HausaTv:
2025-11-06@16:27:21 GMT

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Da Tokwaransa Na Kasar Kuwait

Published: 15th, April 2025 GMT

A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.

Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba, amma da alamun kasashen biyu suna fatan kawo karshen tattaunawar da fahintar juna da kuma cimma yarjeniya mai amfanar bangarorin biyu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

 

An bude bikin CIIE na bana a ranar 5 ga watan Nuwamban da muke ciki, kuma za a ci gaba da gudanar da shi, har zuwa ranar 10 ga wata, inda aka samu kamfanoni 4108 na kasashen ketare da suke baje kolin kayayyakinsu. Duk a wannan biki, kasashe 17 na nahiyar Afirka sun kafa rumfunan baje kolin kayayyakinsu, kuma adadin kamfanoni masu baje kolin kaya daga nahiyar Afirka ya karu da kashi 80% , bisa adadin na shekarar bara.

 

Me ya sa bikin CIIE ke jan hankalin kamfanonin kasashen Afirka? Domin babbar kasuwar kasar Sin, da ta kunshi mutane biliyan 1.4, ta ba da damar sayar da karin kayayyaki, tare da samun riba mai tsoka. Misali, tun bayan da busasshen tattasan Ruwanda ya shiga kasuwannin kasar Sin, bisa damar bikin CIIE na shekarar 2021, noman tattasai ya riga ya zame wa ‘yan kasar wata muhimmiyar sana’a mai alaka da fitar da kayayyaki zuwa ketare, wadda ta ba dubun dubatar manoman kasar damar wadatar da kai. Bugu da kari, a bikin CIIE na shekarar 2024, wasu kayayyakin Afirka irin su zuman Zambia, da furanni na Kenya, da abarba na kasar Benin, su ma sun fara samun karbuwa tsakanin al’ummun kasar Sin.

 

Hassan Mohammed, jami’i mai kula da aikin kasuwanci a karamin ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Shanghai na Sin, ya ce a bikin CIIE da ya gudana a bara, kamfanoni 13 daga cikin 16 na Najeriya sun yi nasarar kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da abokan huldar kasar Sin, ciki har da wata kwangilar samar da tsabar koko, wadda kudinta ya kai sama da dalar Amurka miliyan 1.2. Bugu da kari, yazawa (kashu ko cashew) na Najeriya, da ba a san shi ba a baya a kasar Sin, yanzu yana kara samun karbuwa a kasar, duk albarkacin bikin CIIE.

 

Hausawa kan ce “Da abokin daka ake shan gari”. To, duk wadannan abubuwan da suka faru a bikin CIIE sun tabbatar da gaskiyar maganar. Ma iya cewa bikin ya nuna babbar ka’idar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato samar da damammaki da amfanar da juna.

 

Sai dai, idan wani ya saba da neman sanin abubuwa game da kasar Sin ta hanyar rahotannin da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke bayarwa ko wallafawa, ba makawa zai cika da shakku da damuwa game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Saboda tunanin da Turawa ‘yan kasashen yamma suka saba da shi, ya shafi neman cin moriya da faduwar wani, da tattare samuwar dimbin albarkatu a hannun mutane kalilan, duk da cewa sauran mutane da yawa za su yi fama da talauci da yunwa.

 

Watakila wannan tunani nasu ya hana su fahimtar yanayin huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka na amfanin juna, da sanya su neman shafa kashin kaza ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Amma kamar yadda ake cewa “Gani Ya Kori Ji”, yadda kasar Sin ke kokarin taimakon kasashen Afirka wajen neman ci gaban tattalin arziki, zai rufe bakin gulmace-gulmacen masu yada jita-jita. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 4, 2025 Ra'ayi Riga Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 4, 2025 Ra'ayi Riga A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya? November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho
  • Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
  • Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
  • Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Ta yi Kan Shirin Nukuliyarta
  • Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar
  • Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin