Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
Published: 31st, July 2025 GMT
Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai Ali Isah, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Majalisar bayan wata ganawa da mai kula da jihar Ribas Sole a Abuja.
Ali Isah, ya bayyana cewa mai kula da jihar ta Ribas ya kasance a gidan a wani bangare na ziyarar da ya saba yi domin yiwa kwamitin riko da ke sa ido kan al’amuran gwamnati.
Shugaban marasa rinjaye wanda ya jagoranci taron a madadin shugaban kwamitin wanda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Farfesa Julius Ihonvere, ya bayyana gamsuwa da kokarin da mai gudanarwa shi kadai yake yi na wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya ce mai kula da jihar ya tuntubi manyan masu ruwa da tsaki kan rikicin shugabancin jihar Ribas, shugabannin cibiyoyin addini da na gargajiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi domin ci gaban jihar.
Sai dai jami’in da ya gabata, ya umurci mai kula da shi kadai da ya tabbatar da cewa rikicin shugabancin jihar Ribas bai shafi biyan albashin ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya duk wata da fansho ba kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da majalisar dokokin kasar ke yin duk mai yiwuwa don tabbatar da mulkin dimokuradiyya a kasar nan.
Ali Isah, ya kuma tabbatar da cewa kwamitin wucin gadi zai ci gaba da tuntubar mai gudanarwa da bangaren zartarwa don hana tsawaita dakatarwar daga wa’adin watanni shida domin samun ci gaba.
COV: TSIBIRI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Majilasar Kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
An zabi Doro ne bayan naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Doro a matsayin ƙwararren masani da ke da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni da dama ciki har da aikin asibiti, gudanar da harkokin magunguna, da jagoranci a Nijeriya da Birtaniya.
An haifi Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau. Yana da digiri a fannin magunguna da shari’a, MBA a dabarun kasuwanci na IT, da kuma digiri na biyu a fannin aikin lafiya mai zurfi (Advanced Clinical Practice).
Da amincewar da aka yi masa a yau, ana sa ran Bernard Doro zai rantse a matsayin ɗan majalisar zartarwa (FEC) a zaman majalisar ministoci na gaba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA