Matuƙin jirgin Air Peace na shan barasa, miyagun ƙwayoyi — Rahoton
Published: 12th, September 2025 GMT
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa.
Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama’a da taimakon iyali a hukumar NSIB, Madam Bimbo Olawumi Oladeji, wadda ta bayyanawa Daily Trust.
Daily Trust ta ruwaito yadda jirgin saman Air Peace, a ranar 13 ga watan Yuni, 2925, ya kutsa kai kan titin jirgin bayan ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal, ɗauke da fasinjoji 103.
Jirgin ya kauce hanya daga titin jirgin ba tare da wani lahani ba.
Kauce hanyar jirgin sama kuskure ne ko rashin amfanin da izini na sanya jirgin sama ya kauce asalin titin jirgi.
Hukumar NSIB ta ce, “Jirgin yana aiki ne a matsayin jirgin sufuri na cikin gida da aka tsara daga Legas zuwa Fatakwal tare da mutane 103 a cikinsa, ya sauka a kan titin mai tsawo Runway 21 bayan rashin amfani da umarni, jirgin ya yi tafiya mai nisan mita 2,264 daga bakin titin inda ya tsaya ƙarshe a nisan mita 209 zuwa titin.
“Dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun sauka lafiya, kuma ba a sami rahoton wani rauni ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fatakwal
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp