Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafiz Miko Yakasai
Published: 5th, September 2025 GMT
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak.
BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.
Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da *
Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano.
Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi mai tawali’u, wanda aikin da ya yi zai ci gaba da haskaka fannin harsunan Hausa da na Afirka baki-ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Bayero University Kano Farfesa Hafiz Miko Yakasai Farfesa Hafizu Miko Yakasai Jami ar Bayero Kano Kimiyyar Harshe
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.
A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp