Mutane 29 Sun Rasa Rayukansu A Wani Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Neja
Published: 3rd, September 2025 GMT
Wani da abin ya faru a gabansa ya shaida cewa jirgin ya cika makil da fasinjoji tun daga lokacin da ya bar Tunga Sule, amma matsalar ta fara faruwa a lokacin da suka kai Gausawa, inda jirgin ya kife nan take.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun karɓi rahoton hatsarin jirgin ruwa a wani ƙauye mai suna Gausawa da ke yankin Malale a ƙaramar hukumar Borgu,” a cewarsa
Ya ce, “Bisa rahoton jami’inmu na ‘search and rescue’, jirgin ya tashi daga Tugan Sule da ke gundumar Shagunu dauke da mutane 90, ciki har da mata da yara, suna tafiya Dugga domin gaisuwar ta’aziyya.”
Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a sakamakon yawan fasinjoji fiye da ƙima da kuma bugu da katako da ke karkashin ruwa, tare da cewa babu wani daga cikin fasinjojin da ke sanye da rigar kariya (life jacket), duk da umarnin gwamnati game da amfani da ita a jihar.
Arah ya ce an gano gawarwaki 29, an ceto mutane 50 da rai, yayin da mutane biyu saka ɓace ake ci gaba da neman su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Taron kaddamar da rabar da taraktocin noman, ya gudana ne a Shalkwatar Ma’aikatar Kula da Aikin noma da kuma yin Noman Rani da ke garin Kalaba.
Kazalika, taron ya samu halartar ‘yan Majalisa da Sarakunan Gargajiya da kungiyoyin manoma mata da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da ke jihar da abokan hadaka.
Daukacinsu, sun jinjina wa wannan kokari na gwamna Bassey, kan wannan hangen nesa da gwamnatinsa ta yi, na kaddamar da taraktocin noman, musamman domin ciyar da fannin aikin noman jihar gaba, duba da cewa; fannin ne kinshikin tattalin arzikin jihar.
Har ila yau, gwamna Bassey, ya nanata kudurin gwamnatinsa wajen ci gaba da bai wa fannin aikin noma muhimmanci a matsayin fannin da ke kara habaka tattalin arzikin jihar.
“A lokacin da na karbi jan ragamar shugabancin jihar, mun samar da dabaru da kuma daukar matakai daban-daban, domin kara habaka fannin,“ in ji gwamna Bassey.
“Biyo bayan wata ganawa da muka yi da manoman da ke daukacin kananan hukumominmu, mun gano cewa; kalubalen da suke fuskanta sama da kashi 70 cikin dari, na shiye-shiyen share gonakansu ne, domin fara noma su; saboda kudaden da suke kashewa masu yawa, wajen gyaran gonakin nasu, muna da yakinin wannan shirin zai magance wadannan matsaloi,” a cewar gwamnan.
Kazalika, gwamnan ya bayyana cewa; wannan rabar da taraktocin noma, wadanda ba sa shan man sosai, an tsara su ne kan yadda manoma za su yi gyaran gonakinsu cikin sauki tare kuma da rage musu kashe kudade masu yawa da kuma kara habaka fannin na aikin noma.
“Kashi 108 na kashin farko na shirin, an raba wa manoman jihar jimillar taraktocin noma 324, wadanda kuma aka rabar da su a daukacin fadin jihar,“ a cewar gwamnan.
Gwamna Bassey ya ci gaba da cewa, za a ci gaba da kula da taraktocin ne a karkashin tsarin kungiyoyin manoma na jihar.
“Hakan zai bai wa wadanda suka amfana da taraktocin damar daukar nauyin ci gaba da kula da su, wanda kuma sauran manoman da ke karkara a jihar, su ma za su samu damar samun taraktocin,” in ji shi.
“Ta wannan hanyar, za mu samu damar cin gajiyar da ke fannin noma na jihar, wanda hakan zai kuma bai wa manoman jihar kara dagewa, domin yin noma da samun kudaden shiga da kuma kara samar da wadataccen abinci a jihar,” a cewar tasa.
Kazalika, gwamnan ya kuma zayyano wasu ayyukan noma da gwamnatinsa ta kaddamar da su da suka hada da na samar da Irin noman Rogo, aikin noman Masara da na Waken Soya da sauransu.
Ya bayyana cewa, gwamnatin na kuma ci gaba da habaka samar da Irin Farin Wake da rabar da kayan aikin noma ga kananan manoma tare da kuma shirye-shiyen noman Koko (Cocoa) da Ganyen Shayi, wanda za gudanar ta hanyar yin hadaka da gwamnatin da kuma ‘yan kasuwa.
“Kaddamar da rabar da wadannan taraktocin noman, na daya daga cikin kason farko na kudurin gwamnatinmu na bunkasa fannin aikin noma na jihar, musamman ta hanyar yin amfani da kayan aikin noma na zamani,” in ji gwamnan.
Shi ma, shugaban kamfanin da ya yi kwangilar kawo taraktocin, Femi Odeshirin, ya yaba wa shirin, wanda ya ce; hakan zai kara bunkasa fannin aikin noma na jihar.
“Ba wai kawai rabar da wadannan taraktocin noma ga manoman jihar ba ne da gwamnan ya yi ba, hakan zai kuma kara inganta rayuwar manoman da suka amfana,” in ji Odeleye.
Ya bayyana cewa, kamfanin na kuma kan shirin kafa masana’antar da ake hada taraktocin noma a garin Kalaba da ke jihar, inda masana’antar za ta samar da ayyukan yi sama da 2,000.
Shi kuwa, shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN) reshen jihar, Ojikpong Nyiam Bisong, danganta salon shugabancin gwamna Bassey ya yi da na marigayi tsohon Firimiyan Kudancin Nijeriya, Dakta Michael Okpara.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA