2025-11-03@08:41:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 119
«Jihar Kwara»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma. Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi. Guguwar ruwan sama ta yi barna a kwalejin Ansar Deen da ke Ijagbo yayin da ajujuwa sama da 10 suka yi lalace, inda dalibai da malamai suka makale. An gano cewa guguwar ta afku ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Litinin, tare da yaga rufin ajujuwan tare da lalata muhimman kayan koyo da kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi. Da suke Magana game da wannan...
Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom. Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu. A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa. Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe. A makon da ya gabata, jaridar ta ce ta kara samun wani matsayi na musamman a bikin na bana, wanda kuma ke bikin cika shekaru 20 da kafa kamfanin, ta hanyar baje kolin abin da ke tafe a jaridar Financial Times, babbar jaridar kasuwanci da hada-hadar kudi ta duniya. Gangamin wanda aka fara a makon farko na watan Fabrairu, zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Maris, wanda...
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu. Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar. A cewarsa...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin horas da makarantun firamare da kananan makarantun gwamnati 50 a fadin jihar domin su iya amfani da fasahar ziyyana shafin internet. Da yake gabatar da shirin a madadin Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a Makarantar Sakandare ta Bishop’s Smith Junior Ilorin, babban mai ba gwamna shawara na musamman, Alhaji Sa’adu Salau, ya ce shirin na dijital ya kasance don ƙarfafa fannin ilimi. A cewarsa shirin ya shafi sama da dalibai 150 a kowace makarantu 50 na gwamnati a matakin gwaji. Ya ce idan aka kafa harsashin tsarin zamani, yaran jihar Kwara ba za su koma baya a tsakanin takwarorinsu na duniya ba.” Gwamna AbdulRazaq yace sauran makarantun gwamnati da za su...
Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke. Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu. Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu, tare da tona asirin ɓata-garin cikinsu ga jami’an tsaro kafin miyagun su kai ga aikata munanan ayyukansu ko halaka jama’a.” Ya yi wannan kira ne bayan kisan gillar da wani mai iƙirarin malumta mai suna Abdurrahman Bello, ya yi wa wata ɗaliba ’yar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ake Ilori, mai suna Hafsah Lawal. A cikin sanarwar da basaraken ya...
Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar. Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a hedikwatar Hukumar da ke Ilorin. Ta ce matakin zai hada da inganta ababen more rayuwa, samar da lantarki ta amafani da hasken rana, da samar da wuraren zama na ma’aikata, da samar da ruwan sha da samar da kayan aikin asibiti na zamani a duk wuraren da ke amfana da cibiyoyin kiwon lafiya na farko. Farfesa Elelu ya bayyana cewa shiga tsakani na...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Akalla manoma da ma’aikatan gona 1,000 ne gwamnatin jihar Kwara ta horas da su akan aikin gona da sarrafa ragowar amfanin gona don inganta amfanin gonakin da makiyaya ke amfani da su. Da yake jawabi a karshen horon, a Ilorin, wanda Synergy Impact Limited ya shirya, tare da tallafin gwamnatin tarayya, bankin duniya da kuma shirin gwamnatin jihar Kwara akan kiyo da noma (L-PRES) kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi ya bayyana cewa shirin yana da karfin inganta ayyukan noma a jihar. Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin noma na majalisar, Issa Gideon, ya bayyana cewa shirin ya kara wa dimbin matasa kwarin gwiwa da jami’an noma da manoma wajen samar da kananan manaoma da...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun da Ilesha-Baruba, inda aka buƙace su biya kuɗin fansa har Naira miliyan tara. Yadda Ficewar Kwararrun Ma’aikata Daga Nijeriya Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasa Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara Bincike ya kai ga cafke Umar Sanni daga jihar Neja da Dairu Isiaku daga Ifelodun, da kuma Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi, waɗanda suka amsa laifin yin barazana da...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun da Ilesha-Baruba, inda aka buƙace su biya kuɗin fansa har Naira miliyan tara. Yadda Ficewar Kwararrun Ma’aikata Daga Nijeriya Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasa Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara Bincike ya kai ga cafke Umar Sanni daga jihar Neja da Dairu Isiaku daga Ifelodun, da kuma Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi, waɗanda suka amsa laifin yin barazana da...
A yau ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar kashu kai, inda daga nan zai wuce Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a birnin Addis Ababa, shugaba Tinubu zai bi sahun shugabannin Afirka a zaman taron majalisar zartarwa karo na 46 da kuma zaman taro na 38 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, wanda aka shirya daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabarairun 2025. Shugaban zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa don halartar taron kungiyar ta AU. Yayin da yake...
An kuma samu labarin cewa ɗalibin ya rasa mahaifinsa a wasu shekarun baya, lamarin da ya mahaifiyarsa wadda tsohuwar malamar makaranta ce ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsa tun daga lokacin. Rahotanni sun nuna cewa matsalarsa ta ƙara tsananta tun bayan dawowarsa makaranta a bara, inda abokan karatunsa suka tara kuɗi domin biya masa kuɗin makaranta da kuma siya masa kayan abinci. Duk da cewa jami’ar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma wani babban jami’i a makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, yana mai bayyana hakan a matsayin abin mamaki da ya jefa jami’ar cikin jimami.
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar, ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar. A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike. Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma. Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba...
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa. Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin. A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa. Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje. Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...
