Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
Published: 31st, July 2025 GMT
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran “IRGC” ya bayyana cewa: Hasashen Raunin Iran ya gushe, kuma ba zai sake dawowa ba
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Mohammad Na’eini ya jaddada cewa: Ra’ayin cewa Iran mai rauni ce ya raguje kwata-kwata, yana mai jaddada cewa; Yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan ya fallasa gazawar makiya wajen karya manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma ya nuna cewa duk wani sabon harin wuce gona da iri zai fuskanci martani mai tsanani da gauni da zai wurga makiya cikin mummunar nadama.
Hakan ya zo ne a jawabin da Birgediya Janar Na’eini ya gabatar a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da shahidi Ramadan Ali Jobadari da shahidan yakin baya-bayan nan. Ya kara da cewa: “Babban bangare na yakin kwanaki goma sha biyu ya kasance yakin kafar watsa labarai da na kwakwalwa da kuma fahimtar hakikanin juna,” ya kara da cewa, “Sun samu gagarumar nasara a fagen yada labarai a lokacin yakin da aka yi a baya-bayan nan. Da kafofin watsa labaru ba su da tasiri, da makiya ba su kai hari kan kafofin watsa labaru da ‘yan jarida ba.
Ya bayyana cewa, “a cikin wannan yakin, makiya sun kai hare-hare kan manyan cibiyoyin kasa da suka hada da cibiyoyin kimiyya da na masana, kwamandojin soji, hedkwatar gudanarwa, cibiyoyin leken asiri da tsaro, da kuma kafofin watsa labarai a matsayin cibiyar tsara labarin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025 Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye
Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar.
Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar samar da wutar lantarki da ma’ajiyar man fetur da kuma filin jirgin saman Kenana na jihar White Nile da jiragen sama marasa matuka ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a ba da sanarwar yin watsi da shirin, inda ta yi nuni da cewa, yaƙin na da nasaba da al’ummar Sudan, kuma za ta tunkare shi, ta kuma yanke shawara da kansa.
Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa Youssef Abdel Manan ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Kasashen hudu masu siga tsakani ba su da wani hakki, ko na hukuma, ko na dabi’a, ko na siyasa, ko na kasa da kasa, da zai sanya su zama masu kula da al’ummar Sudan.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci