Likitoci A Amurka A Amurka Sun Bukaci A Kawo Karshen Abinda Ke Faruwa A Gaza
Published: 2nd, May 2025 GMT
Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza, kuma a gaggauwa kawo karshen kissan falasdinawa da kuma bude kofofin shigar da agaji zuwa cikin yankin.
Inda miliyoyin Falasdinawa daga ciki har da yara miliyon guda suke mutuwar yunwa ga kuma kissa da makami ta sama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa.
A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona da iri kan Gaza da kuma al’amuran yanki da na kasa da kasa, inda ya bayyana irin girman bala’in jin kai da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a karkashin gwamnatin Amurka da ke mara baya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.