2025-11-03@08:05:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 309

«zuwa Tawila»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF). Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma...
    130-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka  barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafai wadanda suka hada da littafin Dastane Rastantan na Aya. Shaheed Murtadan Muttahary ko kuma cikin littafin mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro za su kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmun da ya gabata mun bayyana yadda Amirulmuminina Aliyu...
    Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...
    Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara  Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa.   Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA.   Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar.   “Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Mai Martaba Shehun Bama, Dakta Umar ibn Kyari Umar El-Kanemi, ziyara a fadarsa da ke Bama. Ya ce an riga an kammala gina matsuguni 1,000 a Darajamal, sannan kuma aikin gina wasu a sauran garuruwan hudu. “Mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan gudun hijira gida. A Mayanti,...
    A yau Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Beijing ta sanar da cewa, an dawo da wutar lantarki da ayyukan sadarwa a dukkan kauyukan da ibtila’i ya shafa a fadin birnin na Beijing, biyo bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka, yayin da kuma ake ci gaba da aikin ceto wadanda suka bace. Ruwan sama da iska mai karfi da aka yi fama da shi daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da mutane tara suka bace, a babban birnin kasar, kamar yadda aka sanar a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin...
    Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, AVM Kaita ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro da kuma Shugaban Sashen Kirkire-Kirkire na tsaro. Ana girmama shi saboda gudunmawar da ya bayar wajen horarwa da inganta ayyukan rundunar sojin sama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na kimanin kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da Tinubun ya samu. “A yau, ga shi mun taru, domin yin nazari a kan waɗancan alƙawuran tare kuma da tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, abubuwan da muka samu su ne; sauye-sauyen da aka samu duk kuwa da irin ƙalubalen da ake fuskanta a wannan ƙasa. Wannan na nuna cewa, demokuraɗiyyarmu za ta...
    Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin. ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa,  daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa,...
    Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya Aikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba...
    Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai Ali Isah, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Majalisar bayan wata ganawa da mai kula da jihar Ribas Sole a Abuja.   Ali Isah, ya bayyana cewa mai kula da jihar ta Ribas ya kasance a gidan a wani bangare na ziyarar da ya saba yi domin yiwa kwamitin riko da ke sa ido kan al’amuran gwamnati.   Shugaban marasa rinjaye wanda ya jagoranci taron a madadin shugaban kwamitin wanda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Farfesa Julius Ihonvere, ya bayyana gamsuwa da kokarin da mai gudanarwa shi kadai yake yi na wanzar da zaman lafiya a jihar.   Ya ce mai kula da jihar ya tuntubi...
    Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.   A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula.   A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo...
    Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran “IRGC” ya bayyana cewa: Hasashen Raunin Iran ya gushe, kuma ba zai sake dawowa ba Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Mohammad Na’eini ya jaddada cewa: Ra’ayin cewa Iran mai rauni ce ya raguje kwata-kwata, yana mai jaddada cewa; Yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan ya fallasa gazawar makiya wajen karya manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma ya nuna cewa duk wani sabon harin wuce gona da iri zai fuskanci martani mai tsanani da gauni da zai wurga makiya cikin mummunar nadama. Hakan ya zo ne a jawabin da Birgediya Janar Na’eini ya gabatar a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da shahidi Ramadan...
    Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
    Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal  Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu yankuna a Jihar Legas, na iya fuskantar rashin wuta na tsawon kwanaki 25, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara gyaran layin lantarkin Omotosho zuwa Ikeja ta Yamma mai ƙarfin 330kV. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, aikin zai gudana kowace rana daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma, kuma za a kammala aikin a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025. Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Kamfanin, ya bayyana cewa gyaran zai shafi raba wutar lantarki a wasu wurare, kuma hakan na iya janyo ɗaukewar wuta. Sanarwar ta ce: “Abokan...
    Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya. Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.” Ya kara da cewa: “Dole...
    Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji. “Ana iya cin moriyar manufofin ba da fifikon harajin kudi a tsibirin Hainan”, sannan “mu’amalar Hainan da kasashen duniya za ta kasance cikin ’yanci da lumana”. A ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na kara fadada bude kofa ga ketare, wanda ba bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar...
    Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a  wajen taron. Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Nentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis. Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
    Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa a yau Alhamis. Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su dare shugabancin jam’iyyar mai mulki. Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura shi ma na daga cikin wadanda ake duba yiwuwar ba kujerar. Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno NAFDAC ta gano dakin ajiye kayayyaki makare da sinadaran hada bam a Kano A daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi...
    Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan  Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa. Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran. Dangane da zargin da...
    Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka. “Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem. Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen...
    Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana. Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji...
    “Saboda barazanar tsaro da ke tattare da al’amuran siyasa, da kuma buƙatar kare lafiyata yayin gudanar da aiki, ina roƙon a dawo min da jami’an tsarona,” in ji ta. Ta kuma haɗa da kwafin hukuncin kotun, inda ta jaddada marnin dawo da ita bakin aiki. Sai dai komawarta majalisa ya haifar da ce-ce-ku-ce, domin Majalisar Dattawa ta ce hukuncin kotun da Sanata Natasha ke dogaro da shi ba dole ba ne a aiwatar da shi, domin ba umarni ba ne kai-tsaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
    Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai: “Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“ A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan kwashe makonni biyu, inda ya ziyarci ƙasashen Saint Lucia da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X. Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025 don ziyarar aiki a waɗannan ƙasashe biyu. Da farko ya je Saint Lucia domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Caribbean, da kuma ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen kudancin duniya. A ranar 4 ga watan Yuli, Tinubu ya tashi daga Saint Lucia zuwa Brazil, inda ya halarci taron BRICS...
    A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470.   A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara.   Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne.   “Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da...
    Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis. Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci. Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za...
    Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya. Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu  na ajiye makamai”. Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.” Kuniyar PKK ta...
    Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga  hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini. Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da kuma kusoshinta daga yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Bolaji Abdullahi ya ce, “muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar taron ita ce domin razanawa da tursasa wadannan shugabannin jam’iyar su shirya wa ’yan adawar makarkashiya. Wannan ba siyasa ba ce, tsurku ce.” Ya ci gaba da cewa, hadafin taron...
    ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba. Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024. Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun...
    Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu. Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin kasar da kawayenta. Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke kokarin kama shi. A watan Afirilu RSF din ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba kasar. Alawia ta ce yayin da fadan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bada sanarwan cewa da ita da sauran kungiyoyi da suke gwagwarmaya da HKI kimani shekaru biyu da suka gabata, sun amince da batun tattaunawa da kuma tsagaiuta budewa juna wuta wanda masu shiga tsakani suka gabatar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce, wai HKI ta amince da shawarar budewa juna wuta da ya gabatar, amma kuma har yanzun ba’a bayyana dalla-dalla menen a cikin yarjeniyar ta kunsa ba. Har’ila yau gwamnatin kasar Masar ta ce tana kokarin ganin an samar da tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60.
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya. Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya. Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa...
    Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati. Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher...
    Bashir Ahmad, hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban yana cikin ƙoshin lafiya a birnin Landan. A cewarsa, labarin da ke yawo cewa Buhari na fama da mummunar rashin lafiya har yana kwance a ɗakin kulawa na musamman (ICU), ba gaskiya ba ne. Lakurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato ‘Yan Sanda Sun Hana Yunqurin Fasa Shago a Gombe, Tare da Kwato Babur Bashir ya tabbatar da cewa Buhari ya yi rashin lafiya a baya, amma yanzu yana samun kulawar likitoci kamar yadda ya kamata. “Lamarin ba kamar yadda wasu kafafen labarai ke yaɗa labari suka ruwaito ba, Buhari yana cikin yanayi mai kyau kuma magunguna na aiki a jikinsa,” in ji Bashir. Ya ƙara da cewa suna...
    Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar aka gabatar mata. Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin. Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC Ƙungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin. Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra’ila ta amince da ita. To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra’ayin riƙau ba...
    ‘Yan tawagar jam’iyyar UDA ta kasar Kenya da suka kawo ziyara kasar Sin sun kwatanta jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da bishiyar kuka, suna cewa, “Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tamkar bishiyar kuka ce, wadda ke da ingantattun saiwoyi da ma babban karfi na warkar da kanta, tana ta fid da furanni da ‘ya’ya ba tare da tsayawa ba” “bishiyoyin kuka suna da tsawon rai na sama da shekaru dubu”. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana cikin karfinta, kuma za ta ci gaba da kokartawa domin bauta wa jama’a, tare da dogara da jama’a don cimma karin nasarori.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    “Ba za su samu tayin da ya fi wannan ba abu zai ƙara muni idan suka ƙi.” Har yanzu babu martani daga jami’an Isra’ila kan iƙirarin Trump ba. Tattaunawar neman tsagaita wuta ta tsaya cak tun watanni da suka gabata saboda rashin jituwa kan matakin da za a ɗauka bayan an daina faɗa. Isra’ila tana son ta ci gaba da samun damar kai farmaki idan ta ga dama, amma Hamas tana so a daina faɗa gaba ɗaya. Ana sa ran Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai kai ziyara fadar White House a mako mai zuwa. Trump ya ce zai yi magana da Netanyahu domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin. A farkon shekarar nan, wani ƙoƙari na tsagaita wuta ya rushe a...
    A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin. Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci a HK, ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don gina yanki mai tsaro da daidaito, tare da zage damtse wajen gina tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummarsa, kuma sannu a hankali matakan na haifar da mai ido. Lee ya ce, a nan gaba, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da managarcin yanayin tsaro, kana zai gaggauta bunkasa yankin...
    Kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Ayatullah Baqir Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda Hukumar tsaron kasar Iraki ta sanar a ranar litinin cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aiwatar da zaluncin kisa kan Ayatullahi Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda. Ofishin yada labarai na hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan masu laifin Sa’adoun Sabri da Haitham Abdul Aziz, bayan da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen aiwatar da hukuncin kisa kan Shahadar Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa, Alawiyya Bint al-Huda a...
    Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta Lebanon ya fadawa Jaridar da The National ta kasar Amurka kan cewa a makon da ya gabata an kama wani shugaban yan kungiyar yan ta’adda ta ISIS a cikin kasar, tare da zarginsa da shiri hare-hare masu yawa a kasar Lebanon. Kafin haka dai a cikin watan da ya gabata wani dan ta’ada ya tarwatsa kansa a cikin wani coci a birnin Damascus babban birnin...
    JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI. Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya.   Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me doka ta ce a kan daukar doka a hannu da wasu ‘yan Najeriya su’ke yi? NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don kawo karshen daukar doka a hannu a...
    Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
    Daga karshe Musa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.   Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Yelwata da ke karamar hukumar Guma, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka a wani cocin Katolika na yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne. A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya kare matakin farmakin da ƙasarsa ta kai wa Iran, inda ya kwatanta jagoran addini Khamenei a matsayin wani sabon Hitler na wannan zamani. Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan sisaya ta satar kuɗi — EFCC Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe A yayin hirar, duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Shugaban Amurka Donald Trump ya sahale...
    “A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran za a yi tsawa da sanyin safiya a sassan jihohin Benuwe, Filato, Neja, Babban Birnin Tarayya, da Jihar Nasarawa.   “A washegari, ana hasashen tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Neja, Nasarawa, Benuwe, Kwara, Kogi, da Filato.   “A yankin Kudu, ana sa ran samun hadari tare da yiwuwar samun ruwan sama a sassan jihohin Enugu, Ebonyi, Cross River, Legas, Akwa Ibom, Ribas, da Bayelsa,” in ji NiMet. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.   Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.   Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.   “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.   “Martabar...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara...
    Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce shekara biyu da Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin shugaban ƙasa sun fi kowane lokaci muni tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar. Yayin da yake magana da BBC a ranar Dimokuraɗiyya da Najeriya ke cika shekaru 26 tana mulkin farar hula, Dalung ya ce ba wani abin arziƙi da talaka ya amfana da shi daga wannan gwamnati. An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Ya ce: “Kawai abin da talaka ya samu daga gwamnatin Tinubu shi ne tsadar rayuwa, yunwa, wahala da matsalar tsaro.” Ya zargi gwamnatin da cewa cire tallafin...
    Wani mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi sanadin mutuwar mutum takwas ’yan gida daya, yayin da wasu mutum biyu ke can kwance a asibiti rai a hannun Allah. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin a garin Barakallahu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ana tsaka da bukukuwan Babbar Sallah. A cewar rahotannin, lamarin ya faru ne lokacin da wata mota da ke tsala gudu ta kwace sannan ta danne mutanen da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah. Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India A cewar mahaifin mamatan,...
    Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin. Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wasikar wacce ke dauke da sa hannun...
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
    A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama. Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga damar jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa. Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa rarrabuwar kawunan ta samu ne sakamakon nuna iko tsakanin wasu mutane a wasu jihohi. Akwai batun wanda ke da iko da tsarin jam’iyyar shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Yayin da wasu ke cewa wannan shi ne tushen da ya haifar da rarrabuwar kawuna da ke faruwa a cikin tsarin...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Idi Al-Adha a Tehran ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya kawo sauyi mai girma da fadi a Iran Limamin da ya jagoranci Sallar Idin Al-Adha a birnin Tehran Hujjatul-Islam Hasan Abu Torabi Fard ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya share fagen kasancewar al’ummar Iran a fagage mafi muhimmanci na yanke shaawara, sannan kuma ya ba da damar samun gagarumin sauyi mai girma a Iran. Hujjatul- Islam Abu Torabi Fard ya kara da cewa: Muna tunawa da rasuwar wani fitaccen mutum kuma fitaccen mutum wanda ya taso kuma aka rene shi a cikin mazhabar hankali da ilimi da tauhidi na ubangijinmu Ibrahim Majibin Rahma (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Ya ci gaba...
    Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren  gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu. Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don...
    Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka. Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da...
    Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata,  sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano. “Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali. Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai...
    Mazauna Babban Birnin Tarayya za su fuskanci katsewar ruwan sha na tsawon makonni biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Ruwa ta yankin ta sanar. Rashin ruwan, wanda ya fara ranar Juma’a, 30 ga Mayu, ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar Juma’a, 13 ga Yuni. Matsalar ta samo asali ne daga ayyukan gyare-gyare da ake yi a tashoshin tace ruwa na madatsar ruwa ta Lower Usuma Dam. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, gyare-gyaren sun shafi muhimmin aikin haɗa kayan aikin lantarki da injiniya, wanda babban bangare ne na aikin inganta matatar. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno...
    Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza. Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong. Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki. A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi. Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da...
    Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin.  Ta kuma kara da cewa  an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki. Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata....
    Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu su dakatar da bawa HKI makaman da take kishe falasdinawa da su. A birnin Berlin da kasar Jamus dubban Jamusawa sun hadu a dandalin at Oranienplatz inda suke rera taken ‘a bawa Falasdinawa yenci, HKI yar ta’adda ce, kuma gwamnatin Jamas ta dakatar da tallafin da take bawa HKI. Labaran sun kara da cewa hatta mutanen kasar Jamus yan asalin yahudawa sun fito sun bayyana...
    Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta    Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci  wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen  laifukan  da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14 Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da...
    PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya. Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike. Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike...
    Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan a zirin Gaza, yana mai kira da a kawo karshen kisan kiyashi da rashin hukunta shugabannin gwamnatin ‘yan shayoniyya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya don hukunta su. Baqa’i ya yi ishara da laifuffukan da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ya...
    “Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa. An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin. Ya ce Najeriya na...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana. An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan...
    Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...
    Ta ce: “Zargin da aka yi na cewa na shirya ficewar matan daga bikin Uwargidan Gwamna a ranar 2 ga Mayu 2025, karya ce kawai. Ba ni da hannu a cikin wannan lamirin kuma wannan ƙarya ce ta masu tada hankali.   “Na kasance na mai da hankali ne kan karatuna na digiri na uku a lokacin da aka dakatar da ni, ba tare da shiga cikin wani yunkuri ba. Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki su taimaka wajen inganta zaman lafiya a jihar.”   Ta kara da cewa ta kasance tana aiki don ci gaban jihar kuma ta bukaci mutane su guji yada jita-jita maras tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza, kuma a gaggauwa kawo karshen kissan falasdinawa da kuma bude kofofin shigar da agaji zuwa cikin yankin. Inda miliyoyin Falasdinawa daga ciki har da yara miliyon guda suke mutuwar yunwa ga kuma kissa da makami ta sama.
    Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.   Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
    Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa  da ita ba.  A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an  gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.” Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.” Watanni 9 da su...
    Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, ‌kasar Sin‌ za ta ‌kara bude kofarta domin ‌maraba da jarin waje na duniya‌. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka.   Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel. Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji. A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas. Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.   Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba.   Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa.   Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi...
      Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida ba, domin kuwa hakan zai haifar da illa ga moriyar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp