Jiragen ‘Drons’ Na kasar Yemen Sun Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Ramon A Isra’ila
Published: 7th, September 2025 GMT
Wani Jirgin Drone wanda ake sarrafashi daga nisa, ya fada kan zauren fisinjoji a tashar jiragen sama na Ramon dake yankin Araya na kudancin haramtacciyar kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan harin ya nuna irin yadda sojojin Yemen suke fadada hare-harensu a kan HKI, da kuma tabbatar mata da cewa Yemenawa suna iya kaiwa ko wani wuri a fadin kasar Falasdinu da aka mamaya.
Majiyar yahudawa ta bayyana cewa wai wasu fasinjoji ko kuma yahudawa yan shere wuri zauna ne suka ji ciwa sanadiyyar harin.
Sannan babbar abin tambaya ita ce, shin ina makaman kare sararin samaniyar kasar wadanda kasar da kasashen yamma suke tutiya da su. Ta yaya jirgin yaki daga kasar Yemen zai wuce wadan nan garkuwan makamai a HKI ba tare da sun ganoshi, ballanta na su tareshi. Don haka wannan ya tabbatar mana cewa jiragen makiya suna kai ko ina a HKI, ko kasar Falasdinu da aka mamaye.
Jam’ian gwamnatin HKI sun tabbatar da cewa garkuwan makamai masu linzamin kasar basu gano makamin ba, don haka ne bai motsa ba. Wasu sun tabbatar da cewa basu san da shigowar makamin ba sai da ya fada kan tashar jiragen . HKI dai ta cewa tana da garkuwan makamai har guda uku, Dome, David’s Sling da kuma Arrow amma ba wanda ta motsa. A cikin yan kwanakin da suka gabata ne HKI ta kai hare-hare wadanda suka kashe Firay ministan kasar Yemen da kuma wasu daga cikin ministocinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wilayati Yace, Yenci da Tsaron Kasar Iraki Na Da Matukar Muhimmanci Ga Iran September 7, 2025 NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai September 7, 2025 An Gudana Da Zanga zanga Adawa Da Ziyarar Shugaban Amurka a Kasar Malesiya . September 7, 2025 Za’a Fara Taron Makon Hadin Kai Karo Na 39 A Nan Tehran September 7, 2025 Dubban Mutane ne Suka Gudanar Da Zanga-zanga A Birnin London September 7, 2025 An Rufe Kamfanin Kera Makamai Na Isra’ila Dake Birtaniya. September 7, 2025 Araqchi: Suna Ci Gaba Da Musayar Sakonni Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani September 7, 2025 Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Wajabcin Kasancewar Iran Cikin Shirin Yaki September 7, 2025 Shugaban Hukumar Shari’ar Iran Ya Ce: Iran Ba Za Ta Taba Mika Kai Bori Ya Hau Ba September 7, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwata Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Zirin Gaza September 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka.
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan.
A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka.
Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya karbi mulkin kasar ne bayan kisan mahaifinsa tsohon shugaba Idriss Deby, a lokacin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da mayakan ‘yan tawaye a arewacin kasar a shekarar 2021.
Deby ya yi ikirarin samun nasara bayan zaben da aka gudanar bayan shekaru uku na mulkin soja a watan Mayun 2024, sannan kuma aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Disamba, wanda ya bai wa jam’iyya mai mulki rinjayen kujeru.
An samu cece-kuce game da sakamakon zaben, bayan da madugun ‘yan adawa kuma firaministan kasar Succe Massara ya yi ikirarin samun nasara, ikirarin da hukumar zaben kasar ta yi watsi da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci