin Sin da Ghana yadda ya kamata, kana an karfafa imani da juna kan harkokin siyasa, tare da samun manyan nasarori a hadin gwiwarsu ta fannoni daban daban. Kazalika, sassan biyu sun goyi bayan juna a fannin kulawa da harkokin kasa da kasa. Wang Yi ya ce, ana fatan yin kokari tare da minista Ablakwa, wajen kara fadada mu’ammala a tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu, da goyon bayan juna,...
    Aƙalla jami’an tsaro shida ne suka rasu bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a yankin Gada Woro a kan hanyar Patigi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a Jihar Kwara. Waɗanda suka rasu sun haɗa da ’yan banga guda biyar da ɗan sanda ɗaya. ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’ Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a Sakkwato Wasu sojoji biyu, ’yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a fafatawar da ta faru a ranar Litinin. Waɗanda suka rasu sun haɗa da Mohammed Nma Dsuru daga Kokodo, Yanda daga Lafiagi, da Ndagi Saraka daga Edogi. Rahotanni sun ce ’yan bindigar da yawansu ya kai ɗaruruwa sun kai wa tawagar jami’an...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Neja da Kwara sun shaida wa majalisar cewa mutum 600 da suka bace a ambaliyar garin Mokwa kuma har yanzu ba a gan su ba, za a dauka su ma sun mutu. Dan majalisa Joshua Audu Gana (Neja) da Saba Ahmed Umaru (Kwara) ne suka bayyana hakan a yayin gabatar da wani kudurin gaggawa a zauren majalisar a ranar Laraba. Sun ce mummunar ambaliyar da aka yi a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun da ya gabata sanadin mamakon ruwan saman da aka tafka ta yi barna sosai a karamar hukumar ta Mokwa a jihar Neja, sannan ta tsallaka har karamar hukumar Edu ta jihar Kwara. Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
    Da safiyar yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Koriya ta kudu Lee Jae-myung ta wayar tarho. Da farko, Xi Jinping ya sake taya Mista Lee murnar lashe babban zaben shugaban kasa. Sa’an nan, ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Koriya ta Kudu su tsaya tsayin daka kan burin tallafawa juna da cimma moriyar juna, tare da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon matsayi, domin ba da karin tallafi ga al’ummun Sin da Koriya ta Kudu, da samar da tabbaci cikin yankin da ma kasashen duniya baki daya, inda ake fuskanar da sauye-sauye da tashe-tashen hankula. A nasa bangare kuma, shugaba Lee Jae-myung ya ce, yana mai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Myanmar Min Aung Hlaing, sun mikawa juna sakon murnar cika shekaru 75, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 75 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar, bangarorin biyu sun bi ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, da kuma tunanin Bandung, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma kasance abun koyi a fannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da Myanmar, don gaggauta raya hadin gwiwa mai...
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiyan ya zanta ta wayar tarko tare da shugaban kasar Masar abdulfatta Assisi, inda suka taya juna murnar tahowar sallar Babba. Shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tana da tsari ta makobta farko, don haka ne take, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma musamman kasar ta Masar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wata wayar tarho ta daban shugaban ya zanta da Yarima mai jiran gadon sarautan saudiya kuma Firay ministan kasar Muhammad bin Salman inda ya taya shi murnar zagayowar ranar Sallah babba sannan suka yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Duk tare da bambancin ra’ayin da kasashen biyu suke da shi dangane da yadda za’a warware...
    Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Belarus Aleksandr Lukashenko a nan birnin Beijing. Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya sake taya takwaran nasa na Belarus Aleksandr Lukashenko murnar nasarar yin tazarce. Xi ya ce, Sin na daukar huldar sassan biyu da muhimmanci, kuma tana raya ta bisa hangen nesa kan manyan tsare-tsare, tare da fatan kara hadin gwiwa da Belarus, don gaggauta bunkasa huldarsu, da ma cimma moriya tare cikin hadin gwiwa. Ya kara da cewa, dole ne kasashen biyu su kara hadin kai, da marawa juna baya karkashin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD da SCO da sauransu, don taka rawarsu tare wajen dakile babakere, da kiyaye...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta cafke wasu gungun masu satar motoci tare da dawo da wata mota da aka sace. A cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP Ramhan Nansel ya fitar, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin wannan aika-aika, a kan hanyar Doma zuwa Lafia, bisa sahihan bayanan sirri. Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa kai wajen satar mota da bindiga a Jihar Enugu, inda suka kwace wata mota kirar Toyota Venza mai launin baki da karfin bindiga. Sanarwar ta bayyana cewa, saboda saurin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar jihohi ba tare...
    Idan ajiyewa za ki yi sai ki samu roba mai murfi, ki rufe sosai saboda kada ta yi kwari. Yadda za ki tuka: Sai ki dora ruwa a wuta, ya tafasa ki dauko garin doyar, ki rage wuta kina zubawa da kadan-kadan kina tukawa har ya tuku, ki tabbatar bai yi kulalai ba duk kin tuke shi, sai ki dan zuba ruwa kadan ki daddanna ki rufe ki barshi ya yi kamar minti 15, sai ki sauke ki sake tukawa, ki samu leda ki kwashe abinki, shi kenan kin kammala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Sahun ƙarshe na mahajjata 140 daga jihar Kwara, ciki har da jami’an NAHCON, da ya tashi daga filin jirgin sama na Babatunde Idiagbon da ke Ilori ya isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Yayin jawabi ga mahajjatan kafin tashin su da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin Laraba, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmud-Jimba, ya shawarci mahajjatan da su kasance masu ɗabi’a a lokacin da suke kasa mai tsarki. Farfesa Mahmud-Jimba ya bayyana cewa an shirya duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa mahajjatan sun gudanar da aikin hajji ba tare da wata matsala ba. Ya kuma shawarce su da kada su yi ayyuka masu wahala domin samun damar shiryawa...
    Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu.   Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken “Hatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu” wanda Michael Imoudu tare da hadin gwiwar mamba mai wakiltar mazabar Edu/Moro/Patigi na Jihar Kwara, Ahmad Adamu -Saba ya shirya, ya ce za a yi rabon ne kashi biyu.   Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Muhammed Salihu, ya ce manufar shirin bayar da tallafin shi ne tallafawa daliban da iyayensu ba za su iya biyan wasu kudadensu a makaranta ba.  ...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan kasa, tafiya tare da buri a matsayin al’umma”.   Da yake jawabi a wani takaitaccen biki a Ilorin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar ba ta daga tuta kawai ba, a’a tana nuna kwarin guiwar wata alama ce ta hadin kai, alfahari, da kuma kishin kasa.   Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan sadarwa na jihar Bola Olukoju, wanda wasu kwamishinoni uku suka taimaka masa: Aliyu Kora Sabi (sufuri); Nafisat Buge (Muhalli); da Nnafatima Imam (ci gaban al’umma) da sauran manyan baki.   A cewarsa, sandar tuta na kara karfafa martabar jihar a matsayin cibiyar kirkire-kirkire, al’adu, da jagoranci mai ma’ana....
    Shugaban karamar hukumar Kaiama, Honarabul Abdullah Danladi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da LEADERSHIP ta wayar tarho.   Danladi ya ce ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.   Ya kara da cewa, gwamnati za ta kafa wani kwamiti wanda za a dora masa alhakin tilasta wa fasinjojin jirgin ruwa yin amfani da rigar tsira don dole.   Danladi ya ce gwamnati za ta kuma dakatar da tafiye-tafiye da daddare a wani bangare na matakan kawo karshen yawaitar haduran Kwale-kwale da ake fama da shi a yankunan da ke zagaye da ruwa.   Shi ma mai martaba Sarkin Kaiama, Alh Muazu Omar ya nuna alhininsa kan wannan lamari da ya...
    Wani hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 37 a ƙauyen Gbajibo-Mudi da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Hatsarin wanda ake fargabar ya auku ne a sanadiyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata. Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi Lamarin na zuwa ne watanni bakwai bayan aukuwar makamancinsa wanda ya janyo asarar fiye da mutum 106 a jihar. A cewar wani mazaunin yankin, kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji kimanin 150 ya kife ne a tsakiyar ruwa. Bayanai sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su na komawa gida ne bayan cin kasuwa a tsallake...
    Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya.   Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki.   Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya.   An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin...
    Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta kammala shirye-shiryen kaddamar da wani shiri na sana’ar kiwon dabbobi da ya maida hankali kan matasa, wanda aka tsara domin horarwa da samar da kayan aiki da kuma samar da kudade ga masu son noma a fadin jihar.   Kwamishiniyar Raya Dabbobi ta jihar, Misis Oloruntoyosi Thomas ta bayyana haka a lokacin da ta ziyarci sansanin wayar da kan matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, karamar hukumar Edu ta jihar.   Ta ce shirin wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Jihar ke yi na mayar da jihar ta zama wata matattarar kirkire-kirkire da kuma dabbobi.   Kwamishinan ya bayyana cewa, ma’aikatar ta hada kai da hukumar NYSC domin samar...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.   Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.   A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC).   Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon...
    Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare. Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine. Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa ​​a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya. Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya. Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da...
    Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan,  sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi. A wani bangare Aragchi ya fadawa...
    Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.   A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye...
    Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya.   Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin.   A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba.   Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa...
    Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200.   “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.”   Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya,...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.   Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu.   Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba.   Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya. Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji. A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Ƴan fashi sun sace fasinjoji guda bakwai a cikin motocin haya biyu a ƙauyen Eleyin da ke cikin ƙaramar hukumar Isin a Jihar Kwara. A cewar rahoton LEADERSHIP, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yamma a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da wasu ƴan fashi su biyar suka toshe hanya, suka tsayar da motoci biyu, sannan suka tilasta ɗaukar dukkanin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna  Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, daga cikin fasinjojin motar ɗaya, akwai shugaban sashin shari’a na ƙaramar hukumar Oke Ero, Barr. Elizabeth Arinde,...
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.   A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.   Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.  ...
    An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin. Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20 Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15. An mayar da Misa gidan yarin, yayin da ake...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana. Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir  ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori. Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai  cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai  ta Jihar  daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025. Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.   Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki.   Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda.   Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin daukar matakin hadin gwiwa da kasashen yankin domin gaggauta dakatar da laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da kuma tsagaita bude wuta a zirin Gaza, lamarin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen warware wasu rikice-rikice a yankin yammacin Asiya. Jami’an biyu sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, sakamakon ci gaba da kai...
    Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa.   Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB) ta shirya, kwamishinan ilimi da ci gaban bil’adama na jihar, Dokta Lawal Olohungbebe ya ce shirin na daya daga cikin manyan dabarun da jihar ta bullo da shi na bunkasa harkar ilimi domin ya dace da ka’idojin karni na 21.   Ya kuma bukaci malaman da su ci gaba da jajircewa...
    Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka  fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
    A wani labarin makamancin wannan, kimanin kananan masu kiwo 100 ne a Jihar Kwara, suka amfana da tallafin kiwon Awaki na kashin farko. Wannan tallafi, na daga cikin dabarun gwamnatin jihar na son kara bunkasa fannin da kuma samar da kudaden shiga ga masu kiwon, domin samun riba. A jawabinta a garin Ilorin, wajen kaddamar da kashin rabon Awakin, kashi na farko; wato a karkashin shirin jin kan iyali na L-PRES, Kwamishin Bunkasa Kiwo, Oloruntoyosi Thomas ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin ne, suka bayar da tallafin Awakin Thomas ya sanar da cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da shirin L-PRES a jihar ta Kwara. Ta sanar da cewa, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ba...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
    Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci. A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
    Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi mazauna jihar kan yin gine-gine a kan bututun ruwa a fadin jihar.   Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Usman Yunusa Lade, ya yi wannan gargadin a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban bututun ruwa dake Flower Garden, a Ilorin.   Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Sakatariyar Dindindin, Misis Christiana Asonibare, ta ce “kamar gine-gine, masallatai, coci-coci da shaguna a kan bututun ruwa da jama’a ke yi yana da illa ga samar da isasshen ruwa a fadin jihar.”   Yunusa -Lade ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar yin la’akari da bututun ruwa kafin a gina wani gini domin kaucewa lalata bututun ruwa da...
    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga Owena Ijesha a karamar hukumar Oriade ta jihar Osun, daurin sa’o’i 300 (dari uku) da yiwa al’ummar hidima na tsawon sa’o’i biyar a kowace rana ba tare da zabin biyan tara ba, bayan da ya same shi da laifin aikata laifukan da suka shafi yanar gizo wato walawala ko yahoo boyi. Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC...
    An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa.   Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin.   A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa.   Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
    Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.   A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13.   A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.   Sanarwar ta bayyana cewa...
    A yau Talata ce ake saran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump, kuma wannan shine zantawar shuwagabannin kasashen biyu tun shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kakakin Fadar Krimlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen zantawar shuwagabnnin biyu. Peskov ya kara da cewa tattaunawar tasu zai maida hankali ne kan yakin Ukraine da matsalolin da suke kewaye da yakin. Yau ita ce ranar da kasar Rasha ta hade yankin Cremear ga kasar Rasha, a shekara ta 2014. Kwace yankin dai ya jawo matsaloli da dama tsakanin Amurka da Rasha a lokacin.