2025-11-22@07:22:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1207
«da kasar Rasha»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba. An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya. Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.” Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa; Manyan jami’an diplomasiyyar kasashen uku na turai sun yi wani taron sirri a birnin Moscow, inda su ka gargadi Rasha akan keta hurumin samaniyar kasashen mambobi,suna masu cewa za su iya kai wa jiragen Rashan hari. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” din ya ambato jami’an kasashen na turai da su ka halarci taron suna nakalto wannan gargadin, bisa cewa cikin ganganci ne jiragen na Rasha su...
Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja. Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata. Sakamakon kuri’ar raba gardamar da ak ayi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin. Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cea kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a. Jam’iyyun hamayyar kasar ta...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta. Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar, Husseini Babayayi. Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma. “Wurin ba shi da tsafta, kuma yana shafar lafiyar al’ummarmu. Gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuwar al’ummarmu a Akwanga saboda yanayin wurin bai dace ba da yankan dabbobi,” in ji ta. Ta ce idan ba a gyara ba nan da wata guda, to gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen rufe mahautar gaba...
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Rashin Amincewa Da Duk Wani Takunkumi Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku,...
Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya. Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban. “Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki. Kwamishinan...
Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, an kuma ci gaba da aikin ceto na fito da mutanen har zuwa jiya juma’a. Wani mazaunin yankin ya ce, an ceto da mutane 13 daga karkashin baraguzai, ana kuma jin cewa da akwai wasu mutane fiye da 100 da suke karkashin kasa. Wani shaidar ganin ido kuwa cewa ya yi, a tsakanin mutanen da sun kai 100 da...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
Kasashen China da Rasha sun yi kira da a jinkirta mayar da takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kasashen China da Rasha sun bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya kada kuri’a kan tsawaita lokacin sake kakaba takunkumi kan Iran zuwa tsawon watanni shida nan gaba a yau Juma’a. Kasashen China da Rasha sun gabatar da wani daftarin kudiri na hadin gwiwa da ke neman tsawaita dage takunkumin har zuwa ranar 18 ga Afrilun shekara ta 2026. Kasashen China da Rasha sun tabbatar da “ci gaba da hadin gwiwa” tsakanin kasar Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, inda suka yi kira ga bangarorin da ke cikin shirin hadin gwiwa na JCPOA da su gaggauta dawo...
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a bangaren na TTP tun lokacin da aka faro sun hada da, sanya ido kan sama da manyan motocin miliyan uku da ke shiga cikin Tashoshin musamman bisa nufin rage cunkoson da kuma sake fitarsu, daga cikin Tashoshin a kan lokaci Ya sanar da cewa, kirkiro da tsarin biyan kudade kan lokaci na shigar motocin cikin Tashoshin hakan ya taimaka matuka, wanda kuma bisa hadakar da...
Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ƴansandan Jihar Delta ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da wani matashi, inda suka karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan biyu (₦2m) amma duk da haka suka harbe shi saboda rashin isassun kuɗi a asusun bankinsa. Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka (25), da Uche Okechukwu da Somto Chukwuma, waɗanda suka yi garkuwa da wanda abin ya shafa daga gidansa da ke Ogwashi-Uku. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana cewa an gano wanda aka sace a cikin daji da ke yankin tare da raunin harbin bindiga a ƙafarsa. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da...
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga. Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya. Sanarwar ta ruwaito shugaban majalisar na cewa rasuwar tsohon sanata mai wakiltar nasarawa ta arewa, mutuwa ce da ta girgiza al’ummar jihar Egu da ma jihar baki daya ba. “Bishiyar Iroko ta fado, mai taimakon jama’a kuma fitaccen dan siyasa ya je gida ya huta, Allah ya kara masa yarda.” Inji Shugaban Majalisar. Kakakin Majalisar Danladi Jatau ya bayyana...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata. Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Mutane Sun Yaba Da Gina “Tsarin Xinjiang” A Turbar Zamanantarwar Kasar Sin
Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa...
Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine. Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar kasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki. Peskov ya tabbatar wa manema labarai cewa babban kuskure ne a yadda ake cewa Ukraine za ta iya yin nasara wajen karbe ikon yankunanta da ke hannun Rasha. Bayan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a New York, Trump ya ce Ukraine na iya kwato dukkan yankunan da ta rasa, inda ya bayyana Rasha a matsayin kyanwar Lami. Ya kuma ce tattalin arzikin Rasha na cikin gagarumar matsala. Tun da farko...
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar ne wadanda suka hada da kananan yara 3 da mahaifinsu da kuma sannan mahaifiyarsu ta ji Rauni mai tsanani, da kuma yar’uwassu wacce itama ta ji Rauni. Almanar ta nakalto cewa shahadar da kuma kissan kiyashin bai karawa mutanen garin ba sai karfin giwa na riko da kasarsu da kuma gwagwarmayansu. Ministan kiwon lafiya Rakan Nasiruddeen tare da rakiyar minister watsa labarai Paul mahaifiyar yaran...
A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia. Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar...
Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin inganta ilimi da kuma bai wa matasa damar samun kyakkyawar makoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...
Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF. A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar. Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu. “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye. “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne, bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar ilimin ya ƙara jan kunne na da akwai buƙatar tabbatar da cewaana amfani da shi tsarin dokar kamar yadda aka bayyna “a kuma samu dama ta wayar da kan duk masu ruwa da tsaki kan lamarin” a duk illahirin faɗin tarayyar Nijeriya”saboda kar abin ya kawo cikas na jarabawar da ta shafi ƴ aƴ an al’umma.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine din. A kudancin ƙasar ma, hukumomi a Mykolaiv sun bayar da rahoton tashin gobara bayan harin da aka kai kan wasu masana’antu. Yankunan yammacin Lviv da Ivano-Frankivsk ma sun fuskanci gobara sakamakon hare-haren da aka kai masu. Suna kusa da iyakar Poland, inda sojoji suka ce sun tura jiragen sama domin tabbatar da tsaron sararin samaniyar yankin.
Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, tun farkon yaƙinta da wungiyar Hamas a shekarar 2023. Sun haɗa da: Kashe ’yan ƙungiyar, wanda ya janyo musu lahani a jiki da ƙwaƙwalwa; da kuma ƙirƙirar wani yanayi da gangan don lalata ƙungiyar, da hana haihuwa. Rahoton ya ba da misali da kalaman shugabannin Isra’ila, da kuma abubuwan da sojojinta suka yi a Gaza, a matsayin shaida na aikata kisan ƙare dangi. Ma’aikatar...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta yarda da duk wani aiki na siyasa ko matsin lamba na rashin adalci ba Rafael Grossi, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, a yayin wannan kiran, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, da batun maido da takunkuman da aka kakabawa Iran, da kuma matakin ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a kwamitin sulhu na MDD. Araqchi da Grossi sun cimma yarjejeniya a birnin Alkahira kan sabbin hanyoyin hadin gwiwa...
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York. Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne na cikakken shirin zaman lafiya da ke tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga Isra’ila da Falasdinu. Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi don tabbatar da wannan karramawa a ranar litinin da misalin karfe 3:00 na rana a birnin New York (9:00 na yamma agogon Paris), yayin wani taron da zai jagoranta tare da yarima mai jiran gado na Saudiyya. Fadar...
Ya ce ma’aikatar ta tsaya a kan tabbatar da ladabi da bin doka don haka babu wani shugaban makaranta da za a bari yana sabawa doka ko karbar kudade a hannun dalibai da iyaye ba tare da an hukunta shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su. Domin sauke shirin, latsa nan
Rundunar Brigade ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina ta raba buhunan takin zamani ga manoma a ƙauyuka shida da ke kusa da sansanin Natsinta, cikin Jibia da Katsina. Kwamandan brigade ɗin, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya ce an yi hakan ne don ƙarfafa dangantakar sojoji da al’umma, tare da taimaka musu wajen noma, lafiya da ilimi. Ya kuma nemi haɗin kan jama’a wajen bayar da bayanai da sintiri domin tabbatar da tsaro a jihar. A madadin al’umma, shugaban ƙauyen Katoge, Malam Abubakar Bala, ya gode wa sojojin, inda ya bayyana cewa takin zai taimaka wajen bunkasa noma, kuma sun dade suna amfana da tsaro da taimakon sojoji a yankin. Kauyukan da suka amfana da rabon takin sun hada...
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihar Kaduna ranar Juma’a 19 ga watan Satumban 2025. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai halarci daurin auren Nasirudeen Yari, ɗa ga Sanata Abdul’aziz Yari, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma, da Amaryarsa Shehu Idris. A yayin wannan ziyara, shugaba Tinubu zai kuma ziyarci Hajia Aisha, matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansu da ke Kaduna. Ana sa ran shugaban zai koma Abuja a ranar, nan take bayan kammala ziyarar. Daga Bello Wakili
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare. Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda. Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar...
Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak. Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki tsawon sa’o’i biyar, inda bangaren Syria ya gabatar da martaninsa kan shawarar da Isra’ila ta gabatar na cimma yarjejeniyar tsaro, inda ta ce an samu ci gaba a tattaunawar. A baya dai bangarorin biyu sun gana a zagaye na biyu da aka sanar, ban da kuma tarukan sirri da suka gudanar a lokuta daban-daban wand aba a sanar ba, da nufin kulla alaka ta siyasa...
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ya yammacin Afirka. Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna. Sai...
Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin leken asiri da kuma harkokin tsaro da kuma musayar bayanai da jami’an Mossad. An zartar da hukuncin kisar ta hanyar rataya a safiyar yau bayan kammala matakan shari’a kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin. Babak Shahbazi, dan Rahmatullah, ya yi aiki a matsayin dan kwangilar kere-kere da sanya kayan masana’antu ga kamfanonin da ke da alaka da cibiyoyin tsaro, sojoji, da cibiyoyin sadarwa...
Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo. Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba. Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi. Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”. A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa. Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana...
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar. Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar...
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa. A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa. Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda. Share 0...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da wani hari da jiragin sama mara matuki a filin jirgin sama na Isra’ila domin nuna goyon bayansu ga alummar palasdinu adaidai lokacin da isra’ila ke ci gaba da yin kisan gilla a gaza. Kakakin sojojin kasar yamen brigadier ganar Yahaya Saree ya sanar a gidan talabijin cewa yau ma dakarun sojin kasar sun kai wani hari da jirgin sama mara matuki da ya keta sararin samaniyar isra’ila ya dira a filin saukar jiragen sama na Ramon, Tuni dai dakarun kasar yamen suka sanar da aniyarsu ta ci gaba da kai hare hare kan isra’ila har sai ta dakatar da kai hari da yin kisan kiyashi kan alummar gaza. Ya...
A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin cire kayayyakin lantarki. “Rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno an kwashe gawar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken likitanci yadda ya kamata.” Ya jaddada cewa rundunar ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin gargaɗi ga mazauna jihar da su guji aikata lalata kayayyakin gwamnati. Daso ya ƙara da...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana dalilin da ya sa tawagarta ba ta halarci kada kuri’a kan batun Falasdinu ba Ofishin Jakadancin Iran ya jaddada cewa, duk wata hanyar warware matsalar Falastinu a zahiri dole ne ta dogara kan amincewa da hakkin al’ummar Falastinu na dogaro da kai da kuma watsi da duk wani batun tilasta musu yin gudun hijira. Ta kuma jaddada cewa, za a iya samun dawwamammen zaman lafiya ne ta hanyar kawo karshen mamaya da kuma samun cikakken ‘yancin kai gami da samun ‘yancin kai na kasar Falasdinu, tare da la’akari da ainihin nufin ‘yan asalinta-Musulmi, Yahudawa, da Kirista—ta hanyar kuri’ar raba gardama mai ‘yanci, kamar yadda aka gabatar a cikin takardar yarjejeniya mail amba S/2019/862. A...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu. A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel. Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta. Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar...
Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi
Masanan sun yi gargaɗi yayin da Shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na sake fasalin ɓangaren lafiya na Nijeriya, inda ya bayyana cewa babu wani ɗan ƙasa da ya kamata ya rasa rayuwarsa saboda rashin wutar lantarki a cibiyoyin lafiya. Yayin da yake jawabi a Taron Tattaunawar Masu Ruwa da Tsaki na Ƙasa kan Wutar Lantarki a Ɓangaren Lafiya, a Ladi Kwali Hall na Continental Hotel, Abuja, Shugaban ƙasa, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya lura cewa rashin wutar lantarki da ke ci gaba a asibitoci na rage ingancin kulawa da kuma jawo asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Zanga-zangar ta biyo bayan kashe jami’an ‘yansanda uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a wani shingen bincike a cikin garin Egbe. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya shaidawa manema labarai a Lokoja cewa, harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba. Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansanda, Miller Dantawaye, nan take ya tura rundunar ‘yansanda zuwa yankin domin fatattakar maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ne suka sanar da sabon tsarin a ranar Laraba, inda suka bayyana shi a matsayin wani ƙwaƙƙwaran mataki na “rage yawan masu neman aiki a ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu, ta hanyar koyar da dabarun kasuwanci, daidai da ka’idojin duniya, da kuma shirya matasan Nijeriya don samun ayyukan yi a nan gaba. Kwasakwasan da aka ɓullo da su Kwasakwasai na koyar da dabarun Kasuwanci 26 da gwamnatin ta bullo da su, sun hada da Brick Laying, Block Laying and Concreting, Painting Decoration and Finishes (Interior Design), Woodwork, Carpentry and Joinery, Welding & Fabrication, Plumbing and Pipe Fitting, Computer Hardware & GSM Repair and...
Jakadan kasar Iran a Rasha ya bayyana cewa daya daga cikin muhimman alamura da ake gab da cimma yarjejeniya akansa tsakaninsu da kasar Rasha a bangaren makamashi shi ne batun kai iskar gas Iran, wanda tuni aka wuce matakin share fage ana gab da kammalawa Kazim Jalali ya fadi a gefen bikin baje kulin kayayyakin rubobi da aka gudanar cewa” tattaunawar baya bayan nan da aka yi tsakanin Iran da Rasha a kasar chine ya nuna cewa an cimma matsaya tsakanin kasashen biyu, musamman game da kwangoglin da suka shafi tattalin arziki . Jalali ya kara da cewa daga cikin muhimman batutuwa dake tsakanin kasashen biyu shi ne batun isar da gas ga kasar Iran a matsayin wani bangare na...
Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin HKI a yau Laraba sun tsananta hare-hare a cikin birnin Gaza, inda ta rusa hasumiyyar Birnin inda daruruwan falasdinawa suke rayuwa, saboda cimma manufarta na mamaye birnin gaba daya. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a safiyar yau laraba ce jiragen yakin HKI suka yi ruwan boma bomai kan Hasumiyar Tayba II wanda ke unguwar Rimal na birnin Gaza sun kuma dai-daita shi da kasa. Tun cikin kwanakin da suka gabata ne sojojin yahudawan suka fara rusa dogayen gine-gine a birnin Gaza, da nufin korar duk mutane birnin, hasumiyuar Tayba II na daga cikin dogayen gine-ginen da falasdinawa suke zama a cikinsa a gaza wanda HKI suka rusa.. Tun watan da ya gabata ne gwamnatin...
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu. Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong shi ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin nan dan wasan bayan Nijeriya Calvin Bassey ya farke kwallon dab da za a tafi zuwa hutun rabin lokaci. Wannan sakamakon ya sa Super Eagles din rasa tikitin kai tsaye da zai kaisu gasar Kofin Duniya, amma kuma suna da wata damar, idan sukayi kokarin karewa a mataki na biyu a rukunin C. Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da...
Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Idan Afirka Ta Kudu ta yi nasara yau, za ta tabbatar da zuwa gasar Kofin Duniya da za a buga a Arewacin Amurka a 2026, kuma karo na farko tun bayan 2010 lokacin da ta ɗauki nauyin gasar. Nijeriya kuwa, wadda ta halarci gasar sau shida a baya, tana ƙoƙarin dawo da martabarta. Nasarar da ta samu a kan Rwanda a wasan da ya gabata ta farfaɗo da ƙwarin guiwar masoyanta, duk da cewa a wasanni bakwai da ta buga na neman gurbin shiga 2026, sau biyu kacal ta ci. Wasan na yau shi ne karo na 17 da ƙasashen biyu za su haɗu. Nijeriya ta fi samun nasara sau takwas, inda aka tashi canjaras sau bakwai, sai Afirka Ta...
Wani Jirgin Drone wanda ake sarrafashi daga nisa, ya fada kan zauren fisinjoji a tashar jiragen sama na Ramon dake yankin Araya na kudancin haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan harin ya nuna irin yadda sojojin Yemen suke fadada hare-harensu a kan HKI, da kuma tabbatar mata da cewa Yemenawa suna iya kaiwa ko wani wuri a fadin kasar Falasdinu da aka mamaya. Majiyar yahudawa ta bayyana cewa wai wasu fasinjoji ko kuma yahudawa yan shere wuri zauna ne suka ji ciwa sanadiyyar harin. Sannan babbar abin tambaya ita ce, shin ina makaman kare sararin samaniyar kasar wadanda kasar da kasashen yamma suke tutiya da su. Ta yaya jirgin yaki daga kasar Yemen...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fira Ministan gwamnatin kasar Senegal ya nemi afuwar rashin amsa gayyatarsa ta farko a hukumance zuwa Faransa Fira ministan Senegal Ousmane Sonko ya nemi afuwar rashin amsa gayyata a matsayin babban bako a zaman taron bugu na 11 na BPI France Generation Innovation Forum, wanda aka shirya gudanarwa ranar 23 ga watan Satumba a birnin Paris. Wannan zatab kasance ziyararsa ta farko zuwa Faransa tun bayan hawansa kan karagar mulki. Fira Minista ya sanar a cikin wata sanarwa da aka buga a shafinta na yanar gizo da kuma dandalin X cewa: Sonko ba zai iya halartar gayyatar ba saboda “tsarin alkawurran da aka tsara,” tare da nuna cewa wani memba na gwamnatinsa zai wakilci Senegal a dandalin. Wannan taron yana...
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jimamin Rasuwar Mutane A Nutsewar Jirgin Ruwa A Borgu, Ta Umurci NEMA Ta Kai Agaji
“Muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa, gwamnatin jihar da kuma al’ummar Neja. Jimamin mu da addu’o’in mu suna tare da duk wanda wannan ibtila’i ya shafa.” Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar da dukkan tallafi da ake buƙata ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka tsira, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja domin tabbatar da gaggawar tallafi da taimako. Haka kuma, gwamnatin ta umurci Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da ta gudanar da babban kamfen na wayar da kai a faɗin ƙasar nan domin ƙara faɗakar da jama’a kan matakan tsaro...
“Ma’aikatar ba ta yi shiru ba kan irin takunkumin da iyakace kudi ya sanya a tafiyar da ayyukan ofisoshin, ciki har da rashin iya biyan albashin ma’aikatan gida, biyan bukatun kudi ga masu bayar da ayyuka, haya ga masu gidaje, da kuma alawus ga jami’an da ke aiki a gida,” in ji sanarwar. Yayin da ta jaddada cewa wannan yanayi na nuna halin tattalin arzikin kasa gaba daya, ma’aikatar ta lura cewa karancin kudi a tsawon shekaru ya ragi ikon ofisoshin wajen gudanar da manyan ayyukan diflomasiyya. “Dole ne a bayyana, duk da haka, cewa ofisoshin diflomasiyyar Nijeriya ba su da kariya daga halin tattalin arzikin gida da kalubalen da ke tattare da ayyukan gwamnati. Matsalar kudi a...
Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 20 ga watan Yulin bana, an gano gawarwaki 85 a gefen buhunan abinci masu dauke da tambarin MDD, wadanda suka hada da mata da yara. Wasu na ci gaba da rike buhunan abinci lokacin da aka same su, yayin da wasu yaran ke cikin yanayi na nuna galabaita kafin mutuwarsu. Wannan shi ne mummunan sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai a wani wurin rarraba kayan agaji a zirin Gaza. Abun takaici shi ne, ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan abun ba. Wani rahoton MDD ya nuna cewa, mutum guda na mutuwa a duk minti uku a fagen yaki a fadin duniya. Mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon yaki, su ne mafi daukar hankali...
Wani da abin ya faru a gabansa ya shaida cewa jirgin ya cika makil da fasinjoji tun daga lokacin da ya bar Tunga Sule, amma matsalar ta fara faruwa a lokacin da suka kai Gausawa, inda jirgin ya kife nan take. Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Mun karɓi rahoton hatsarin jirgin ruwa a wani ƙauye mai suna Gausawa da ke yankin Malale a ƙaramar hukumar Borgu,” a cewarsa Ya ce, “Bisa rahoton jami’inmu na ‘search and rescue’, jirgin ya tashi daga Tugan Sule da ke gundumar Shagunu dauke da mutane 90, ciki har da mata da yara, suna tafiya Dugga domin gaisuwar ta’aziyya.” ...
Ya ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da kula da tsaro tare da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce alakar Sin da Rasha ta zama misali na kyakkyawar dangantaka tsakanin manyan kasashe, wadda ke kunshe da ingantaccen yanayin kawance na makwafta, da cikakken salon tafiya tare bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin zantawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing. A nasa tsokacin kuwa, shugaba Putin ya ce shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da tsarin shugabancin duniya ta zo a lokacin da ake matukar bukatarta, kuma wajibi ne a yi aiki da ita, kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance gibin dake akwai a tsarin shugabancin duniya. Ya ce a nata bangare, Rasha a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin. Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin. Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru...