2025-10-15@16:27:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10214

«a gudanar da bincike»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Wasan Kalankuwa A Nijeriya, 1977 A gwamnatance a wannan kasa, an fara shirya manyan bukukuwan nuna fasahohinmu da aladunmu na-dauri, cikin Shekarar 1977 a Legas. Wanda aka fara gudanar da taron, daga 15 ga Watan Janairu, zuwa 12 ga Watan Farairun Shekarar 1977. A farkon lamari, an niyyaci ci gaba da shirya bikin na baje-kolin al’ada ne a duk Shekara, da niyyar samar da hadin-kai a tsakanin jama’ar Kasa bakidaya. Da farko an kira bikin ne da FESTAC ’77, daga baya aka koma kiransa da NAFEST (National Festibal of Arts and Culture). Saboda muhimmancin irin wadannan bukukuwa, lokacin da aka fara shirya shi a wannan kasa, an sami mahalarta taron ne daga mabanbantan kasashe har kimanin hamsin da biyar (55)....
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
    Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan. A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama. Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Filato, ta sha alwashin ba da misali da masu yanke hukunci da kansu ba tare da barin doka ta yi aikin ta ba.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, CP Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Jos yayin da suka kama wasu manyan mutane tara (9) da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da wasu laifuka daban-daban.   Ku tuna cewa a wasu lokutan a cikin watan Agustan wannan shekara ta 2025, an kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a karamar hukumar Bassa sakamakon aikata irin wannan danyen aiki.   An bayyana cewa dan sandan ya tafi...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kaddamar da wasu sabbin motocin alfarma masu kujeru 18 guda 50, domin inganta ayyukan zirga-zirgar jama’a na jihar.   Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya bayyana ci gaban a matsayin wani sabon babi a tarihin sufuri na Zamfara.     A cewar Gwamnan, motocin bas din suna da kayan kariya na zamani da na jin dadi, wadanda suka hada da na’urorin sanyaya waje da sauran kayyakin jin dadin matafiya.   Dokta Lawal ya bayyana cewa, da gangan aka samu jinkirin tura motocin bas din bayan isowarsu, inda ya ce gwamnati ta fara samar da tsare-tsare na sa ido da kuma bin diddigi don...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.   Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.   A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.   Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan.     Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ofishin Kano, ta gudanar da wani taron kara wa masu yi wa kasa hidima na NYSC aiki a karkashin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (EMVs).   An zabo mahalarta taron ne daga kungiyoyin ci gaban al’umma (CDS) a kananan hukumomin Tarauni da Dawakin Kudu Kano.   An tsara horon don ƙarfafa ilimin membobin ƙungiyar a matsayin wakilai na gaba na rage haɗarin bala’i da amincin al’umma.   Da yake jawabi a lokacin bada horon, shugaban ayyuka na hukumar NEMA Kano reshen jihar Jigawa, Dakta Nura Abdullahi, ya bukaci jami’an tsaro da su ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da koyo.   Mahalarta taron sun nuna haɗin kai mai ƙarfi a duk...
    Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar.   Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.   Ya ce an boye magungunan ne a cikin fakiti 35 na Polyglycine da kuma allunan Tramadol 28.     Yayin da yake mika haramtattun magungunan ga wakilin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, Konturola Dalhatu Abubakar, ya ce abubuwan na da illa ga lafiya da suka hada da lalata gabobi, jaraba, da rashin natsuwa, musamman a tsakanin matasa.   Abubakar yayi gargadi game da illolin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Muna tabbatar da inganta tsarin na PCS domin a kara tabbatar da karfafa gasa a fadin diniya a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na NPA wanda hakan zai kuma kara samar da damar janyo masu zuba hannun jari daga waje na kai tsaye da kuma kara karfafa tattalin arzikin kasar, a nan gaba,”. A cewarsa, za mu ci gaba da kulla hadaka domin mu cimma burin da aka sanya a gaba, na kara inganta ayyukan Hukumar ta NPA. Ya ci gaba da cewa, a rabin zangon farko na shekarar 2025, ingancin da aka samar a bangarorin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar sun bayar da gudunmawar da ta karu, zuwa kaso 19.6 a fannin fitar da kaya waje, da ba su shafi...
    Ƴan ƙasar Congo sun fara mayar da martani kan hukuncin kisa da Babbar Kotun Sojin Ƙasar ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ranar Talata a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa. Joseph Kabila mai shekaru 54, ya mulki jamhuriyar Demokradiyar Congo tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019 lokacin da ya mika mulki ga shugaba Felix Tshisekedi da ya gaje shi. Baya nan cikin kotu, lokacin yanke hukucin a ranar 30 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki, saboda yana can makwabciyarsu Rwanda inda yake zaman gudun hijirar siyasa shekaru biyu da suka gabata. Yayinda magoya bayan shugaba Tshisekedi ke yabawa matakin, wasu masana siyasa da ƴan adawa na kira da a yi taka-tsan-tsan. Jam’iyyar PPRD...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala. Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya tsakanin gwamnati da jama’a, kuma tana bawa shugaban kasa dama gane ma idonsa irin kalubalen da ake fuskanta da kuma bada umarnin kawar da duk wani abu da ka iya kawo cikas wajen ayyukan raya kasa. Gwamnatin iran ta mayar da hankali wajen karfafa damammaki a bangaren ilimi da ci gaban tattalin Arziki a jihohi daban daban, ziyarar lardin Hormuzgan wani bangare ne na babban...
    Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta fadi cewa akalla sama da falasdinawa 66225  ne suka rasa rayukansu, yayin da 168938 kuma suka jikkata a aci gaba da kiran kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza tun daga watan oktoban shekarar bara da ta gabata. Akalla fararen hula 77 ne ake kaashewa 222 kuma suke jikkata a duk rana sakamakon hare hare da sojojin Isra’ila ke kawai kan fararen hula marasa karia a yankin Gaza. Fararen hula da dama ne ciki har da mata da yara kanana suka dimauce bayan da HKI ta harba hayaki mai sa hawaye da kuma bomb na hayaki da jirgi mara matuki na HKI ya kai a makarantu da gidaje domin tarwatsa alumma dake...
    Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran tayi  Allah wadai da da irin bayanan da kungiyar G7 ta yi game da shirin nukiliyarta, kuma ta bayyana shi a matsayin munafunci da kuma canza gaskiya , Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il baghae ya fadi cewa kungiyar G7 ta amince da matakin da ya sabama doka da rashin Adalaci da Amurka da kasashen turai 3 suka dauka na sake dawo da takunkumi kwamitin tsaro na majaliar dinkin duniya kan kasar iran, matakin da ya sabama dokar kasa da kasa. Haka zalika ya soki kungiyar ta G7 na yi gum da baki kan shirin nukiliya Isra’ila ,yace kasashen ba su da hurumin da za su iya yin lecture kan dokokin kasa da kasa...
    Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla  ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza. Haka zalika shugaban kasar Bolivia da takwaransa na kasar Cuba  suna yi Allah wadai da Isra’ila , haka su ma ministocin harkokin wajen spaniya jose manueal dana kasar irish simon harris sun bayyana damuwarsu matuka game da halin da tawagar ta flotilla ke ciki a hannun Israi’la na kokarin hana su isa yankin gaza. Ita dai tawagar Sumud Flotilla tana dauke...
    Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
    Lamidon Akko da ke jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya nada Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu, sarautar Sarauniyar Yaki a masarautar. Basaraken dai ya karrama uwargidan shugaban ƙasar ce a ranar Alhamis a wani biki na musamman da ya gudana a fadarsa. An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku A cewar basaraken, ya ba ta sarautar ce domin yabawa da gudummawar da take bayarwa wajen kare marasa ƙarfi tare da tallafawa mata da yara a fadin ƙasar nan A yayin ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar Gombe, Remi Tinubu ta kuma ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative Flow With Confidence, wani muhimmin shiri na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto.   A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto mai kyau na fasfo ko na bikin aure ko bikin suna, ko kuma kowane irin taron biki. Amma yanzu, manhajojin AI suna ba wa mutane damar kirkirar irin wadannan hotuna daga wayoyin su ko kwamfuta cikin mintuna kadan ba tare da zuwa shagon daukar hoto ba. Wannan yanayi na iya jefa...
    Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin yau. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya.   Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.   “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
    Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.” Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki  Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata. Yayin da yake jawabi a bikin da...
    A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya. Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake...
    A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.   Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya musanta cewa yana son ya janyewa wani takara saboda matashin ɗan takara kafin zaɓen 2027. A baya dai tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban Ƙasa a 2027. An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Atiku dai ya fice daga Jam’iyyar PDP bayan ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen da ya gabata. A watan Agusta, Atiku Abubakar da wasu ’yan siyasa na adawa da suka haɗa da: tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi da dai sauransu, sun koma jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi...
    Gwamnatin Rasha ta jaddada cewa: Yarjejeniyar dabarun da kulla da Iran dole ne a aiwatar da ita Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a yau Alhamis a cikin wata sanarwa cewa: Yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara aiki, tare da tabbatar da cewa kasashen biyu bisa tsarin yarjejeniyar suna fuskantar kalubale da barazana amma ba zasu yi wani tasiri ba. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar ta bayyana cewa: A ranar 2 ga watan Oktoba ne yarjajjeniyar huldar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Iran Masoud Peskov suka sanya wa hannu a ranar 17 ga watan Janairun shekara...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da aikata sabbin kura-kurai tare da jaddada cewa duk wani hari da za a kai wa Iran zai fuskanci martani mai tsauri fiye da martanin Alkawarin Gaskiya na baya. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki matakin soji da na siyasa bai daya dangane da tunkarar barazanar da take fuskanta da kuma matakin da ya biyo bayan sake maido da takunkumin da kare kan kasarta, a daidai...
    Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa da yake hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da cewa, da sanyin safiyar ranar Larabar nan, sun kai hari kan jirgin (MINERVAGRACHT) da makami mai linzami a mashigin tekun Aden. Sanarwar da Rundunar Sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Sojojin ruwan kasar sun kai wani samame na soji kan jirgin Ruwan na (MINERVAGRACHT) saboda kamfanin ya keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye. Sanarwar ta bayyana cewa an kai harin ne a mashigin tekun Aden tare da wani makami mai linzami, wanda ya yi sanadin harbo jirgin kai tsaye tare da kama jirgin. Yanzu yana cikin...
    Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza. Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.” Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”. Lazzarini ya kara da cewa...
    Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya kan kogin Nilu. Wannan dai ya zo ne a wata ganawa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan suka yi a birnin Port Sudan, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar. Abdel Aty ya ce ziyararsa ta uku zuwa Port Sudan cikin shekara guda sako ne na nuna goyon baya...
    Jami’ar Tianjin wadda aka kafa a shekarar 1895 a matsayin jami’ar Peiyang, ita ce jami’ar zamani ta farko ta kasar Sin kuma ta yi na’am tare da amsa sunanta na yanzu ne a shekarar 1951. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani da ‘Akuskura.’ Ko wanne buhu na dauke da kwalabe 350, adadinsu ya kai kwalabe 2,450, wanda kudinsu ya kai ₦2,450,000.   SP Kiyawa ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro, “Rundunar ta mika wadanda aka cafken da kayayyakin su da darajarsu ta kai N120,000,000 ga hukumar NDLEA, ta jihar Kano, domin ci gaba da bincike.” Hakazalika, jami’an rundunar sun kama wasu fitattun...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana matukar bayyana takaicinta da kuma nadama a kan matakin da kasar Amurka ta dauka a baya, kan daftarin kudirin kwamitin sulhun MDD da aka tsara da nufin magance matsalar jin kai a zirin Gaza. A jawabin da ya yi kan amfani da hawan kujerar na ki a wajen muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Fu ya ce, kasashen duniya sun dade suna yin gagarumin kira na tsagaita bude wuta da dakatar da yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da haddasa masifar tabarbarewar jin kai, inda hakan ke dakushe lamiri da tausayin bil’adama da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis,  jami’an ’yan sanda da ke aiki da sashen bayanan sirri sun kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Franklin Ozo a Zariya. Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa An kama shi da ƙunshin ƙwayoyin Exol guda 500, na miliyoyin Naira. “Bincike na farko ya nuna cewa,...
    Ganau sun ƙara da cewa a lokacin da aka shaida wa matar cewa Yelwa ba ta nan, sai ta koma mashigar gidan ta kwarara wa kanta man fetur tare cinna ashana wanda hakan ya janyo wuta ta tashi.   Nan take lamarin ya janyo hankalin mutanen da suke kusa da wurin inda suka yi ƙoƙarin kashe wutar amma lamarin ya ƙazanta.   Daga baya kuma aka kwasheta zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda daga bisani ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi.   An kuma ce marigayiyar ɗiyar tsohon wani alkalin kotun Shari’a a Bauchi ce, wacce ta taɓa yin aure har da ‘ya’ya.   Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil a ranar Alhamis...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
    Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
    Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
    Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka kai wa jirgin ruwan Global Sumud Flotilla a cikin ruwan kasa da kasa. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na fashin teku da ta’addanci kan fararen hula”, tana mai kira ga “dukkan masu kare ‘yanci a duniya” da su yi Allah wadai da harin. Kungiyar Jihadin Islamic ta Falasdinu...
    Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23. An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar. An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa  rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo. Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan...
    Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya. Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke birnin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu da dama, wasu ma sun makalle a karkashin baraguzan gine-gine. Wasu mutane 11 kuma sun yi shahada, sannan wasu da dama sun jikkata a harin bam din da aka kai a makarantar Al-Falah da ke unguwar Al-Zeitoun a kudu maso gabashin wannan birni. Makarantar tana dauke da iyalai da suka yi gudun hijira. A...
    Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba. Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi. Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji,...
    Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60 a birnin Geneva, wakilin kasar Iran Ali Bahreini ya yi ishara da rahoton da kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan yankin Falasdinu da ta mamaye a watan Satumba, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukumar, wacce ke binciken abubuwan da suka faru tun ranar 7 ga Oktoba 2023, ta gano...
    Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraq. Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar safarar...
    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza. Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu. Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa. Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra’ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta’addanci. An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra’ila a yankin
    Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda ya ce “lokacin alkawura marasa amfani ya wuce, wannan sanarwa kuwa ita ce alkawarinmu ga mutanen Arewa.” Ya yi gargadi kan karuwar ta’addanci da ‘yan bindiga, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya danganta da gazawar shugabanci da kuma rashin wakilci nagari. A cewarsa, kungiyar ba ta da manufar ballewa daga kasa, amma akwai gaggawar bukatar sabuwar...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar...
    Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.   A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM).   Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar.   A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata.   “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.   A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa.   Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su.  ...
    An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.   Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa.   Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna.   Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai.   Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa.   Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman.   A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su.   “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata.   Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya.   Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
    Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja.   Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu.   Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa.   Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
    Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma  don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar  da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da  ministocin  Turai, amma wakilin Amurka Steve Witkoff ya ki isa a lokacin da aka tsara. Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ta kuma bayyana cewa, kasarta na ci gaba da musayar sakwanni kai tsaye da kuma a fakaice, kuma tana ci gaba da kokarinta, sai dai kuma gwamnatocin  yammacin duniya su ne ke warware alkawuran da suke dauka. A nasa bangaren, sakataren majalisar kula da harkokin tsaron kasar,...
    Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya. Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki? Wannan shine batun...
    Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen Ruwan, sannan kuma suka killace su. Baya ga haka kuma sun kama dukkanin mutanen da suke cikin wasu jiragen sun tafi da su. Sanarwar ta ce, kyamarorin da ke cikin jirgin sun samu matsala, sannan sojojin Isra’ila sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka umurci jiragen da su karkata zuwa tashar jiragen ruwa ta Asdod da ke karkashin ikon su. Rahotanni sun tabbatar da...
    Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus. Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin  dawo da takunkumai a...
    Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan Indomie, domin mu kafa tarihi.” A wajen Collins, fentin fuska ba nishaɗi ba ne kaɗai ba, fasaha ce da ke bayyana fikira da ƙirƙira. Ƙoƙarinsa ya haskaka wa duniya irin baiwar da matasa ’yan Nijeriya suke da ita a idon duniya. Kamfanin Indomie, ya jima yana bayar da gudummawa da goyon baya a fannin ƙirƙira da ilimi a tsakanin matasa, kamfanin ya bayyana farincikinsa da...
    Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza. A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana  wadanda abin ya shafa...
    A wannan Laraba ce wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu madugun ‘yan adawa Julius Malema da laifin harba bindiga a bainar jama’a a shekarar 2018, hukuncin da zai iya sa a hana shi shiga majalisar. Malema ya harba bindiga sama a lokacin bikin cikar shkaru biyar da kafa jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF)  a lardin Eastern Cape, wanda ya saba wa dokar hana sarrafa bindigogi. Idan har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari, Malema, wanda ya shafe sama da shekaru 10 yana dan majalisa, za a dakatar da shi  daga ci gaba da zama mamba a majalisar dokoki a karkashin kundin tsarin mulkin kasa. A rahoton kamfanin dillancin labaran Reuters Mai shari’a Twant Olivier ta ce, kwanaki...
    Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
    Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan. Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin...
    Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.” Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki. A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya...
    Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur. Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba.   An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
    Fitaccen masanin karatu da ƙira’ar Al-Qur’ani kuma babban malamin nan da ke karantarwa a Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba. Shafin Al-Haramain ya ruwaito cewa Sheikh Bashir ya rasu ne bayan shafe kusan shekaru sittin yana koyar da Al-Qur’ani a Al-Masjid An-Nabawi da ke birnin Madinah. Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Sheikh Bashir da aka haifa a shekarar 1358 Hijiriyya, wanda shi ne mafi shahara a cikin sahun bajiman malaman ƙira’a, ya rasu bayan shafe kusan shekaru 90 a doron ƙasa. Fitattu daga cikin malamansa akwai Qari Fath Muhammad Panipati, da Sheikh...
    A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai,  hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa  iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza. A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan harin 7 ga watan oktoba da isra’ila ta kaddamar a yankin gaza, inda ta kai hari kan yan jarida 30 daga watan mayu na 204 zuwa Augustan shekara ta 2025 ta kashe 25 daga ciki ta jikkata wasu gida biyar kuma. Darakatan sadarwa na kungiyar ta RSF Antoine bernard ya bayyana cewa isra’ila a koda yaushe tana kokari ne wajen rufe bakin yan jarida, Yace...
    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi,  wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani,  makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
    Cibiyar nazarin fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, an samu bunkasa sosai a fannin kere-keren fasahar kirkirarriyar basira (AI) ta kasar Sin, inda yawan kamfanonin bangaren ya zarce 5,300 a watan Satumba, wanda ya kai kashi 15 cikin 100 na dukkan adadin na duniya baki daya. Mizanin kudin masana’antar ya zarce yuan biliyan 900 (kimanin dalar Amurka biliyan 126.7) a shekarar 2024, inda aka samu karuwarsa da kashi 24 cikin dari a ma’aunin shekara-shekara. Bangaren fasahar AI na kasar ya kafa cikakken tsarin masana’antu wanda ya kunshi tun daga kan kayayyakin aiki da ake bukata, zuwa fasalin abubuwan da za a aiwatar, da kuma manhajojin aikace-aikacen masana’antu. Cibiyar ta kara da cewa, kayayyakin manhajoji na zahiri da ake...
    Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.   Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
    Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai  maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
    Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
    Jakadan Iran na dindin a majalisar dinkin duniya yayi kira da a gaggauta kakabawa HKI takunkumi saboda hujjoji da ake da shi dake tabbatar da cewa tana kisan gillan ne kan alumma Gaza, kuma yayi tir da matsayin kasashen turai game da abin da ke faruwa a yankin gaza. A baya bayan nan kwamitin bincike mai zaman kansa ta majalisar dinkin duniya ya fitar da sakamakon bincike da ya tabbatar da irin kisan  gillan da HKI ke yi kan alummar falasdinu ,a gefe guda kuma kasar iran shugabar yan gwagwarmaya tana goyon bayan alummar falasdinu, Tun bayan harin 7 ga watan oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta kai hari kan HKI  mutane da dama sun nuna kin jinin gwamnatin sahyuniya...
    Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da ci gaban da ƙasar ta samu a ƙarƙashin mulkin ƴan ƙasa da kuma ƙalubalen da take fuskanta. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar ƙasar ke rayuwa a cikin mawuyacin hali, sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa waɗanda suka biyo bayan sauye-sauyen da gwamnatocin da suka gabata da kuma mai ci suka ƙaddamar da zummar sake fasalin tafiyar da ƙasar. A irin wannan rana a shekarar 1960, aka rantsar da Dr. Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban ƙasa, tare da Sir Abubakar Tafawa Balewa a matsayin Firaminista, shugabannin da suka yanke...
    A jiya 30 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya mika sakon taya murna ga Safi Kharib bisa zama sabon firaministan kasar Algeria. Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Algeria sun sada zumunta mai zurfi da juna. A cikin shekaru 67 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, an raya dangantakarsu yadda ya kamata, da yin kokari tare da nuna goyon baya ga juna. A watan Yuli na shekarar 2023, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya kai ziyara a kasar Sin cikin nasara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaba Tebboune, batun da ya samar da taswirar raya dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. Sin ta maida hankali sosai kan raya dangantakar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A cewar Wike, ana sa ran kamfanin CCECC zai kammala aikin gabanin kaddamar da fara amfani da titin nan da watan Yunin shekarar 2026. Tsarin aikin ya kunshi komai da komai, ba kawai shimfida titin ba har ma da gada mai ginshikai guda hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba. Rikicin ya samo asali ne bayan...
    Bello, ta kuma bayar da umarnin ƙara tsaro a duk faɗin ƙasar na , musamman a tashoshin mota, hanyoyin ruwa a jihohin da ke bakin teku, da kuma filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa. Samamen ya biyo bayan bayanan sirri daga masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa, waɗanda suka sanar da hukumar cewa akwai mutane da ake shirin safararsu a filin jirgin Abuja. Bayan kusan sa’o’i 6 da aka gudanar ana bincike, an kama mutane biyar da ake zargi, sannan an ceto mutane 24 da aka so yin safarar su. Adekoye ya ce waɗanda aka ceto, masu shekaru tsakanin 15 zuwa 26 ne, kuma an ɗauko su daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas. An shirya kai...
    “Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima.   Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba. Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya. Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu. Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe...